Bayanan cutar korona cikin zane mai motsi: Ta yaya za mu yi hasashen girman asarar rayukan da ke ta'azzara sakamakon Covid-19?

Irin wahalar da aka sha kan annobar cutar korona ta bayyana irin yadda shekarar 2020 ta kasance. BBC ta zayyana irin girman mace-macen da aka yi a fadin duniya ta hanyar amfani da fure - alamar da ke nuna tsananin bakin ciki da aminci da kuma soyayya.

Ka kalli annobar a matsayin fure . A cikin zane mai motsin da ke kasa furen na girma a yayin da yawan masu kamuwa da Covid-19 ke karuwa a tsawon lokaci, sannan ganyen na bushewa yayin da mutane ke mutuwa sakamakon cutar.

Dan tsaya, bayanan na tafe

latsa wajen sauti don sauraron annobar da aka bayyana ta cikin sauti.

Duniya ta samu kanta dumu-dumu a cikin bala'in Covid-19 a watan Afrilu, kamar yadda ganyen da ke girma yake nuna wa a wannan taswirar mai motsi.

Yawan mutanen da suke mutuwa ya fara hauhawa a karshen lokacin bazara a yankin arewacin duniya. Kuma ganyayyakin da ke nuna bayanai na baya-baya su ne mafi girma da ke nuna - yadda yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon Covid-19 a fadin duniya suka karu a yanzu fiye da yadda aka taba samu.

Ta yaya abin ya shafi nahiyoyi da yawa a duniya?

Zana fure ga kowace nahiya na bayyana yadda yawan mace-macen da ake yi a duniya ke karuwa a yayin da hankalin duniya ya fara kauce wa daga kan annobar cutar korona.

Raguwar yawan mutanen da annobar take kashewa a Turai da ya zo daidai da lokacin bazara, sai dai kuma an samu karuwar mace-mace a Kudancin Amurka a lokacin sanyi. Sannan a yayin da yawan wadanda suke mutuwa ya ragu a Kudancin Amurka, sai kuma ya sake karuwa a Turai.

Rana ta farko da annobar ta fara da misalin karfe 12

A wasu sassan ma an ga shigen irin hakan. Raguwar masu mutuwa a Kudancin Amurka - musamman a Amurka - ya faru ne saboda karuwar yaduwar cutar a nahiyar Asiya.

Rahotanni mace-mace da aka samu a Gabas Ta Tsakiya da Afirka sun ci gaba da kasancewa a kasa sosai. Yankin Oceania kuwa - da babu hotonsa a sama - ya tsira daga annobar.

ABin takaici, duk da ci gaban da aka samu na samar da riga-kafin Covid-19 da dama, har yanzu annobar ba ta nuna alamar wucewa. Kowace kasa tana wani mataki daban na yaki da cutar, Zabi kasa daga jerin kasasehn da ke kasa don ganin girman barkewarta sosai.

Ya annobar take a kowace ƙasa?

Dan tsaya, bayanan na tafe

Latsa nan domin ganin jadawalin ƙasashe masu Covid-19

Yi amfani da burauza ta zamani domin ganin cikakken bayani

Ana tunanin fara samun mutum na farko da ya kamu da Covid-19 a China cikin watan Nuwamba amma ba a da tabbacin yaushe. A ranar 31 ga watan Disamba, ma'aikatan lafiya a birnin Wuhan suka ba da rahoton cewa suna kula da mutane masu fama da cutar pneumonia. Kwanaki bayan nan, masana kimiyya suna gano cewa wata sabuwar ƙwayar cuta ce ta haddasa hakan.

An gano wanda ya fara kamuwa da cutar korona ranar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a ƙsar

Sabbin masu kamuwa da cutar

Yankin Wuhan ya sanar da mutuwar mutum 1,290 ranar 17 ga watan Afrilu abinda ya ƙara yawan mutanen da suka mutu a China da aka nuna a matsayin babban ɓangare na furannin kamar yadda yake a sama. Hukumomi sun ce an samu hauhawar ne sanadin ƙarin bayanai da mace-mace

Hanyar bincike

Ya ya furanni ke aiki?

Tsawon kowane itacen fure ya yi daidai da yawan masu kamuwa da cutar korona a kasar ko nahiyar ko duniya baki daya.

Kowane layi cikin zagayen furen na nuna ranar da aka fara annobar. Girman ganyen ya danganta da yawan mace-macen da aka tabbatar a kowace rana cikin wadancan ranakun.

Me sautin yake nufi?

Sautin ya yi daidai da tsananin bacin ran da aka kai a annobar cutar korona. Kadawar kararrawar na nuna yawan wadanda suka kamu da cutar, yayin da karar da cire furen ke nuna yawan mace-macen da ke karuwa.

Daga ina bayanan da ake gani suke zuwa?

Akasarin adadin masu cutar da waɗanda suka mutu na zuwa ne daga Jami'ar Johns Hopkins, duk da cewa ana amfani da bayanan Cibyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta Turai wadda ita ce ke ba da bayanan China da kuma duk wani bayani kafin 22 ga Janairu, a lokacin da aka fara samun bayanan Jami'ar John Hopkins. An yi amfani da bayanan gwamnati kan lamarin Birtaniya da Faransa.

Duka adadin ba su bayyana ainahin tasirin cutar korona ba. Idan yawan mace-macen suka wuce ƙima, adadin na ƙaruwa ne da dubun-dubata.

Za a iya samun bayanan da muke sabuntawa kan halin da ake ciki dangane da annobar a shafinmu da ke bibiyar yadda annobar take a duniya

Wadanda suka tsara aikin

Daga Irene de la Torre Arenas da Sarah Rainbow da Scott Jarvis da Adam Allen da Ed Lowther da Harriet Agerholm.