Sarkin Jordan ya mallaki gidaje a Malibu da Washington DC a Amurka da London da Ascot a Birtaniya.
A Malibu, Califonia, ya kashe fam miliyan 50 (dala miliyan 68) na wasu gidajen alfarma guda uku
A cewar alƙalumman California, ɗaya daga cikin ana dab da gida ɗaya daga cikinsu girmansa ya ruɓanya, ɗayan kuma yana da wurin ninkaya.
Gidajen Sarkin sun ƙunshi rukunin gidaje a Washington DC, inda ɗansa ya yi karatunsa na jami'a.
Gida mai ɗaki bakwai a wannan ginin an saye shi kan fam miliyan 4.7 (Dala miliyan 6.5) a 2012
Haka kuma a Birtaniya, Sarki Abdalla ya saye gidaje takwas a Birtaniya ta hanyar kamfanonin sirri.
Sun haɗa da na miliyoyin daloli kusa da Fadar Buckingham. Ya saye gidan a gefen hagu da gidaje a gefen dama.