Yaya zafin garinku yake?

Duniya na kara dumama. Da alama Yulin 2019 zai zama mafi zafi a tarihi. Sannan kuma zafin Yuli ya karu a kowanne sako a duniya cikin shekara 10 da suka gabata idan aka kwatanta da shekarun 1880 zuwa 1900, kamar yadda wannan kwallon duniyar yake nunawa.

Tasawirar da take nuna cewa zafin duniya ya canza tun daga shekarar 1900

Masana kimiyya sun yi gargadi cewa wajibi ne a takaita dumamar duniya zuwa 1.5 na ma'aunin digiri don guje wa matsalar sauyin yanayi. In aka kwatanta da zafin shekarar 1850 zuwa 1900 kafin yaduwar masana'antun kere-kere.

Tuni dai duniya ta kai zafin 1C tun daga wancan lokaci.

Kila abin ba yawa, sai dai idan kasashe ba su dauki matakin rage dumamar yanayi ba duniyarmu za ta fuskanci "mummunan sauyi", in ji wata hukuma mai kula da dumamar yanayi ta kasa-da-kasa IPCC.

Tekuna za su yi ambaliya, abin da zai raba miliyoyin mutane da mahallansu. Sannan za mu fuskanci karin zafin yanayi, kamar fari da tsananin zafi da mamakon ruwan sama sannan mu fuskanci matsala wurin shuka masara da alkama da shinkafa.

Idan yanayin zafin duniya ya ci gaba da karuwa a kan wannan ma'aunin yanayi zai dumama da 3C zuwa 4C nan da karshen wannan karni.

Bincika yadda garinku ya dumama da kuma abin da zai biyo baya.

Domin ganin wadannan bayanai sabunta manhajarka

Duba kasa don ku gano

Bari mu saukaka abin. Wannan layin yana nuna bayanin shakara 10 ne na tsaka-tsaki a kowane wata. Amma me ya yi zafi yanayi zai zama nan da shekarar 2100?

Mafi kyawun yanayi Yadda yanayin zafi zai kasance a 2100

Janairu: {{temp}}C ({{diff}} daga 1900)

Yuli: {{temp}}C {{diff}} daga 1900

Ta yaya hakan zai iya faruwa?

Hayaki mai gurbata mahalli zai karu a farkon karnin sannan ya ragu. Wanna zai takaita karuwar dumamar yanayi zuwa kasa da 2C, kuma za a bukaci dokoki masu tsauri domin hana yaduwar hayakin.

Yanayi mai karancin kyau Yadda yanayin zafi zai kasance a 2100

Janairu: {{temp}}C ({{diff}} daga 1900)

Yuli: {{temp}}C {{diff}} daga 1900

Ta yaya hakan zai iya faruwa?

Hayaki mai gurbata mahalli zai karu nan da 2040 sannan ya ragu. Wannan ya danganta ne da irin matakan da aka dauka domin dakile sauyin yanayi.

Yanayi mai dan kyau Yadda yanayin zafi zai kasance a 2100

Janairu: {{temp}}C ({{diff}} daga 1900)

Yuli: {{temp}}C {{diff}} daga 1900

Ta yaya hakan zai iya faruwa?

Wannan ya yi daidai da yanayi mai karancin kyau, amma hayaki mai gurbata mahalli ba zai ragu ba har sai 2080.

Mummunan yanayi Yadda yanayin zafi zai kasance a 2100

Janairu: {{temp}}C ({{diff}} daga 1900)

Yuli: {{temp}}C {{diff}} daga 1900

Ta yaya hakan zai iya faruwa?

Wannan mummunan yanayi ne wanda hayaki mai gurbata mahalli zai ci gaba da karuwa a baki dayan karni na 21 ba tare da an dakile shi ba. Hakan kuma zai kai ga karuwar dumamar yanayin da 3C da zuwa 5C daga shekarar 2100.

Ba a san me gaba za ta haifar ba. Wasu daga cikin wadannan yanayin da muka lissafa za su fi saurin faruwa, sannan kuma za su dogara ne kan matakan da kasashe ke dauka.

Me hakan zai jawo?

Kwallon duniya da ke nuna inda New York yake
Birnin New York Amurka

Birnin New York yana daya daga cikin manyan birane a duniya, inda yake da mutane sama da miliyan takwas. Sai dai yana fuskantar barazanar ambaliyar ruwa da guguwa kamar guguwar Hurricane Sandy da aka yi a Oktoban 2012. Guguwar Sandy ta kwaranyo ruwa cikin hanyoyin karkashin kasa, wanda hakan ya jawo daukewar lantarki sannan kuma sama da mutum 50 suka rasa rayukansu.

Ana tsammanin sauyin yanayi zai jawo karin mahakautan guguwa mai dauke da ambaliyar ruwa. Sannan kuma tekuna su kara cika. Tazara tsakanin birnin New York da ruwa, wadda ta kai kilomita 1,500, ta sa garin cikin barazanar haduwa da matsalar sauyin yanayin. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Amurka ta kiyasta cewa, nan da tsakiyar wannan karnin daya cikin hudu na garin - inda kusan mutum miliyan daya ke zaune, zai kasance cikin ambaliyar ruwa.

Kwallon duniya da ke nuna inda Arctic yake
Yankin Arctic

Yankin Arctic yana cikin yankunan da sauyin yanayi ke damunsu, kuma yana dumama cikin sauri kamar sauran duniya. Saboda haka ana kallon hakan a matsayin "wani gargadi" game da abin da sauyin yanayi zai iya haifarwa.

Kamar sauran yankuna na duniya, ana kallon yankin Arctic a matsayin wata alama ta yadda duniya ke kara dumama. Amma Tekun Arctic yana lullube ne da kankara wadda ke narkewa lokacin bazara sannan kuma ta kara haduwa a lokacin hunturu. kankarar takan narke cikin sauri sama da yadda take haduwa, hakan yana jawo karewarta baki daya. Wannan ya kara bayar da gudummawa ga dumamar yanayi idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.

Kwallon duniya da ke nuna inda Jakarta yake
Jakarta Indunusiya

Babban birnin kasar Indunusiya, inda mutum miliyan 10 ke zaune yana daya daga cikin biranen da suke nutsewa a duniya Yankin arewacin birnin yana nutsewa a kan 25cm duk shekara a wasu yankunan. Saurin nutsewar na faruwa ne saboda yawan janyo ruwan karkashin kasa da ake yi wanda hakan ke haddasa cikar tekuna gami da dumamar yanayi. An gina shinge mai tsawon kilomita 32 a cikin ruwa da kuma tekuna da aka kirkira kan kudi dala biliyan $40 duka ndomin kare birnin.

Sai dai masana sun ce wannan matakin na dan wani lokaci ne. Sun ce a dakatar da duk wani aikin janyo ruwa daga karkashin kasa nan da shekarar 2050 yayin da birnin ke kokarin dogara kan wasu hanyoyin na samun ruwan sha. Amma cikar tekuna babban kalubale ne kamr yadda ta addabi sauran biranen kusa da teku. Cikar na da alaka da zafafar da ruwan karkashin kasa yake yi - tekunan na kara cika ne saboda karuwar zafi da kuma zagwanyewar kankara.