Mata Dari na BBC na Shekarar 2020

  • Boyayyar Gwarzuwa

    Fadin Duniya Kawo sauyi

    A shekarar da ta fita daban, da mata da ke fadin duniya suka sadaukar da kansu domin taimakon sauran jama`a, an bar gibi na 100 cikin jerin domin yaba wa aikin da suka yi, da kuma tuna wadanda suka rasa rayukansu a lokacin da suke fafatukar yin tasiri.

    Kodayake tsarin mata 100 na BBC ba zai iya ambaton kowacce mace da ke sassan duniya ba, da ta ba da tata gudunmawar, an tanadi wannan gurbi ne domin ba ka damar tuna mutanen da suka yi tasiri a rayuwarka a shekarar 2020.

  • Loza Abera Geinore

    Habasha Yar kwallon kafa

    An haifi Loza Abera Geinore, ta kuma yi kuruciyarta a wani dan kauye da ke kudancin Itofiya. Ta buga wa kungiyar Hawassa City SC a gasar wasan mata ta firimiya har kakan wasanni biyu, a lokacin ne ta zama wacce ta fi zura kwallo a raga

    A yanzun kwararriyar `yar wasan kwallon kafa ce, kuma `yar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar

    > Kowacce mace a duniya na iya cimma burinta da ta tsara wa kanta, duk runtsi.

  • Houda Abouz

    Maroko Mawakiyar Gambara khtek.17

    Houda Abouz Mawakiyar gambara ce da ta yi fice a irin wake-waken ta da salon kade-kaden ta

    Ta yi tsayin daka wajen kare hakkin mata. a ,tsayinta ta mai kidan gambara a fagen da maza suka yi kaka gida, Houda ta dauki kidin nata da wakar tata a matsayin abubuwan da take amfani da su wajen kawo canji.

    > ci gaba da gwagwarmaya, kirkira, tsayin daka, ba gudu ba ja da baya. Yanzu muka soma gwagwarmaya, kuma mune komai da Duniyar nan ke bukata: Iko na Mata

  • Christina Adane

    Netherlands 'Yar Gwagwarmaya christina.adane

    Christina ce kashin bayan korafin da aka yi a Ingila na samar da abinci kyauta lokacin hutu na zafi, da dan kwallon kafa Marcus Rashford ya goyi baya

    A matsayinta ta daya daga cikin shugabanni na Bite Back 2030, wacce gwagwarmaya ce ta yaki da rashin adalci a bangaren Abinci- kuma ta karbi abinci kyauta ita da kanta Christiana na so ta ga babu wani yaro da ke Ingila da ya kasance cikin yunwa

    > Kada ki taba ja da baya a gwagwarmayar ki ko abubuwan da kikayi imani da su. Domin kuwa babu wata mace da ta taba kawo sauyi ta hanyar ja da baya a cikin taro

  • Yvonne Aki-Sawyerr

    Saliyo Mai Mukamin Magajin Gari

    Magajin Gari Yvonne Aki-Sawyerr OBE ta yi suna ne a wani tsari da ta shirya na shekara uku na ciyar da Garin Firitawun, da ya shafi bangarori guda goma sha daya kama daga magance tabarbarewar muhalli da sauyin yanayi, zuwa taimawa samar da ayyukan yi domin rage rashin aikin yi na matasa a shekara. da matsalar muhalli tai kamari ga ambaliya, ga gobara da suka shafi miliyoyin jama'a a duniya, Magajin Gari Aki-Sawyerr ta karfafa wa mazauna Firitawun gwiwar shiga gangamin dasa itatuwa miliyan daya cikin shekara biyu.

    tsarin #FreetownTheTreeTown, na dashen itatuwa da aka kaddamar a watan janairu na 2020 ba tare da ko kwabo ba, zuwa watan Oktoba an dasa irin irin itatuwa fiye da 450,000, sauran aka bari sai daminar badi mai zuwa.an dasa itatuwan ne domin magance matsalar ambaliya, zaizayar kasa da kuma karancin ruwa.

    > Babu mamaki muna cikin kunci da rashin gamsuwa. bai kamata wannan ya ci gaba da illata mu ba; zamu iya sauya wannan ya zama alheri gare mu, don kaiwa ga sauyin da muke so mu gani.

  • Rina Akter

    Bangaladash Mai sana'ar Karuwanci a da

    Da aka shiga kullen Kwarona Rina da ayarin masu taimaka mata suna ba da abinci kusan 400 a mako da ya hada da shinkafa da gayyayaki na lambu da kwai da nama ga karuwai da ke Dhaka da suka tsinci kansu cikin halin yanayin rashin kwastomomi, da neman abin da za su ci

    > Mutane na yi wa sana'ar ta mu kalon kaskanci amma munayi ne domin samun na abinci, muna kokari mu tabbatar mata da suke wannan sana'ar ba yunwa ba kishirwa, kuma 'ya'yansu ba za su yi wannan sana'a ba.

  • Sarah Al-Amiri

    Hadaddiyar Daular Larabawa Ministar Ayyukan Kimiyyar kere-kere masu zurfi

    Mai Girma Sarah Al-Amiri karamar minista ce ta fasahar kere-kere mai zurfi ta Daular Larabawa, kuma shugabar hukumar kula da sarari samaniya ta Daular. a can baya itace jagorar ayyuka na kimiyya kuma mataimakiyar manaja na zuwa wata na Daular

    Wannan buri na zuwa Duniyar Mars na kasar shi ne zai zama na farko da wata kasa ta Larabawa za ta taba yi. shi kunbon da aka fi sani da suna Amal da harshen larabci, fata ta gari lamiri da harshen Hausa, ana sa ran zai isa tauraron mai launin ja a watan Fabrairu na 2021. bayanan da wadanda suka je suka tattaro daga watan, shi zai taimaka wa masu ilimin kimiyya yin nazarin yanayin duniya

    > Kwayar cutar da ta bukaci duniya tsyawa kacokan, wanda akan hakan ne mukayi tsayin daka domin waiwaye da kuma cigaba a matsayin mu na daddaiku. muna bukatar mu hada karfi waje guda domin cigaba da bunkasa, da kuma tabbatar da dorewa daga cikin wannan duniya ta mu mara tabbas.

  • Waad al-Kateab

    Siriya Mai Shirya Fina-Finai

    Waad al-Kateab 'yar gwagwarmaya ce ta kasar siriya, 'yar Jarida, mai shirya fina-finai da ta samu lambobin yabo, da ta samu kyaututtukan yabo masu yawan gaske (ciki harda ta Emmy) saboda rahotannin labaru a Aleppo. A shekarar 2020 kyautarta ta farko ta SAMA, ta ci lambar yabo na BAFTA da tafi iya ba da bayanai, kuma aka ba da sunanta domin ba da lambar yabo ta Acedemy saboda wannan bayanai/fita.

    Saboda rasa matsugunninsu a Aleppo a shekarar 2016 Waad da mijinta da 'ya'yansu mata biyu yanzu haka suna zaune a Landan, inda Waad ke aiki da tashar Channel 4 News da kuma jagorantar gwagwarmayar fadi da cikawa ta Sama.

    > Mukan rasa nasara ne idan muka hakura. ga dukkan mata koma a ina suke ya kamata ku cigaba da gwagwarmayar abubuwan da kuka yi imani da su, saboda haka babu batun mika kai ko gazawa

  • Adriana Albini

    Italiya Kwararriya wajen Nazarin Cututtuka

    Adriana Albini itace shugabar dakin bincike na ayyukan lafiya na IRCCS da kuma nazarin kwayoyin halitta na jijiyoyin jini da kuma gidauniyar MultiMedical Foundation; Farfesa ta nazarin cututtuka a jami'ar Milan-Bicocca; kuma tsohuwar jami'ar kimiyya mai bakuntar cibiyoyin lafiya na Amurka

    Ita ce yar kasar Italiya ta farko da aka zaba cikin hukumar daraktoci ta kungiyar binciken cutar sankar ta Amurka. A matsayinta ta shugabar kulob din matan Italiya da ke kan gaba bangaren kimiyya a gidauniyar sanya ido a kan al'amuran lafiyar mata ta kasa, har ila yau ita ce zakara inda ta ci tagulla a gasar kwararru ta cin kofin duniya ta 2018 ta kuma ci azurfa a gasar zakarun Turai ta 2015

    > Masu Bincike kan soma aikinsu ne ta hanyar bin turbar da masu ilimin kimiyya suka tsara wacce turbar ce da ta kakare a hanya. dole ne mata masu ilimin kimiyya su yi amfani da baiwar da Allah Ya yi musu wajen lalubo turbar da babu wanda ya lura da ita.

  • Ubah Ali

    Kasar Somaliya Mai Ilimantarwa bangaren hana yiwa mata kaciya

    Ubah Ali a matsayinta ta daya daga cikin wadanda suka kafa gidauniyar sauqi ga 'yan matan Somaliya, wacce gidauniya ce da ta mike tsaye wajen ganin ta kawar da dukkannin wani nau'i na yiwa mata kaciya ta hanyar ilmantarwa da kuma karfafa mata.

    Ali har ila yau 'yar gwagwarmaya ce ta kare hakkin 'yan ci rani da ke lebanon, domin kuwa ta yi karatu ne a jami'ar Amurka da ke Beirut.

    > Duniya ta samu dumbin sauye sauye a shekarar 2020. akwai kiran gaugawa na neman hadin kan mata dake duniya- mata da dama na fama da tashin hankali na gida, da fyade da yi musu kaciya da sauransu. idan akwai hadin kai mata na iya neman ayi musu adalci

  • Nisreen Alwan

    Iraki/Ingila Kwararriyar Likita

    Nisreen likita ce ta jama'a kuma malama a Ingila da tayi bincike bangaren lafiya da kyautata jindadin mata da yara, inda ta maida hankali akan juna biyu

    A lokacin Kwaronabairos, ta fadakar akan bukatar kasashe su dauki matakai don magance ba mutuwar iyaye mata kadai ba har ila yau doguwar jinya sakamakon cutar, (ciki harda cutar Kwaronabairos). mutanen dake da Kwarona kan bayyana alamomi irinsu gajiya da ciwon kai da daukewar numfashi

    > A Shekarar 2020 na yi karin abubuwa guda 3; bayyana abubuwan dake cikin zuciyata,yin abinda nake tsoro da yafewa kaina. sannan na rage abubuwa guda 3; rage damuwar da abubuwan da mutane suke tunani a kaina, zargin kaina da kuma imanin cewa kana nake da saura.

  • Elizabeth Anionwu

    Ingila Ma'aikaciyar jinya/Nas

    Farfesa Dame Elizabeth Anionwu mai matsayin gaba da farfesa ce a bangaren jinya a jami'ar West London/Landan ta yamma kuma uwar kungiyar masu yaki da cutar amosanin jini ta ingila

    Farfesa ce da ta taka rawar gani bangaren jinyar masu amosanin jini da cututtuka na gado da suka jibanci jini wacce tayi gwagwarmayar ganin anyi mutum-mutumi na Mary Seacole Nas yar kasar Jamaica da ke Birtaniya. ta zama wata jigo wajen wayar da kan jama'a a kan illar cutar kworonabairos ga al'umomin BAME.

    > ka da ki taba raina gagarumar gudunmawar da ke da sauran mata ke badawa a duniya.

  • Nadeen Ashraf

    Misra Yar Gwagwarmaya actuallynadeen

    Nadeen daliba ce ta Falsafa da tayi imani a cewa soshiyal midiya kafa ce ta kawo canji. Babban burinta shine yada ilimi ta yadda ze kai ga kowa cikin sauki

    Nadeen ita ce ta kirkiro da dandalin instagram akan cin cin Zarafi na 'yan sanda da mata da ke kasar Misira/Masar zasu iya bayyana labarinsu na cin zarafinsu bangaren lalata

    > Na tashi na girma kewaye da mata da suka sadaukar da rayuwarsu ga gwagwarmayar kawo sauyi/canji; ban taba tunanin zan tsinci kaina a matsayin mai magana da yawunsu ba. Ba ka taba makara ga soma aiwatar da abin da ka yi imani da shi.

  • Erica Baker

    Jamus Injiniya

    Erica darakta ce bangaren Injiniyanci a GitHub. Tun shekara 19 da suka wuce Erica ta soma aiki bangaren fasaha inda ta ke samar da tallafin ayyukan fasaha ga jami;ar Alaska kafin daga bisani a 2006 ta koma Google/Gugul.

    Ta soma aiki da Slack a 2015 da kuma Patreon a 2017 kafin ta tsunduma Microsoft sannan ta koma GitHub. Erica na cikin hukumomin bada shawara a Atipica da Hack the Hood da Cord.org Diversity Council da Barbie Global Advisory Council Board, da hukumar daraktoci na Girl Develop It, kuma jigo ce ta fasaha ga Black Girls Code. a yanzu haka Erica na zaune a Oakland ta Carlifornia/Kalifoniya.

    > Duniyar ta yi matukar sauyawa a shekarar 2020, kuma a daidai lokacin da muke sake koyon zama masu aiki tukuru da muhimmancin aikida amfanin sanin kowa, har ila yau ana tunatar damu cewa duniya ba daidai ta ke ga kowa ba. Ina karfafawa mata da ke fadin duniya suyi amfani da ikon da suke dashi wajen yakar rashin adalci da yakar 'yanci da tabbatar da an yiwa dukkanmu adalci.

  • Diana Barran

    Ingila Minista A Gwamnatin Ingila

    A shekarar 2019 an nada Baroness Barran ministar Kungiyoyi na al'umma na Ingila, sannan ita take da alhakin yin tsare-tsare da suka jibanci ofishin kungiyoyin al'umma. ita ta kafa Gidauniyar SafeLives kuma tsohuwar babbar shugabanta wacce gidauniya ce ta kasa da aka sadaukar da ita da kawo karshen cin zarafin mata a cikin gida. har ila yau itace tsohuwar jagoran tallafin cigaba a wata sabuwar kungiya ta kwararru, sannan ta yi aiki bangaren alkinta kadarorin kungiyar kafin kafa daya daga cikin asusun tallafi na Turai a shekarar 1993.

    Baroness Barran na cikin amintattu na gidauniyar agaji ta Royal Foundation, kuma shugabar kungiyar tallafi ta Henry Smith. Ta samu lambar yabo ta Beacon ta Ingila a 2007 kuma ta zama MBE a shekarar 2011 saboda kokarin da ta yi wajen magance matsalar tashe-tashen hankula a cikin gida

    > Nakan tuna kalaman Maya Angelou;"Mutane sukan manta abinda ka fada, Mutane sukan manta abinda ka aikata, sai dai mutane basu taba manta yadda ka kyautata musu ba".

  • Bilkis

    Indiya Shugabar Zanga-Zanga

    A lokacin da take da shekara 82 a Duniya Bilkis na cikin wata kungiya ta mata da suka yi zanga-zangar lumana a kan wata doka ta dan kasa.

    Ta zama ita kadai ake jin duriyarta a zanga0zangar da aka dade ana yi a babbar birnin Shaheen Bagh, yankin da musulmi suke inda akayi zanga-zangar. 'Yar Jarida ta kasar Indiya kuma marubuciya Rana Ayyub ta kwatanta ta a matsayin muryar wadanda ake nuna wa wariya.

    > Ya kamata mata su yunkura domin ficewa daga gidajensu da daga muryoyinsu musamman inda suka ga ana rashin adalci. In ba sun fito daga gidajensu ba ta yaya za su nuna suna da karfi?

  • Cindy Bishop

    Tailan Jakadar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya cindysirinya

    Bishop Cindy Siriniya 'yar wasa ce abar koyi da ke jagorantar shirye-shirye na gidan talabijin, wacce har ila yau ke gangamin kawo karshen cin zarafin mata. A wannan shekarar aka nada ta Jakadar fatar alheri ta mata ta Majalisar Dinkin Duniya ga yankin Asiya da Fasific, da ke daukaka daidaiton jinsi ta hanyar ilimi da gwamnatoci. Ta kafa kungiyar #DontTellMeHowToDress a 2018 bayan hukumomi da ke kasar Tailan sun hana mata shiga mai bayyana tsiraici in har suna so su kaucewa cin zarafinsu a wajen bukukuwa na sabuwar shekara na kasar Tailan

    Har ila yau Darakta ce ta ilimi ta DragonFly360, wanda dandali ne na yanki da ke gangamin daidaiton jinsi a Asiya, sannan tana rubuta littattafai da dama na yara akan kare lafiya da hakkoki da mutunta zumunci.

    > An samu dunbin sauye-sauye a duniya a 2020. Canji kan zo da dama ta ci gaba. Ya kamata a ba kowa damar zama daya da walwala. dole ne mu cigaba da karfafa gwiwar zuri'a ta mata da maza da ke tasowa.

  • Macinley Butson

    Austireliya Mai Ilimin Kimiyya da Kirkire-Kirkire

    Macinley Butson ta soma kirkire-kirkire ne tun lokacin tana yar shekara 7 a yanzu da take 'yar shekara 20 ta kirkiro na'urori daban-daban dake da manufar kyautata sakamakon Na'urar kashe kwayoyin cutar sankara, da sankarar mama/nono da samar da tsaftateccen ruwan sha ga kasashe da ke tasowa.

    Ta zama abin koyi ga matasan Autireliya da ke tasowa inda take nuna musu yadda zasu tallafa wa al'umma ta hanyar kimiyya da fasaha da Injiniyanci da lissafi

    > Babu wani abu da ke iya yin shamaki ga burin kawo canji. ina kira ga kowace mace da ke fadin duniya ta tambayi kanta, "In ba ni ba, to sai wa? In ba yanzu ba, to sai yaushe?"

  • Evelina Cabrera

    Arjantina Mai Horas da 'yan wasa kuma Manajar Kulob evelinacabrera23

    An Haifi Evelina a wani mawuyacin hali na cin zarafin mata amma wannan bai hana ta zama mai horas da 'yan wasa kuma manaja ta kulob din kwallon kafa. Tana 'yar shekara 27 ta kafa kungiyar kwallon kafa ta mata ta Arjentina.

    Ta kafa kungiyoyin kwallon kafa masu yawan gaske( a cikinsu har da kungiyar kwallon kafa ta mata masu lalurar gani), ta horas da fursunoni ta taimakawa mata da 'yan mata da ke mawuyacin hali ta hanyar kwallon kafa da ilimi. tana daya daga cikin mata manajojin kungiyoyin kwallon kafa a Arjentina, ta wallafa tarihinta dake bayanin gwagwarmayar da ta yi ta kare hakkin mata.

    > Bai kamata jinsin mu ko asalinmu ya zama shi ne zai iya tantance alkiblarmu ba. Turba ce mai wuyar gaske, amma idan aka hada karfi za'a iya cimma daidaito.

  • Wendy Beatriz Caishpal Jaco

    El Salbador Yar gwagwarmayar kare hakkin masu cutar nakasa wendy_caishpal

    Wendy Caishpal 'yar kasuwa ce, 'yar gwagwarmaya, mai maganganu na karfafa gwuiwa, kuma muryar 'yancin mutanen da ke da lalurar nakasa kuma wacce ta rayu daga cikin takaddama ta makamai.

    Ita ce wakiliyar El Salvador a cibiyar mata ta shugabanci da lalurar nakasa da kai komo ta duniya da ke Amurka. Har ila yau itace ta kafa kungiyar Ahuachapan Sin Barriers(Ahuachapan mara shamaki), wanda aiki ne na cikin birni da ke daukaka hakkokin masu lalurar nakasa da kare su a yankin.

    > Dole mu kaunaci abin da muke yi; yadda muke yi. ya kamata mu zama ginshikin kawo ci gaban zamantakewa; mu yunkura, mu yi gwagwarmaya domin kawo canji. Idan kowa da kowa ya shiga wannan gwagwarmaya, za mu samu kyakyawan makoma a duniya.

  • Carolina Castro

    Ajentina Shugabar Kungiyar Kwadago

    Carolina Castro ita ce mace ta farko da ta kai mukamin shugabanci a kungiyar kwadago ta Ajentina a tarihin kungiyar da ta kai shekara 130 a duniya Gwagwarmayarta ta taimaka gaya ga cigaban gwagwarmayar mata a jam'iyu a kasar da ake yi wa muhawara ta bainar jama'a fahimta daban-daban.

    Castro ita ce jagorar zuri'a ta 3 na kamfanin sarrafa kayan gyara na motoci na iyali da ya kafa tarihita hanyar daukan mata aiki a albashin da ya zarce na kasuwa a kwanakinnan ta wallafa Rompimos el Cristal("Mun fasa Gilashin"), bayanin tattaunawa da mata18 'yan kasar Ajentina da suka yi fice bangaren kasuwanci,fasaha da siyasa da kimiyya.

    > Ajandar gwagwarmayar daidaito ba wasu mutane ne na daban ke daukaka su ba illa kowannenmu na kowane jinsi daidai gwargwadon zabi da za mu iya yi.

  • Agnes Chow

    Honkwan Yar gwagwarmayar Goyon Bayan Dimukradiyya chowtingagnes

    Agnes Chow 'yar shekara 23 a duniya mai gwagwarmayar goyon baya dimukradiyya a Honkwan jigo ce a lokacin gwagwarmayar lema ta 2014. a wannan shekarar tana daya daga cikin 'yan gwagwarmaya kalilan da aka kama a karkashin sabuwar dokar tsaro mai shirbici da bangaren tsaro na Bejin ya kafa, an zargeta da laifin hada baki da dakaru 'yan kasashen waje.

    Tuni aka ba da belin ta sai dai wannan kama ta da aka yi ya sa ta samu gagarumar goyon baya tun tana 'yar shekara 16 take siyasa ka'in da na'in. Masu goyon bayanta suka sa mata suna "Mulan", sunan wata gwarzuwa 'yar kasar Caina/Sin da tayi yaki don ceton iyalinta da kasar.

    > Zama jagora ta mata ba yana nufin wani abu bane ga hakkokin mata. muna bukatar canji a tsarin da kuma Dimukradiyya ta zahiri.

  • Patrisse Cullors

    Amurka Yar Gwagwarmayar kare Hakkin bil'Adama

    Mai tsarawa, Mai ilmantarwa, wacce ta yi suna a iya magana a cikin jama'a Patrisse Cullors 'yar asalin Los Angeles ce, daya daga cikin wadanda suka kafa gidauniyar kawancen al'amuran da suka shafi rayuwar bakake ta duniya kuma babban daraktan kungiya, sannan wacce ta kirkiro kungiyar martaba da iko a yanzu wacce kungiya ce ta karkara da ke Los Angeles

    A yanzu haka Patrisse ita ce daraktar tsangaya a kwalejin Presscott da ke Arizona ta sabbin aikace-aikace na zamntakewa da muhalli da ita ta tsara su.

    > Kada ki taba baras da ikon ki. Tsara jin dadin ki, ki kuma bukaci canji, ba don kanki kadai ba - amma domin sauran mata da zasu biyo bayanki

  • Tsitsi Dangarembga

    Zimbabiwe Marubuciya kuma mai Shirya Fina-Finai

    Tsitsi fitacciyar marubuciya ce mai shirya fina-finai kuma 'yar gwagwarmayar al'adu. Ta rubuta littattafai da suka ciyo lambobin yabo da aka dauke su a matsayin adabi na kasar Zimbabiwe, sannan an nuna fina-finan ta a wuraren bukukuwa da akayi a sassan duniya ciki har da fim din bikin al'adu na Sundance.Tana zaune a Harare, ta na aiki da mata masu rubuta fina-finai na afirka.

    Tsitsi na daya daga cikin wadanda aka tsare saboda shiga cikin wata zanga-zanga a zimbabiwe a wannan shekarar, da masu zanga-zangar suka zargi gwamnati da laifin aikata rashawa da rashin iya mulki. An ba da belinta bayan an tuhume ta da laifin zuga jama'a su ta da zaune tsaye da karya dokokin lafiya da aka bullo da su domin dakile yaduwar kwaronabairos. Abokanta marubuta sun yi kiran a janye tuhumar da ita kanta tace bata aikata ba.

    > Kada ki ji tsoron canji. Ki sanya shi ya zama canji mai ma'ana gare ki.

  • Shani Dhanda

    Ingila Mai Gwagwarmayar kare hakkin masu lalurar Nakasa

    Shani Dhanda kwararriya ce bangaren samun lambobin yabo na masu lalurar nakasa kuma 'yar kasuwa da ta samu yabo a matsayin daya daga cikin masu lalurar nakasa da suka fi yin tasiri a Ingila. Shani ce ta kirkiro da kungiyar mata masu lalurar nakasa da ke Asia, take kuma cigaba da jagorantarta, Da kuma wata kungiyar ta ayyuka daban-daban

    Dukkan fage guda 3 da aka rikirkita an hade su ne ta hadaddiyar gwagwarmaya karkashin al'umomin da aka wakilta.

    > A daidai lokacin da duniya ke farfado wa hakkn mu ne mu taru domin sake tsara al'kibla mai dorewa da kowa ke ciki domin ci gaban kowa da kowa.

  • Naomi Dickson

    Ingila Babbar Shugaba

    Naomi ta sadaukar da rayuwarta a matsayinta ta kwararriya ga tallafa wa mata da yara Yahudawa da suka yi fama da cin zarafi a cikin gida da ilmantar da al'ummar Yahudawa domin samun kwakkwaran ginshiki na tona cin zarafi a cikin gida da za'a iya kauce musu a yanzu da kuma nan gaba.

    A mtasayinta ta babbar shugabar kungiyar agaza wa mata Yahudawa, Naomi na jin dadin aiki da mata mabiya dukkan addinai, da ilmantar da a'ummomi da shugabannin addini domin samar da duniya da babu dukkan wani nau'i na cin zarafin mata da yara mata kanana.

    > An samu dinbin sauye-sauye a duniya a shekarar 2020 mun kuma koyi yin namu tsayin dakan domin iya taimaka wa saura.

  • Karen Dolva

    Nowe Mai Fasahar Kirkire-Kirkire

    Karen Dolva ce babbar shugaba kuma daya daga cikin wanda suka kirkiro kamfanin Ba Killacewa wacce ke Oslo a watan Oktoba na shekarar 2015. Burinta shine tattaro mutane wuri guda ta hanyar fasaha da ilimi.

    Zuwa yau, kamfanin ya samar da kayayyaki guda biyu: AV1 wacce na'ura ce da ke magance kadaici a tsakanin yara da matasa da doguwar jinya ta shafa, da KOMP, wacce na'ura ce mai maballi guda da aka tsara musamman domin dattawa suyi amfani da ita.

    > Bai kamata mu ce Kwaronabairos ce ta dakatar da mu daga gwagwarmaya ba. Ya kamata ya zama amsa kira ne: wandanda ba su da karfi su lamarin yafi shafa, dole muyi amfani da wannan lokaci wajen kawo canji da kare wadanda ke cikin mawuyacin hali.

  • Ilwad Elman

    Somaliya Mai Gwagwarmayar Zaman Lafiya

    Ilwad Elman matashiya ce shugaba da ke kan gaba wajen tabbatar da an zauna lafiya a somaliya, kuma mai fada a ji a duniya a bangaren kawo karshen takaddama da sasanta al'umomi

    Tana 'yar shekara 20 kawai ta zama daya daga cikin wadanda suka kafa cibiyar rikice-rikice da suka shafi fyade. A shekarun da suka gabata Ilwad ta kasance kan gaba wajen gina zaman lafiya ta hanyar yin tasiri ga mata da yara 'yan mata da rikici ya shafa dama ta ba da gudunmawa.

    > Cutar ta jefa duniya cikin mawuyacin hali. mun ga mata na shugabanci a inda wasu suka gaza. Dole ne a daina daukar mata da ke kan shugabanci a matsayin rashin zabi, illa babban abin mayar da hankali a kai.

  • Jeong Eun-kyeong

    Koriya ta Kudu Kwamishinar KDCA

    An kwatanta Likita Jeong Eun-Kyeong a matsayin "mai farautar kwayoyin cututtuta" kuma ta jagoranci dakile cutar Kwaronabairos a Koriya ta Kudu

    A matsayinta ta kwamishinar Hukumar yaki da kuma rigakafin cututtuka ta koriya a halin yanzu haka (KCDA) - da a can baya ta zama ita ce babbar shugaba mace ta farko ta yi suna wajen gaskiya da kwantar da hankalin jama'a da takeyi kullum a bayanan da ta ke wa jama'a a kan cutar.

    > Ina matukar jinjina da yabawa dukkan ma'aikatan lafiya da su ka sadaukar da rayuwarsu ga yaki da cutar . Zan yi matukar kokarina wajen taimakawa duniya zama mara cututtuka ta hanyar karfafa yaki da cutar.

  • Fang Fang

    Caina/Sin Marubuciya

    Fang Fang wacce ainihin sunanta shi ne Wang Fang, marubuciya ce ta kasar Caina da ta wallafa littattafai fiye da 100 da kuma samun lambobin yabo. A wannan shekarar ta soma tattara abubuwan da suka faru a Wuhan garin da cutar Kwaronabairos ta soma barkewa. Wadannan bayanai da ta tattara sun baiwa miliyoyin 'yan Caina sanin abubuwan da basu iya gani ba a birnin, kuma ta rubuta komai kama daga kalubalen da aka dinga fuskanta a kullum da kuma tasirin kaiwa ga killacewa.

    Da yake wannan rubutu na ta ya cigaba da jan hankalin duniya har aka fassara shi cikin harshen Ingilishi, sai martanin da ake mayar mata a kan wadannan bayanai suka karu cikin hanzari ta intanet, 'yan Caina da dama ransu ya baci har suka kira ta a matsayin mai cin amanar kasa.

    > ki zama mai 'yancin kanki.

  • Somaya Faruqi

    Afaganistan Jagorar Ayarin 'yan Mutum-Mutumi

    Da aka soma ba da rahoton barkewar cutar Kwaronabairos ta farko a lardin garinsu na Herat, Somaya da dukkan ayarinta mata da ake kira da "Afghan Dreamers" wato masu mafarkin Afaganistan, suka mike tsaye domin kera na'urar taimakawa numfashi mai saukin kudi domin warkar da masu jinyar Kwaronabairos.

    Somaya da ayarinta na nan suna shirin nuna tsarin nasu ga ma'aikatar kula da lafiyar jama'a. Idan an amince da wannan fasaha tasu za ayi amfani da ita a asibitoci da ke yankunan karkara. Somaya da aka haifeta a shekarar 2002 ta sama lambobin yabo masu yawan gaske ciki harda kyautar azurfa ta kwazo a FIRST Global Challenge ta duniya, don yabawa da kokarinta bangaren kimiyya da fasaha a Amurka, a wajen wani taro na duniya na ba da lambobin yabo da kuma wata lambar yabo ta bikin fina-finai da kuma wani biki na mutum-mutumi a Estonia na kasashen Turai.

    > Mabudin ci gabanmu ya ta'allaka ne ga abubuwan da muke koya ma yaranmu 'yan mata da samari a yau. ya kamata mu tabbatar da kowane yaro ya samu ilimi iri daya, kuma sinadarin tabbatar da burinsu ya cika.

  • Eileen Flynn

    Jamhuriyar Ailan Sanata

    Eileen Flynn ta kafa tarihi a wannan shekarar a matsayinta ta mace ta farko daga al'umar 'yan kasar Ailan matafiya da ta taba zama a majalisar dattawa ta Ailan.

    A yanzu haka tana amfani da matsayinta wajen taimaka wa 'yan kasar Ailan matafiya da sauran al'umomi da ake nuna musu wariya. babban burinta shi ne bullo da dokar mayar da kiyayya a matsayin babban laifi a Jamhuriyyar Ailan.

    > Ku kula da juna; ku mika wa juna hannu; kada ku taba kokarin tunkude wata matar kasa. Kashe wutar kyandir din wata ba zai taba kunna naki kyandir din ba. Idan muka yi tsayin daka baki daya, mu na iya girgiza duniya.

  • Jane Fonda

    Amurka Yar Wasa

    Talabijin, Jane Fonda sau biyu tana lashe lambobin yabo na Academy Awar-winning Actress, da tayi fice a fina-finai irinsu Klute, Coming Home, On Golden Pond, 9 to 5 da sauransu. A yanzu haka itace tauraruwa a Fina-finan Kamfanin Netflix mai suna Grace and Frankie.

    A bayan fage kuwa ta kasance kan gaba a gwagwarmaya fiye da shekara 50 da ya sanya muryarta ta taimaka ga kwato hakkin mata har ake biyansu albashi mai tsoka, sannan a baya bayannan ta kaddamar da Fire Drill Fridays da tare da Greenpeace ta Amurka da ke nunawa duk mako domin ilmantarwa da kuma nuna rashin amincewa da matsalar yanayi/muhalli.

    > Duniyar sai kara dumama takeyi ba kakkautawa fiye da yadda masu ilimin kimiyya suka yi hasashe. bil'Adama na cikin matsala ta kawar dashi daga doron kasa. Hakan na bukatar hada kai domin magance matsalar. Mata sun fahimci cewa dukkanmu mun dogara da juna su matsalar muhalli ke shafa kuma su ne za su jagorance mu ga magance matsalar. Ya kamata mu mike don hakan.

  • Kiran Gandhi

    Amurka Mawakiya

    Kiran Gandhi da ke kade-kade da wake-wake a matsayin Madame Gandhi, wanda burinta shi ne daukaka kare hakkin mata tana ta rangadi wadda tana kida tana rawa kamar su MIA da Hukumar Thievery Corporation.

    A kwanakin baya ta gudanar da guje-guje na Landan mai taken "free bleeding" domin kawar da kyama da ake nuna wa masu jinin al'ada

    > Saboda yawancinmu sai sun sake tsara ayyukansu domin yin aiki daga gida. a zahirin gaskiya dama ce ta fita da tsafta domin kai wa ga haihuwa/reno. Muna da baiwa ta sake tsara al'amuranmu domin su tafi daidai da bukatunmu.

  • Lauren Gardner

    Amurka Mai Ilimin Kimiyya

    Lauren Gardner Farfesa ce bangaren Injiniyanci a jami'ar Johns Hopkins, sannan daya da ga cikin daraktocin cibiyar kimiyya da injiniyanci.

    Gardner ta jagoranci ayarin da ya samar da na'urar bibiyar cutar kwaronabairos wacce ta zama hukumar da ke samar da bayanai da gwamnati da cibiyoyin bincike na dakile cututtuka da kafofin yada labarai da ke duniya ke samun bayanai a kan cutar daga gareta.

    > Kada ki tsaya kina neman izini. Nemi wajen zama ki zauna domin yin abin da ya dace.

  • Alicia Garza

    Amurka Yar Gwagwarmayar kare hakkin bil'Adama

    Alicia Garza Wacce ke tsara dabaru na siyaya kuma marubuciyar The Purpose of Power: How We Come Together When We Fall Apart.

    Ita babbar jami'a ce ta asusun Black Futures Lab And The Black to the Future Lab kuma daya daga cikin wanda suka kirkiro kungiyar Black Lives Matter and the Black Lives Matter Global; Sannan darakta ta tsara dabaru da kawance a wata kungiyar gamayyar ma'aikata da ke aiki a cikin gida ta kasa har ila yau daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Supermajority sannan wacce ta karbi bakuntar Lady Dont Take no Podcast.

    > Tsayin daka da kafafu, Kai a sama, Idanu a kwazo.

  • Iman Ghaleb Al-Hamli

    Yemen Manajar Makamashi

    Iman ta tafiyar da wata kungiya ta mata guda 10 da ta kafa makamshin ta amfani da hasken rana, makamashi mai tsafta da bai da illa sosai, mil 20 daga inda yakin yakin basasa na Yemen ya daidaita.

    Shi wannan makamashi na Microgrid na daya daga cikin guda 3 da shirin ayyukan raya kasa na Majalisar Dinkin Duniya ya samar a yankunan Yemen da basu da lantarki kuma guda daya tilo da ilahirin mata ke amfani da shi. Da farko ana ta yiwa ayarin na Iman iya shege da shegantaka cewa sun je suna aikin maza. To tun daga lokacin suka sa aka soma mutunta al'umarsu a daidai lokacin da kuma suke samar wa kansu kudaden shiga da kuma samar da sabbin sana'o'i.

    > Sakona ga dukkan 'yan mata da ke Yemen shi ne su kokarta don cika burinsu dole su cire duk wani tsoro su fuskanci dukkan kalubalen da ke tattare da rayuwarsu domin kaiwa ga gaci.

  • Sarah Gilbert

    Ingila Mai Ilimin Kimiyya

    Masu ilimin kimiyya na kasar Caina suna wallafa bayanin kwayoyin hallittar sabuwar cutar Kwaronabairos, sai Sarah da ayarinta a Oxford suka bazama aiki kuma tuni suka kirkiro da rigakafin Kwaronabairos da a halin yanzu haka yake mataki na 3 na gwaji.

    Mai ilimin kimiyya da ta sami horo a bangaren Nazarin kwayoyin halitta da ido baya iya gani da kimiyyar nazarin halittu da nazarin kwayoyin cuta da ilimin samar da magunguna na rigakafi, Sarah tana ta aiki tukuru domin samar da magungunan rigakafin cututtuka da ke ta kunno kai tun shekarar 2014.

    > Za mu iya yin wadatacciyar jurewa domin kaiwa ga karshen shekararnan. Lokaci yayi da za'a maida hankali ga ainihin al'amura: lafiya, ilimi da kuma kyakyawar dangantaka da saura.

  • Maggie Gobran

    Masar/Misira Ma'aikaciyar Coci stephenschildrenus

    Mama Maggie Gobran ta sadaukar da rayuwarta ga kyautata rayuwar yara da aka nuna wa wariya a Masar. Ta yi watsi da rayuwar jin dadi kuma fitacciyar 'yar boko, ta sadaukar da dukkan karfinta da arzikin ta ga kula da yara, ta wanke musu kafafuwa, sannan ta kalli idanunsu ta ce musu kuna da amfani.

    Tun shekarar 1989, Maggie da ayarinta suka tunkari kyautata rayuwar dubban yara, ta kyautata jindadinsu da iliminsu da lafiyarsu, sannan uwa uba mutunci/martabarsu.

    > Idan kika sasanta da kanki, to za ki sasanta da duniya da lahira.

  • Rebeca Gyumi

    Tanzaniya Lauya

    Rebecca Gyumi ita ce ta kafa, sannan babbar darakta a kungiyar Msichana Initiative, wacce kungiya ce ba ta gwamnati ba da ke fafutukar kare hakkin yara 'yan mata. 'Yar gwagwarmayar kare hakkin mata ce, kuma tana da kwarewa sosai bangaren aiki da matasa da kafa kungiyoyin ci gaban mata da samar da gwagwarmaya a matakin kasa da yankunan karkara.

    A 2019, kungiyar Msichaina ta samu nasara a wani hukunci da kotun daukaka kara da ke Tanzaniya ta yanke, da ya haramta yi wa yara 'yan mata kanana aure har sai sun kai a kalla shekara 18.

    > Komai ya yi zafi maganinsa Allah. Mu kara dukufa ga cigaba da gwagwarmaya da magana da murya daya da gudunmawar da muke bayarwa har sai mun cimma ajendar kare hakkin mata bangaren daidaito.

  • Deta Hedman

    Jamaika Zakara a wasan jefa kibiya

    Deta na aiki da daddare a Royal Mail har tsawon shekara 22. ta ci gasar jefa kibiya har so 215 wato ta biyu a dukkan wasannin Phil Taylor ce kadai ta doke ta. Ta kai gasa ta karshe har sau 341 fiye da duk wani a tarihin gasar. Deta ta isa Ingila a 1973 kuma a yanzu ita ce kyaftin ta kungiyar wasan jifar kibiyar ta Ingila.

    Jakadiya ce kungiyar charity Heart ta wannan wasa, da kuma a kungiyar matasa dake wannan wasa ta Ingila sannan ta kasance a hukumar wasannin jefa kibiya ta duniya a matsayin wacce ta wakilceta a wasan. Ta yi na daya a duniya har sau 11 kuma ita ce ta 2 'yar wasa da aka fi jinjinawa a kungiyar mata ta Ingila.

    > Zanyi kira ga dukkan mata ku dage don cimma burinku kada ku taba ba da kai bori ya hau. Shekaru, macentaka da jinsi ba dalilai ne na kasa kaiwa ga nasara ba. wannan dama ce guda daya da ya kamata ku yi kyakkyawar amfani da ita #Believe.

  • Muyesser Abdul’ehed

    An sa ta yin gudun hijira daga Ghulja da ke kasar Caina, Yining. Marubuciya

    Muyesser Abdul'ehed wacce aka fi sani da Hendan ta soma yin suna ne a matsayin mawakiya kuma marubuciyar Insha'i a lokacin da take karatun likita. A lokacin da ta kammala karatun Digirinta na 2 a bangaren kula da lafuyar al'umma sai ta yanke shawarar mayar da hankali ga rubutu. Bayan ta sauya matsuguni zuwa Turkiya a 2013Hendan ta kafa kungiyar ilimi ta Ayhan wacce kungiya ce da ta dukufa ga koyarwa cikin harshen Uighur a kasashen ketare. A yanzu haka tana Istanbul.

    Littafin Hendan mai suna Kheyr-Khosh (Bankwana da Rana) na kwanan nan da ya yi fama da rikicin da ke aukuwa a garinsu. Shi ne kagaggen labari na farko da ya maida hankali ga abubuwan da suke faruwa a sansanoni da ke yankin Uighur.

    > A kowane lokaci yara su ne fatan ci gaban kasa. Ilimi shi ne zai taimaka ga cimma wannan fata.

  • Uyaiedu Ikpe-Etim

    Nijeriya Mai Shirya Fina-Finai

    Uyaiedu Ipke-Etim mai shirya fina-finai ce kuma darakta, 'yar gwagwarmayar LGBTQ da ta sadaukar da kanta ga kirkiro labaru a kan kungiyoyi al'umma da ake nuna wa wariya a Nigeriya.

    Fim dinta Ife da ke nufin "kauna" cikin harshen Yarbanci, labari ne na wasu 'yan Nijeriya 'yan madigo da ke nuna wahalu na rayuwa da sukan tsinci kansu a ciki a Nigeriya. Bayan sanar da fim din zai fito , fim din yayi fama da matsala ta tacewa a Nijeriya kasar da har yanzu ke matukar kyamar madigo.

    > Mata don Allah ku ci gaba da mamaye ko'ina kuma kada ku daina ba da labarun wadanda aka hana su magana.

  • Miho Imada

    Jafan Gwana Bangaren Yin Barasa

    Sana'ar yin barasa ta dade a hannun maza shekaru aru-aru, an haramta wa mata sa kafarsu a masana'antun yin barasa na kasar Jafan.

    Bayan mai yin barasa na gidansu yayi murabus Miho ta yanke shawarar samun horo da kuma zama daya daga cikin mata kalilan da ke sana'ar barasa a Jafan. A yanzu haka kamfanonin yin barasa wajen guda 20 da ke kasar mata ke gudanar dasu.

    > Idan har zaki iya samun aikin da zai fisshe ki kunya to tsunduma kanki ciki. Idan ki ka mutunta sana'ar da kika zabar wa kanki tsakaninki da Allah za ki kama hanyar cimma burinki.

  • Isaivani

    Indiya Mawakiya isaivaniisaiv

    Isaivani fitacciyar mawakiyar Gaana ce a Indiya. Kade kade na Gaana sun fito ne daga ma'aikata makwabta na Arewacin Cannai(Tsohuwar Madaras) a Tamil Nadu. Isaivani ta kwashe shekaru tana waka da rawa a wannan sararin duniya da maza suka kankame.

    A ce ki yi waka ki gwangwaje a dandamali daya da sauran fitattun maza mawaka za'a iya cewa nasara ce ta kashin kai. Isaivani ta yi nasarar kafa tarihi a wannan dadaddiyar al'ada da ta karfafawa sauran 'yan mata mawakan Gaana su fito fili domin bayyana kansu.

    > An samu canje-canje masu yawan gaske a duniya a 2020, amma ga mata duniyar na canzawa ne a kullum: mata sun canza fahimtar da kalubalantar damammaki. Wannan abu ne da zai ci gaba ga al'umomi da zasu biyo baya

  • Manasi Joshi

    Indiya Yar Wasar Motsa Jiki

    Manasi 'yar wasan motsa jiki na masu lalurar nakasa, a yanzu haka itace zakarar duniya a wannan fage. a watan Yuni na 2020 hukumar wasannin Badmitton ta duniya ta ayyanata a matsayin ta 2 a duniya a wasan mutum dai-dai. Har ila yau Manasi Injiniya ce kuma mai kawo canji.

    An yi na'am da burinta na canza irin kallon da ake yi wa mai lalurar nakasa da kuma wasanninsu a Indiya. A 'yan kwanakinnan ne mujallar Time Magazine ta ayyanata a matsayin jagorar zuri'a ta gaba har ta buga hotonta a shafin farko na mujallar ta Asiya a matsayin 'yar gwagwarmayar kare hakkin masu lalurar nakasa a Indiya

    > Wannan shekarar na tattare da kalubale ga mata a ta fannoni da dama. kada ki yarda wannan kalubale suyi nasara a kanki: ci gaba da laluben kowace dama. Ki dinga samun dama kina hutawa kullum

  • Nadine Kaadan

    Faransa Marubuciya

    Marubuciya 'yar kasar Siriya Nadine Kaadan na ta rubuce rubuce da zanen hotuna na labaru tun tana 'yar shekara 8 a duniya. Saboda rashin gamsuwa da matsayin wakilci da ta gani a littattafanta dake ci gaba, sai ta yanke shawarar rubuta labaru da kowane yaro zai iya ganin an wakilce shi a ciki.

    Karfin gwiwar da ta samu daga al'adun da ta gada da kuma burinta na yada dabi'ar karance-karance a duniyar larabawa, labarunta sun tabo darussa kamar na yara da ke da bukatu na musamman da kuma takaddama a gabas ta tsakiya.

    > Wa ya Allah takaddama ce ko cutar Kwaronabairos ce mata na cigaba da wanzar da zama lafiya da shugabanci. Duk da tsarin bai mana dadi gwagwarmayar gyara su na a hannun mata ta yadda za su ci gaba da cikakkiyar bayyana kansu.

  • Mulenga Kapwepwe

    Zambiya Mai Warkarwa kuma 'Yar Al'adu

    Mulenga Mpundu Kapwepwe na daya daga cikin wadanda suka kafa gidan tarihi na matan Zambiya da aka karfafa a shekarar 2020 saboda gudunmawar da mata ke badawa ga kasarsu, har ila yau ta gina wa yara da ke Lusaka Babban birnin Zambiya dakunan karatu.

    Ta shugabanci Hukumar Al'adu ta kasar Zambiya daga 2014 zuwa 2017 har ila yau ta kasance uwa ga kungiyoyi na raye-raye da rubuce-rubuce da kade-kade da al'adu.

    > Ki mayar da Canji a matsayin damarki.

  • Dr Jemimah Kariuki

    Kenya Likita

    Dafta Jemima Kariuki ta mike ka'in da na'in bangaren magunguna na rigakafi musamman lafiyar uwa da ta jaririnta, ita ta kafa kulob din zama lafiya da ta bullo da shi sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zabe 2007, da kuma kulob din kula da lafiyan al'umma wanda shine jigon gudanar da ayyukan rigakafi na sankarar mahaifa.

    A matsayinta ta dalibar aikin likitar mata, ta lura da raguwar mata da ke zuwa haihuwa asibiti da karuwar matsaloli na haihuwa a lokacin Kwaronabairos musamman a lokacin kulle. Da ta gane ana samun jinkiri na kaiwa ga ayyukan lafiya saboda rashin wadataccen sufuri sai ta bullo da tsarin ababen hawa masu lasisi da zasu dauki mace daga gida zuwa asibiti, wannan ya taimakawa ceton rayuka ta hanyar samun motar daukar marasa lafiya kyauta.

    > Kwaronabairos ta shafi kowa da kowa; ba ke kadai bace. Duk da haka wannan tunani da kike yawan yi a kullum ka iya zama dama a gareki; saboda haka kada ki tsorata wajen yin wani abu. Babu mamaki ke ce amsar bukatar wata.

  • Gülsüm Kav

    Turkiyya Yar Gwagwarmayar Adalci

    Gulsum Kav likita ce ta Turkiyya, ma'abociyar ilimi kuma daya daga cikin wadanda suka kirkiro kungiyar We Will Stop Femicide wato dakatar da kashe mata. A shekaru da suka gabata akwai karuwar kisan mata da 'yan majalisu ke ta muhawara a kai ta ko taron Istanbul gyara(tsari na doka da akayi domin kare wadanda ake cin zarafinsu a cikin gida) ya janyo suka ta ko ina a Turkiyya

    Gulsum ta yi aiki tukuru wajen wayar ma jama'a kai akan cin zarafin mata a Turkiyya da kuma gwagwarmaya a madadin iyalai da dama da suka rasa 'yan uwansu sakamakon kisan da ake yi wa mata.

    > Mata dake bijirewa a yau na bukatar daidaito da 'yanci. Cutar Kwarona wacce ta bayyana baro-baro rashin daidaito da mata ke fuskanta, ya nuna basu da wani zabi illa mikewa tsaye domin kawo canji.

  • Jackie Kay

    Ingila Marubuciyar Wakoki

    Jackie Kay marubuciyar wakoki da wasanni da zube ce 'yar Sikotlan, Rubutunta mai suna Red Dust Road da ya yi bayani filla-filla a kan neman mahaifanta, marubuciyar ta kwatanta shi a matsayin wasikar kauna ga iyayenta farar fata da suka rene ta. A shekarar 2016 aka rada mata sunan Scots Makar wato marubuciyar wakaki ta kasar Sikotlan

    Ita Uwa ce ga Jami'ar Sikotlan ta sama lambobin yabo masu dama saboda ayyukanta, kuma a 2020 aka sa ta zama CBE saboda ayyuka na adabi.

    > Kada mu taba gudu ko ja da baya. Zanga-Zangar da ake tayi a duniya a wannan shekara sun cika ni da bakuwar fata ga ci gabanmu.

  • Salsabila Khairunnisa

    Indonesiya Yar Gwagwarmayar Kare Muhalli jaga_rimba

    Salsabila daliba ce 'yar shekara 17 a duniya daga Jakarta Indonesiya a duk Juma'a sai ta jagoranci yaji a makaranta akan kwararowar hamada/sare itatuwa a gaban ofishin ma'aikatar muhalli da gandun daji.

    Da take 'yar shekara 15 tana daya daga cikin wanda suka bullo da kungiyar dalibai, Jaga Rimba. Da kuma kare daji, kungiyar da tayi gwagwarmayar kare hakkin al'umma 'yan kasa da ke asarar gidajensu a dajin Kinipan, daya daga cikin dazuzzukan ruwa da suka tsira a Kalimantan.

    > Cutar kwaronabairos ta sa mun hankalta da hada kai cewa dukkanmu muna karkashin tsari daya na jari hujja da burinsa shi ne samun riba. Lokaci yayi da zamu hada kai , da jagora shuke-shuke da farfado da lamura.

  • Mahira Khan

    Fakistan Yar wasa mahirahkhan

    Mahira Khan ba karabitin 'yar wasa ba ce, ta yi suna wajen yaki da cin zarafin mata ta lalata, wacce ta ki yarda da amfani da mai na canza launin fata/bilicin da kuma ba da goyon baya ga yaki da nuna wariyar launin fata. Tana son magance matsaloli na zamantakewa a al'umarta ta Fakistan ta hanyar amfani da fina-finai da kuma talabijin.

    Mahira jakadiya ce ta fatan alheri ta kasa ga babban kwamishinan al'amuran 'yan gudun hijira, na Majalisar Dinkin Duniya,inda take wayar da kai a kan halin da 'yan gudun hijira na Afganistan ke cikin a Fakistan. tana da farin jini wajen masu kallonta tun lokacin da ta soma fita a talabijin da bidiyo a 2006. Mahira har ila yau uwa ce da ta dukufa ga renon danta me shekara 11 a duniya.

    > Furta dalilai da batutuwa da ke da muhimmanci ga karfafa gwiwar kawo ci gaba.

  • Angelique Kidjo

    Benin Mawakiya

    Angélique Kidjo wacce so hudu tana sammu lambar yabo ta Grammy, tana daya daga cikin fitattun makada da maraya a duniya a yau. ta ratsa al'adu daban daban ya yammacin Afrika a lokacin da take yarinya a Benin da ke da birbishin kade-kaden R&B, da kidan Jazz da sauransu,da kuma tasiri daga Turai da Latin Amurka.

    Bayan ta bi lunguna da titunan Afrika a wakokinta na Talking Heads ta ci gaba da haskakawa, a yanzu haka mawakiyar 'yar kasar Benin da Faransa na binciken tushen Celia Cruz a Afirka wacce haifaffiyar kasa Cuba ce (Queen of Salsa). har ila yau Angelique na gwagwarmaya a madadin yara a matsayinta ta jakadar asusun UNICEF. Sanna ta hannun gidauniyarta ta tallafi mai suna Batonga da ke tallafawa ilimantar da yara mata a Afirka.

    > Ya kamata mu cigaba da kula da juna cikin hadin kai da kauna da karfafawa, bari mu ci gaba a matsayin masu kula da juna. Ya kamata wannan tafiya ta ratsa azuzuwa na zamantakewa da kabila da jinsi.

  • Chu Kim Duc

    Biyetinam Mai Ilimin Zayyana Gine-Gine kim_duc_

    Akitekt Kim Duc na kan wani buri ne na daukaka kare hakkin yara ya yin wasa ya Biyetinam. a matsayinta ta daya da ga cikin wanda suka kafa wuraren wasannin yara na Think Playground kuma Daraktar wannan waje, tana ta aiki da kungiyoyin kawance da al'umomi da ke kasar domin samar da wuraren wasa na yara guda 180 da aka samar dasu daga tsarin ma yar da bola jari.

    A yanzu haka tana nan tana aiki a kan wuraren wasan yara na yara masu lalurar nakasa na asibitin kasa na yara na Biyetinam a Hanoi, da kuma wajen wasan yara na farko mai saukin iskar sinadarin gawayi a birnin.

    > Kasance mai wasanni- a aiki da kuma rayuwa lamari ne na koyo daga karfafa gwiwa; me kike bukatar kiyi; mai kika fi jin dadin yi? Buri, da koyo ba kakkautawa su suke taimakawa magance wahalhalu da fata nagari.

  • Safaa Kumari

    Siriya Mai Nazarin Cututtuka Da Suka Shafi Tsiro/Shuka

    A matsayinta ta mai nazarin cututtuka na tsirrai Dafta Safaa Kumari tana ta laluben magungunan kwarin da ke kashe amfanin gona. Bayan ta gano iri na shuka da zai iya bunkasa samar da abinci a Siriya, ta yi kasadar ceto su daga Aleppo

    Ta kwashe shekaru tana gano ire-iren shuka da ke bijirewa kwari da ke addabar shuka, ciki harda wani wake da ke bijirewa cutar da ake kiraYellow Virus (FBNYV).

    > Duniya ta samu dumbin sauye-sauya a 2020. A cikin kungiyar da aka dora mata alhakin magance irin wannan matsaloli, lamari ne na kwazo - ba jinsi ba. Dole ne mata su yi imani da cewa gudunmawarsu daidai take da gudunmawar duk wani namiji.

  • Ishtar Lakhani

    Afirka ta Kudu Yar Gwagwarmayar Kare Hakki

    Ishtar 'yar gwagwarmaya ce, da tasa wa kanta sunan "Rigimammiya" tana zaune a Afirka ta Kudu ne inda ta hada karfi da kungiyoyin gwagwarmayar yin adalci da kuma sauran kungiyoyi da ke fadin duniya da ke samar da tallafin da suke bukata don karfafa yadda suke tunkarar kare hakkin bil'Adama.

    A wannan shekarar ta taka muhimmiyar rawa a gangamin bada maganin rigakafi kyauta, da goyon bayan cibiyar gwagwarmaya ta Artistic Activism da kuma bangaren muhimman magunguna na jami'o'i (UAEM). Ta na aiki da sauran kungiyoyi domin tabbatar da an samar da magungunan rigakafin cutar Kwaronabairos cikin rahusa ga kowa da kowa, da kuma kaiwa har inda mutum yake kyauta.

    > Wannan lokaci na jinkirta abubuwa har ila yau dama ce ga dukkanmu mu bunkasa ci gaba maimakon kokarin samar da tsari da bai taba yin daidai da farin cikinmu ba.

  • Claudia López

    Kolombiya Magajin Gari

    Claudia Lopez itace mace ta farko da ke rike da mukamin Magajin Garin Bagota babban birnin Kolombiya kuma birni mafi girma a kasar.

    Diya ga malamin makaranta ta taba yin sanata ta yankin Alianza Verde (A Jam'iyyar Green Alliance) daga 2014 zuwa 2018. ta jagoranci aiwatar da batun nan da ya yi farin jini na yaki da rashawa da ya samu kuri'a miliyan 11.6 (goyon bayan kashi 99 cikin 100) domin goyon bayan wannan kudiri kamar yadda yake a tarihin Kolombiya.

    > Zuwa ga matan duniya, ina fada muku; kada ku dakata. Gwagwarmayar juyin juya hali da aka soma a karni na baya ba za ta tsaya ba. Za muga canji baro-baro a tsawon rayuwarmu ta bainar jama'a da ta sirri.

  • Josina Machel

    Mozambik Yar Gwagwarmayar Kare Hakkin Bil'Adama JosinaZMachel

    Josina Z Machel ta dade tana kare hakkin mata, da aka haifa a gidan da ke da tarihin gwagwarmaya. Saboda haka ta kuke da sadaukar da rayuwarta wajen gwagwarmayar kare hakkin mata.

    Tana da Digiri na 2 daga makarantar tattalin arziki da kimiyyar siyasa ta Landan (LSE). Ta tsira daga cin zarafi na cikin gida sai ta mayar da wahalar da ta sha zuwa abu mai amfani ta hanyar wata kungiya da ta kafa. Kungiyar ta taimaka wajen gaggauta kawo canji na zamantakewa bagaren mata da kuma samar da kyakyawan rayuwa ga matan da aka ceto daga tashe-tashen hankula na al'umma a sassan kudancin Afirka.

    > Tasirin karin matsi ga mata abu ne da har yanzu ba ya lissafuwa, sai dai tsayin dakan da mukayi yasa muke da mafita ga iyaye da matan aure da 'yan uwa mata, jagorori da manyan shugabannin fannoni na bukatu na duniya.

  • Sanna Marin

    Finlan Firaministar Finlan

    Sannan Marin Firaminista ce ta kasar Finlan kuma jagorar jam'iyyar Social Decocratic Party ta Finlan. Gwamnatin hadaka da ta ke jagoranta hadaka ce ta jam;iyun siyasa 4 duka karkashin jagorancin mata: Maria Ohisalo ta jam'iyyar Green League, Li Andersson ta jam'iyyar Left Alliance, Anna-Maja Henriksson ta jam'iyyar Swedish People's Party da Annika Saarikko ta Center Party.

    A na yabawa kasar Finlan saboda yadda ta tafiyar da batun Kwaronabairos da a duk Turai ita ke da karancin wadanda suka harbu da cutar Kwaronabairos a kasashen Turai zuwa watan Nuwanba na 2020.

    > Mu jagororin mata ne da ke iya nuna cewa za a iya yakar cuta a kuma magance matsalar sauyin yanayi, zuba jari ga ilimi da kuma kawo sauye-sauye na adalci na ci gaban al'uma duk a lokaci guda.

  • Hayat Mirshad

    Labanon Yar Gwagwarmayar Kare Hakkin Dan Adam

    Yar gwagwarmayar kare hakkin mata, 'yar jarida kuma mai ayyukan jinkai, Hayat na daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Fe-Male wacce kungiya ce ta farko ta hadin kan mata a Labanon. Mara tsoro ballantana gudu ko ja da baya burin Hayat shi ne tabbatar da mata da 'yan mata sun kai ga yi musu adalci, bayanai, kariya da kuma kare hakkin bil'Adama.

    Ta ci gaba da yada manufofinta ta hanyoyi daban-daban ta hanyar shirya maci na kasa baki daya, da tattaro talakawa domin kalubalantar mulkin rashawa da bukatar sauyi.

    > Duk da kalubale da kuma koma baya da mata suka fuskanta a tarihi da kuma yaki da danniyar da maza ke yi wa mata, ta hanyar tafiya tare da 'yan uwantaka ta mata da kauna, za mu ci gaba da gwagwarmaya da kwarmata muryoyinmu da bukatar adalci da daidaiton jinsi.

  • Bulelwa Mkutukana

    Afirka ta Kudu Mawakiya/Marubuciyar waka zaharasa

    Bulelwa Mkutukuna da aka fi sani da Zahara idan ta hau dandamali. Ta taso ne natsattsiya a Afirka ta Kudu sai ta ga tana kaunar shiga wakokin kwaya a makaranta. ta soma sana'ar wake-wake ne a titi, sai dai a shekarar 2011 jerin wakokin Zahara suka karade ko ina cikin mako 3.

    Mawakiya/Marubuciyar waka

    > Addu'a ce ta sa na iya tsallake shinge mai wahala. Ba abinda ya fi karfin addu'a.

  • Lucy Monaghan

    Irelan ta Arewa Yar Gwagwarmaya

    Lucy Monaghan ta kawar da 'yancin ta na asan ko ita wace ce, ta yi magana akan yadda yan sanda da masu tuhuma a Arewacin Irelan suka mata bayan ta kai karar zargin an mata fyade a 2015. Da farko dai 'yan sanda suka fada mata cewa akwai shaidar ta na yawon banza da wanda take zargin ya mata fyade saboda haka a karshe ita za'a hukunta.

    Lucy ta kalubalenci hukumomi a kan kin gudanar da bincike, da yayi sanadiyyar yin sauye-sauye ga yadda ake tafiyar da lamarin wadanda akayi wa fyade. A yanzu Lucy na tallafawa wadanda aka yi wa fyade sanna a 2019 ta shiga wani nazari da aka sake yi na Mai Shari'a Gillen, da ya ba da shawarwari guda fiye da 250 don canza dokar.

    > Sunce bazan iya ba. Ga shi na yi. Haka ke ma zaki iya yi.

  • Douce Namwezi N'Ibamba

    Jumhuriyyar Dimukradiyyar Kwango Yar Jarida

    Douce Namwezi N'Ibamba yar jarida ce da ke amfani da kafofin yada labaru daban-daban na zamani kuma wacce ta kirkiro da wata kungiya ta Uwezo Afrika Initiative, wacce kungiya ce da ba ta neman riba ba da ke tallafa wa mata da sana'o'i ta hanyar aikin jarida da horon aiki da sauran al'amura na koyon sana'o'i.

    Ta yaki wasu munanan dabi'u a kan jinin al'ada ta hanyar ilmantarwa akan jima'i da samar da kayayyaki na kiwon lafiya ga dalibai da mata a Jumhuriyyar Dimukradiyyar Kwango.

    > Bari mu zama mu ne zuri'ar 'yan mata da mata da suka kawo canji da a kowane lokaci suke laluben hanyoyin magance matsalolinsu na yau da kullum wadanda ke fadin; ba wata matsala da ba ta da magani.

  • Vanessa Nakate

    Uganda Yar Gwagwarmayar Kare Muhalli/Yanayi

    Vanessa Nakate, yar shekara 23, 'yar gwagwarmayar kare muhalli/yanayi wacce ta fito daga Uganda kuma wacce ta kirkiro da kungiyar Rise Up Movement ta Afirka. Tana ta fadakarwa a kasashen duniya domin nuna illar canjin yanayi da ke aukuwa a Afirka. Ta maida hankali musamman akan yadda matsalolin yanayi ke daukaka talauci, da takaddama da rashin daidaito na jinsi

    A watan Janairu na 2020 jaridar Associated Press ta cire hoton Nakate da ke nuna Greta Thunberg da sauran mata masu gwagwarmaya na kasashen Turai, bayan sun halarci wani taro na tattalin arziki na duniya bayan nan Nakate ta yi magana a kan nuna wariyar launin fata a gwagwarmayar kare muhalli. Daga bisani Jaridar AP ta maida hoton Nakate. Da take nuna ba an yi ne da wata manufa ba, amma ba ta nemi gafara ba. a ranar 27 Janairu 2020 babban edita Sally Buzbee ya sa a dandalin twitarsa, ya na neman gafararta a madadin jaridar AP

    > Mata suka fi shan wahala daga kulle da kuma matsaloli na canjin yanayi amma har ila yau mu ne maganin: ilmantar da mata da karfafa su shi zai taimakawa matsalar da samar da shugabanni bangaren yanayi don ci gaba.

  • Dr Ethelreda Nakimuli-Mpungu

    Uganda Kwararriya Bangaren Lalurar Kwakwalwa

    Likita Ethel Nakimulu-Mpungu ta jami'ar Makerere da ke Uganda, ta na kokarin samar da magani da yafi karkata da gargajiya musamman ga wadanda ke dauke da cutar HIV damuwa.

    Ta samar da wani shiri mai sauki na magani da ma'aikatan lafiya za su iya aiki dashi har ila yau wannan shiri na rage alamomi na damuwa da yaki da cututtuka ga wadanda suka harbu.

    > Ki bada fifiko ga lafiyarki da sake karbe ikon ki.

  • Nandar

    Myanmar Yar Gwagwarmayar Kare Hakkin Mata

    Nandar 'yar gwagwarmaya ce ta kare hakkin mata, mai fassara, mai ba da labaru/tatsuniyoyi da ta kirkiro da dandalin intanet guda 2 na Podcast: Feminist Talks da G-Taw Zagar Wyne. Ita ta kirkiro kungiyar Purple Feminists ta mata, kuma take daya daga cikin wadanda suka ba da umurni a fim din The Vagina Monologues a Yangon da ya shafi al'aurar mata.

    Ta girma a kauye da ke Arewa maso Gabashin jihar Shan, Nandar ta sha wahalar da mata ke sha da suka kalubalanci wasu dabi'u na al'adu na iyali da al'uma a Myanmar. Yanzu ta na amfani da wannan dandali na ta wajen yakar miyagun dabi'u a kasar da suka shafi jinin al'ada da zubar da ciki.

    > Zan so in samu karin jama'a da zasu shiga wannan gwagwarmaya ta kawo karshen rashin daidaito domin mu iya rayuwa a duniyar da ake ganin darajarmu da mutunta mu a matsayinmu na 'yan Adam. Idan muka hada karfi zamu iya samar da duniya ta adalci.

  • Vernetta M Nay Moberly

    Amurka Yar Gwagwarmayar kare Muhalli/Yanayi

    Vernetta Moberly Matr aure ce, Uwa ce, Kaka ce kuma kawa.

    Ta kwashe shekaru tana tattara bayanai daga magabatanta, Sannan ta mika iliminta da kwarewarta zuwa ga zuri'a ta gaba na al'ummar Inupiat. Burinta shine gwagwarmaya domin ceton Duniya.

    > Iyaye Mata: ku kula da kanku. Ku cigaba da cin gajiyar ilimin magabatanku. Duka muna da alaka da juna. Muna da buri iri daya na taimakawa 'ya'yanmu su girma. Duk rintsi nemi mafita.

  • Nemonte Nenquimo

    Ikwado Jagorar Waorani nemonte.nenquimo

    Nemonte Nenquimo mace ce 'yar asalin Waorani da ta dukufa ga kare yankin magabatanta, da al'adunsu da hanyar rayuwansu a dajin ruwa na Amazon.

    Tana daya daga cikin wanda su ka kafa kungiyar kawance da ba ta neman riba ba ta Ceibo Alliance, mace ta farko shugabar kungiyar Waorani ta lardin Pastaza kuma daya daga cikin mata 100 da mujallar Time ta zabo da suka fi yin fice a duniya.

    > A matsayinmu na mata zamu iya samar da karfin da ake bukata domin samar da turba ta ci gaba a wannan lokaci da ake ciki mai hadari, da rayuwar wannan duniya tamu da bil'Adama ke cikin mawuyacin yali. a yanzu ne yakamata mata su hada kai.

  • Sania Nishtar

    Fakistan Jagorar Al'amuran Lafiya a Duniya

    Likita Sania Nishtar jagora ce ta al'amuran lafiya a duniya da dorewar ci gaba. Tun 2018, ta ke jagorantar wani shiri na kawar da fatara da ya kyautata rayuwar miliyoyin 'yan kasar Fakistan ta hanyar samar musu da bankin tafi-da-gidanka da kuma asusun ajiyar kudi da sauran abubuwa na taimaka musu.

    A mtsayinta ta mataimakiya ta musamman ga Firaministar Fakistan bangaren kawar da fatara da kariya ta walwala, Sania ta taimaka wajen karfafa talakawa ta hanyar daukar matakan da suka wajaba na farko domin bunkasa jin dadi a Fakistan.

    > Illar da cutar Kwaronabairos ta yi ta sa idon mu ya bude ga samar da duniyar adalci da kawar da fatara da rashin daidaito a yanayi na tabarbarewar yanayi. Saboda haka dole ne su ma mata su zama masu ruwa da tsaki da aka karfafa.

  • Phyllis Omido

    Kenya Yar Gwagwarmayar Kare Muhalli/Yanayi

    Phyllis Omido ita ce ta kafa sannan babbar darakta ta Cibiyar Shugabanci na Adalci da Fadi da cikawa bangaren muhalli, da ke gwagwarmayar kare hakkin muhalli da zamantakewa da tattalin arziki na al'umomin da abin ya shafa a Kenya. A 2015 ta sama lambar yabo ta muhalli ta Goldman Environmental Prize mai lakabin ("the Green Nobel"), da lambar da ta yaba wa nasarar da ta samu wajen rufe wata masana'anta ta dalma mai doyi a Owina Uhuru.

    A Yuni 2020 ta yi nasara a wata shari'a ta muhalli da kudin Kenya Biliyan 1.3 da aka bayar ga al'umar Owino Uhuru, da kuma karin wasu kudin Kenya Miliyan 700 ga CJGEA. Har ila yau kotun ta bada Umurnin a biya kudin daukar lauya na Phyllis. Hukummar gudanar da Muhalli ta Kasa ta daukaka kara a halin yanzu haka.

    > Kamar yadda mata da ke fadin duniya ya kamata su sake sunani a kan halaliyar sararin da ya kamata su kasance a ciki daga dukkan wata tursasawa, hakanan ma yanayi ke gwagwarmayar kwatar kai daga tabarbarewar muhalli. Mace ce kadai za ta iya kawar da wannan matsala.

  • Laleh Osmany

    Afghanistan Yar Gwagwarmayar kare Hakkin bil'Adama

    A Afaganistan yin amfani da sunan mata a al'amura na bainar jama'a abu ne da ba'a so. Sunan mahaifi ne kadai ake sawa a takardar shaidar haihuwa. Idan mace za ta yi aure ba a sanya sunanta a katin gayyata: idan ba ta da lafiya ba a sa sunanta a takardar da likita ke rubuta magani, idan kuma ta mutu ba a sa sunanta a takardar shaidar mutuwa ko da kuwa a jikin dutsen da ke kan kabarinta ne.

    Da ta gaji da wannan wariya da ake nuna wa mata sai 'yar gwagwarmaya Laleh Osmany ta soma wani gangami mai taken Ina Sunana Yake?. bayan gwagwarmaya ta shekara 3 a shekarar 2020 sai gwamnatin Afaganistan ta amince ta dinga sa sunan mata a katin shaida na dan kasa da takardun shaida na haihuwan 'ya'yansu.

    > Kowa yana da hakkin kokarin kyautata jindadi a duniya. Canji abu ne mai wuya sai dai abu ne mai yi wu wa. Za ka ga haka a tattare da matan da ke gwagwarmaya a duk wata kasa ta al'ada kamar Afaganistan.

  • Ridhima Pandey

    Indiya Yar Gwagwarmaya ta Kare Yanayi

    Ridhima Pandey 'yar gwagwarmaya ce ta kare yanayi wacce tana 'yar shekara 9 da haihuwa ta rubuta wani korafi da ke kalubalantar gwamnatin Indiya na kin daukar matakin magance matsalar muhalli. A 2019 Radhima tare da wasu su 15 masu kare hakkin mata su ka kai kasashe 5 kara a Majalisar Dinkin Duniya.

    A yanzu haka Ridhima ta na halartar wani taro na duniya da kuma taimaka wa karfafa sauran dalibai a dukkan matakai, domin gwagwarmayar kare al'kiblar su da kuma tsirrai daban-daban da ke duniya. Ridhima na aiki tukuru domin ceton gaba da kuma na zuri'a ta gaba.

    > Yanzu ne ya kamata mu hada kai da hada karfi wuri guda domin nuna cewa zamu iya jure lokuta na wahalhalu. Idan mace ta kuduri aniyar cimma wani abu babu wanda ya isa yayi mata birki.

  • Lorna Prendergast

    Australia Mai Bincike Bangaren Tabin Hankali

    A 2019, Loma Prendergast ta zama labari a kafofin yada labarai na duniya lokacin da ta gama karatu daga jami'ar Melbourne tana da shekara 90 a duniya, da kuma digiri na 2 a wannan shekaru na ta. Ta sadaukar da digirin nata ga mijinta da ya rasu, da suka shekara 64 suna tare a matsayin miji da mata, da kuma yayi fama da lalurar tabin hankali.

    A matsayinta ta mai bincike ta samar da kyakyawan fahimtar bukatun mai lalurar tabin hankali, da kyautata rayuwansu da dangantakarsu da masu kula da su.

    > Duk shekarun ka yaro ko tsoho zaka iya kawo canji a duniya .

  • Oksana Pushkina

    Rasha Mataimakiyar Jihar Duma

    Oksana Pushkina ita ce mataimakiyar mataimakiyar shugabar kwamiti na batutuwa da suka shafi iyali da mata da yara a jihar Duma ta Rasha.

    A 2018, da mata 'yan jarida daban-daban suka yi zargin Leonid Slutsky da nemansu da lalata, shugaban kwamitin kula da al'amuran kasashen waje na jihar Duma, Oksana shi ne kadai dan majalisa da ya fito a fili ya goyi bayan 'yan jaridan

    > Duniya ta yi matukar canzawa a 2020, sai dai banda wahalhalu da takaddama, abu daya da na koya shi ne sabbin kalubale a kowane lokaci kan zama alheri ga jama'a.

  • Cibele Racy

    Brazil Malamar Makaranta

    Cibile Hedimasta ce da ta yi ritaya da ta jagoranci koyarda daidaiton jinsi ga 'yan makarantar Firamari a Sao Paulo.

    Ta nazarci dukkan dabi'u na gudanar da makarantu don samar da yanayin da za'a tafi da dukkan malamai ba batun banbancin jinsi ko matsayi ko al'uma.

    > Wannan shekarar ta tilasta mana zama tamkar 'yan gudun hijira ta bangaren dukufar al'uma ga kawo canji. Ina fata mu hada karfi waje guda domin tunkarar kalubalen 2021.

  • Susana Raffalli

    Venezuela Mai Ilimin Abinci Mai Gina Jiki

    Susana ma'aikaciyar jinkai ce da ta kwashe shekara 22 ta na taimakawa ayyuka na gaggawa a fadin duniya. Ta taimakawa Caritas da Vanezuela samar da sinadari da ya nuna a zahiri illar matsaloli na jinkai a kan yara, a daidai lokacin da aka hana wannan rikici a Benezuwela. Har ila yau Susana ta kafa kwancen wasu cibiyoyi da ke samar da abinci masu gina jiki ga yara da ke geto/Matsugunai.

    A 2020 Susana ta yi aiki ga dorewar abinci ga 'yan kasa marasa galihu da mata masu HIV da yara da ke gidan yari a lokacin kullen Kwaronabairos. Ta yi aiki da kungiyar da ta jibaanci abinci masu gina jiki, har ila yau ta ba da shawarar a raba abinci mai gina jiki a sassan tsakiyar amurka a lokacin Kwaronabairos.

    > Soma kula da kanki, sannan ki soma gwagwarmayar samun 'yanci daga nan. Wannan ita ce tsira daga kulle.

  • Sapana Roka Magar

    Nepal Mai Aiki a Wajen Kona Gawa

    Bayan ta zama ba ta da gida na tsawon wata 3 Sapana ta yi tafiya zuwa Kathmandu inda ta shiga kungiyar da ke kona gawawwaki da babu masu su.

    Gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon Kwaronabairos sojojin Nepal ne ke tafiyar da su sau da kafa. Kungiyar Sapana kan tsintsince gawawwakin da aka watsi da su a titi ko wajen ajiye gawawwaki sannan su tsara yadda za a kai su asibiti domin gudanar da gwaje-gwaje a kansu. Idan har akayi kwana 35 babu wanda ya zo ya ce gawarsa ce, kungiyar za ta dauki gawar ta kai wajen konawa. wacce a al'adar Hindu dan mamacin ne yake gudanar da ita.

    > Akwai mutane da ba su da muhalli ko aka yi watsi da su a sassan duniya. Mutanen da suka mutu a titi sun cancanci a kula da gawarsu.Ina wannan aiki ne ba wai don aiki ne na walwala ba, sai don in samu kwanciyar nawa hankalin.

  • Pardis Sabeti

    Iran Kwararriya Bangaren Cututtuka

    Pardis Sabeti Farfesa ce a Jami'ar Havard da cibiyar Broad ta MIT da Harvard da kuma cibiyar lafiya ta Harvard Hughes. ta ba da gudunmawa ga ra'in bayanan bincike da suka shafi dan Adam da kananan kwayoyin halitta da ido baya iya gani, da kuma sanya ido a cututtuka da ke sauri yaduwa a yankunan karkara da kuma kokartawa bangaren ilimia Yammacin Afirka.

    A 2014 tana cikin ayarin likitoci da ke yaki da Ebola da mujallar Magazine ta sa wa suna Persons of the Year(Gwarazan Shekara), da har ila yau take cikin jerin mata 100 da sukafi yin tasiri, itace ta karbi bakuncin wasu bidiyo daban-daban na ilmantarwa mai suna Against All Odds (Duk Rintsi), ta kuma zama mai bada waka ana amsawa a kungiyar 'yan wasa Rock band Thousand Days.

    > Dukkan wani kalubale zamu jure shi, hada kai da wasa da dariya da sauran mutanen arziki a gwagwarmayar kyautata duniya shine jigon juriyarmu da nasarar mu.

  • Febfi Setyawati

    Indonesiya Yar Gwagwarmayar Kare Hakkin Bil'Adama Febfisetyawati

    Febfi Setyawati ce ta kafa Untukteman.id, wacce kungiya ce da ke taimakawa mutane da ke bukatar taimako - musamman mutanen da ke jinya kuma ba su da kudi da kuma wadanda cutar Kwaronabairos ta shafa. Ita da ayarinta suka zagaya al'umomi a cikin mota Bosawaja domin samar da intanet kyauta (da ka iya yin tsada) da dakin karatu na tafi da gidanka ga dalibai domin su ci gaba da ayyukansu. a yanzu haka ayarin na nan na kokarin samar da tiransimita mai sigina a yankunan da babu intanet

    Bakin cikin da ya sameta a lokacin da danta Akara Haykal ya rasu sakamakonwata cuta ta kwakwalwa da ba kasafai ake ganinta ba yasa Febhi taimakon saura.

    > Duniyar ta yi matukar sauyawa a 2020. Dole mu ma mu canza domin duniyar, gara mu dan yi abu mai amfani maimakon mu tsaya muna ta korafi.

  • Ruth Shady

    Peru Mai Ilimin Kayayyakin Tarihi Da Ke Boye A Karkashin Kasa

    Ruth Shady na da digiri na 3 bangaren nazarin kayayyakin tarihi da ke karkashin kasa da nazarin dan Adam, kuma ita ce mataimakiyar shugaban bincike ta Tsangayar Kimiyyar Zamantakewa ta Jami'ar kasa ta San Marcos. Ita ce darakta ta bincike a fannoni daban daban a wajen binciken kayan tarihi na Caral, da ake ganin wajen ne mafi dade wa na wayewar kan Amurkawa.

    Ta na da digirin girmamawa daga jami'o'i 5 na Peru sannan a 2018 ta lashe lambar yabo ta L'Oreal-Unesco ta mata bangaren kimiyya. Har ila yau an ba ta lambar yabo ta Jumhuriyyar Peru.

    > Ya kamata mata su shiga aikace-aikace da ke bukatar daukaka canji da gina al'uma da mutane za su zauna da juna lafiya daidai da albarkatu da Allah ya huwace musu.

  • Panusaya Sithijirawattanaku

    Thailand Daliba 'Yar Gwagwarmaya

    A zanga-zangar goyon bayan Dimukradiya ta wannan shekarar ta ratsa ta Tailan, sannan dalibai kamar su Panusaya 'yar shekara 22 su ne suka jagoranceta. Ita da sauran 'yan gwagwarmaya an kamasu saboda shigarsu cikin zanga-zangar amma daga bisani an ba da belinta.

    Bidiyon da ke nuna lokacin da aka kama ta, na nuna wasu jami'an 'yan sanda su 4 cikin farin kaya sun dauketa daga kasan wani daki da ke otel, su ka dora ta a kan kujerar guragu su ka gungurata zuwa motar 'yan sanda. Panusaya ta ce sam ba ta aikata laifuffukan da ake tuhumarta da su ba ciki harda haddasa hargitsi.

    A watan Agusta ta tsaya gaban cincirindon dalibai ta karanta manufofi guda goma da ke yin kira ga sarakuna su dena tsoma kansu cikin al'amuran siyasa. wannan yunkuri ne da ya ba da mamaki saboda Tailan na daya daga cikin 'yan dai-daikun kasashe da ke da dokar hukunta bata sunan gidan sarauta.Duk wani da ke sukar sarki ko sarauniya ko jinin sarauta ana iya masa daurin shekara 15 a gidan yari.

    > Kowa ma mai iya kawo canji a duniya ne. Ko ma me kayi ko kuma kai wanene ka zama mara tsoro ka sanya raywarka ta zama mai ma'ana.

  • Nasrin Sotoudeh

    Iran Yar Gwagwarmayar Kare Hakkin Bil'Adama

    Nasrin Sotoudeh lauya ce 'yar kasar Iran mai gwagwarmayar aiki da doka da kare hakkin 'yan siyasa da ke gidan yari, da 'yan adawa, mata da yara da ke Iran. ta na wani hutu na wucin gadi daga dogon hukunci na dauri saboda yakin da takeyi da tsarin rashin adalci da kowa ke suka.

    Duk da daure ta da akayi a gidan yari da yawan barazana da ake ta yiwa iyalinta Sotoudeh ta ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da aiki da doka.

    > Hijabi wajibi ne (a Iran) idan har za su tilasta mana sa rabin kyalle to za su iya yin komai da mu.

  • Kathy Sullivan

    Amurka Mai Ilimin Kimiyya/'Yar Sama Jannati

    Kathy Sullivan ta cika burinta na zama mai ilimin kimiyya 'yar sama jannati, marubuciya kuma babbar shugaba. Ta na daya daga cikin mata 8 na farko da suka bi sahun 'yan sama jannati na NASA a 1978, da ya sanya ta zama mace ta farko Ba'amirkiya da ta yi tafiya a sararin samaniya.

    Ita ce mace ta farko da ta yi ninkaya cikin teku zuwa waje mai zurfin gaske a cikin teku, sannan wannan kwarewa ta ta bangaren sararin samaniya da kuma cikin teku ya sa a ka sa mata sunan "most vertical person in the world".

    > Duniya ta samu dinbin sauye-sauye a 2020. Wannan ke tunatar da mu yadda duka rayuwa da ke duniya ke dogara da juna da ya tilasta mana sake nazarin gaskiyar abubuwan da muke bukata da darajantawa.

  • Rima Sultana Rimu

    Bangaladash Malamar Makaranta

    Rima Sultana Rimu wakiliya ce ta jagororin mata matasa masu zama lafiya a Cox's Bazar da ke Bangaladash. Wannan shiri, wani bangare ne na kawancen mata na duniya masu wanzar da zaman lafiya, da ke da manufar karfafa mata matasa daga kasashen da rikici ya shafa domin zama shuwagabanni da kuma jakadun zama lafiya.

    Rima ta agaza ga ;yan gudun hijirar Rohingya a al;ummarta ta hanyar kira ga mata su samar da ayyukan jin kai. ta shirya fadakar da mata, da ilimantar da masu shekaru da sauran jinsin jama'a ga 'yan gudun hijirar Rohingya, da kuma mata da yara 'yan mata da ke cikin al'umma da ba sa zuwa makaranta. har ila yau Rima ta yi amfani da gidajen rediyo da dandamali na wasanni domin wayar da kai a kan kudurorin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, da suka jibanci musamman da zaman lafiya da tsaro a al'umarta.

    > Na kuduri aniyar kawo daidaito na jinsi ga Bangaladash. Na yi imanin mata da 'yan mata na da karfin kwato mana 'yancinmu/hakkokinmu. Za muyi nasara.

  • Lea T

    Brazil Mai Talla leat

    Ba kowacce mace za ta ce ta fara wannan aiki cikin sa'a ba, amma ita Lea T haka ta kasance mata ga shi ta shekara fiye da goma tana wannan sana'a kuma ta mamaye shafukan manyan jaridu da mujallu harda Marie Claire da Grazia da Vogue.

    A 2016, Lea ta zama ita ce ta farko da ta samu shiga bikin bude gasar wasannin Olimpics. Lea ta zama jigo ta gwagwarmayar kare al'adu da take yaki da nuna wariya ga mutanen LGBT da kira ga al'uma ta magance wannan matsala. Iya tsawon wannan sana'a ta ta tana ta kokarin jan hankalin saura su yi koyi da ita don cimma burinsu na rayuwa.

    > Duniya na canzawa a kowane lokaci kuma muna motsawa ko wani lokaci sai dai mata ba za su iya tafiya su kadai ba.

  • Ana Tijoux

    Faransa Mawakiya

    Ana Tijoux 'yar adawa ce ta kade-kaden Hip-Hop na kasar Chile/Cile. wacce ke gwagwarmaya ta hanyar wakokinta ta na adawa da abubuwan da suka saba wa al'adu. Iyayenta sunyi gudun hijira a lokacin mulkin kama-karya na Augusto Pinochet a Chile, wanda ya bar alama a fitacciyar sana'a ga batutuwa na musamman ga siyasa da zamantakewa.

    Ta zafafa goyon bayanta ga kwato hakkin mata da adawa da cin zarafin mata a wakokinta na Vengo na 2014. Tijoux na yawan shiga gangamin yaki da nuna rashin daidaito da kuma danniya a duniya.

    2020 ta durkusar da tsarin tattalin arziki a cikin wannan yanayi muka samu karfin hada kawance. ya kamata mu dinga tuna haka a kowane lokaci saboda a nan ne karfinmu da kimarmu da martabarmu suke.

  • Opal Tometi

    Amurka Yar Gwagwarmayar Kare Hakkin Bil'Adama

    Opal Tometi mace ce da ta samu lambobin yabo a gwagwarmayar kare hakkin bil'Adama kuma daya daga cikin mata 3 da suka kirkiro da kungiyar Black Lives Matter (Rayuwar Bakar Fata na da Muhimmanci). Har ila yau itace ta kirkiro da wata sabuwar kafar yada labarai kuma jigo ta gwagwarmawa a duniya, Diaspora Rising.

    Iyalan Nijeriya da ke ci rani a Amurka suka haifeta, gwagwarmayar ta ta kare hakkin bil'Adama ta ratsa kasashen duniya tun kusan shekaru 20 baya.

    > Farkarwa ta gaskiya ta auku, a yanzu duka muna sane da cewa kawar da kai daga rashin adalci tamkar hada baki ne a aikata. Ina karfafawa kowa da kowa gwiwar yayi tsayin daka da dukufa da kuma kasancewa da Al'umarki.

  • Sviatlana Tsikhanouskaya

    Belarus Yar Siyasa

    Sviatlana Tsikhanouskaya tshohuwar 'yar takarar shugabancin kasa ce a Belarus, inda ta jagoranci wata kungiya ta gwagwarmayar Dikukradiyya. A Agusta 2020 shugaba Alexander Lukashenko ya ce shi ne ya lashe zaben, abinda ya yi sanadiyyar bore a sassa daban-daban na kasar da zargin an tabka magudin zabe.

    Jim kadan bayann zaben, saboda tsoron mai zai sameta da 'ya'yanta sai Sviatlana ta tsere daga Belaru zuwa Lithuania. ta cigaba da jagorantar gwagwarmayar dimukradiyya a inda ta ke gudun hijira.

    > Ka da ko na dakika daya ki amince da wanda zai ce miki kina da rauni. Sau da dama ba ma sanin karfin da muke da shi.

  • Yulia Tsvetkova

    Rasha Yar Gwagwarmaya

    An haifi Yulia Tsvetkova a wani dan karamin gari na masana'antu da ke gabas mai nisa ta Rasha inda ta je karatun fasaha da rawa da ba da umurni. daga bisani daga cibiyarta ta al'uma da dandamalin gwagwarmaya sai ta soma tayar da batutuwa da suke da dangantaka da hakkokin mata, hakkokin LGBT, da batun muhalli da kama karya irin ta soja.

    A 2019 a ka tuhume ta da yada hotunan tsiraici da kuma shari'a ta Prapagandar LGBTE. A yanzu haka tana fuskantar kwashe shekara 6 a gidan yari saboda ta sanya zanen jikin mace a intanet. Kungiyoyin kare hakkin bil'Adama na kasar rasha na daukarta a matsayin firsinar siyasa. ta ce sam ba ta aikata laifuffukan da ake tuhumarta da aikatawa ba.

    > Ka da ki taba yarda da cin zarafi ko daga gwamnati ko daga kawa ko al'uma. Kina da karfi da ikon kawo sauyi a duniya. komi nisan dare gari zai waye, ci gaba da gwagwarmaya.

  • Arussi Unda

    Mexico Yar Gwagwarmaya

    A lokacin da kisan mata ke ta karuwa a Mexico Arussi da ayarinta Brujas Del Mar ("Mayun Teku") su ka fito a matsayin muryar mata.

    A wannan shekarar sun janyo hankalin mata da ke sassar kasar domin yin yajin aiki na kasa baki daya a ranar 9 ga watan maris da ya sanya mata su ka dakatar da aiki da saura aikace-aikacensu, sukayi zamansu a gida.

    > A yanzu haka akwai take iri-iri kamar su "Juyin juya hali na mata" ko "Ci gaban mata" , - sai dai yanzu ne ya kamata mata su motsa. Dole mu jajirce mu ci gaba da yunkurawa.

  • Anastasia Volkova

    Yukiren Yar Kasuwa

    Dafta Anastasia Volkova 'yar kasuwa ce kuma manomiya da ta yi amfani da kimiyya da fasaha wajen tunkarar matsaloli da suka shafi karancin abinci.

    A 2016 ta kafa FluroSat, wanda kamfani ne da ke amfani da mutum-mutumi da data ta tauraron dan adam da sauran kayan aiki domin taimakawa manoma bunkasa amfanin gonakinsu.

    > Ki zama ke ce canjin da kike bukatar gani a duniya. Ina fata dukanmu za muyi amfani da tamu hanyar a wannan hali da ake ciki domin kawo canji.

  • Kotchakorn Voraakhom

    Tailan Mai Zayyane-zayyane na Shuke-Shuke kotch_voraakhom

    Kotchakom Voraakhom ta kwatanta kanta a matsayin badass mai gyara birane ta soma aiki ne da nufin gyara hanya da ta tsage ta Bankok daga nan sai kwakwalwarta ta bude a kan kawata waje.

    Yanzu haka ta dukufa ga gyara wuraren jama'a kuma tana gyara wuraren watayawa domin magance matsalar yanayi da muhalli ta hanyar shuke-shuke.

    > Ina amfanin manya-manyan gine-gine idan ilahirin birninmu na tabarbarewa?. Kafin mu ci gaba da gine-ginenmu muna bukatar mu duba matsalar sauyin yanayi, sai dai ba a matsayin al'uma daya tilo ko kasa tilo ko yanki tilo ba ya kamata mu hada kai duniya baki daya. Wannan duniya gidanmu ce kuma hanya daya ta warkar da ita ita ce muyi aiki a matsayin tsintsiya daya madaurinki guda.

  • Siouxsie Wiles

    Ingila Mai Ilimin Kimiyya

    Siouxsie mai ilimin kimiyya da kuma sadarwa bangaren lafiyar jama'a wacce ta yi fice a New Zealand a lokacin Kwaronabairos ta hada gwiwa da ma zane zane Toby Morris domin isar da sakon kimiyyar Kwaronabairos; aikin nasu su biyu ya hada da nuna yadda cutar ke illa da aka fassara zuwa harsuna daban-daban, kuma gwamnati ta yi amfani da shi don taimakawa jama'a su fahimci kullen da akayi.

    Har ila yau ta jagoranci wani dakin bincike na Biolumunescent Superbugs na Jami'ar Auckland, inda ita da ayarinta suka sanya wata kwayar cuta yin haske a cikin duhu domin fahimtar yadda kwayoyin cuta ke sa mu rashin lafiya da kuma gano sabbin magunguna.

    > Kasashen da mutane suka hada kai domin nasarar kare juna daga cutur Kwaronabairos na nuna mana komi girman matsala za a iya magance ta idan an hada karfi.

  • Elin Williams

    Wales, Ingila Mai Lalurar Nakasa Mai Tashe a Intanet

    Elin marubuciya ce mai lalurar nakasa da ke fadin irin wahalun da ta sha bangaren makanta a dandalinta na intanet mai suna My Blurred World(Makantacciyar Duniyata), tun tana 'yar shekara 16.

    Ta rubuta ainihin zahirin abinda ya sameta, ta bayyana komai kama daga shawara da tausayin halin da take ciki zuwa iyakancewa ta al'uma da ta fuskanta da muhimmancin daukaka saukin kaiwa ga masana'antar kwalliya. Tsawon lokaci tana saka zaren cimma burinta a fatanta na daukaka wayar da kai da kuma sanya sauran jama'a da ke cikin yanayi irin nata su san cewa ba fa su kadai ba ne.

    > Nemi wata damar da za ki iya bayyana fasahar ki da karfin ki da tunaninki da damuwarki da farin cikinki. Rungumi dukkan ci gaban da za ki iya samu. Kin cancanci dukkan wani abu da yake naki ne, ba tare da wani ya hanaki kaiwa ga gaci ba.

  • Alice Wong

    Amurka yar gwagwarmaya mai lalurar nakasa

    Alice ce ta kirkiro da wani gangami na karfafawa masu lalurar nakasa ba da labarunsu.

    A wannan shekarar ta wallafa sabon labari , Disability Visibility: wanda labari ne wanda mutum da kansa ke bayarwa daga karni na 21.

    > Duniyar ta yi matukar sauyawa a 2020, kuma ba na fatan abubuwa su koma daidai.

  • Dr Leo Yee-Sin

    Singafo Likita

    Likita Leo Yee-Sin ta na gudanar da babbar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa ta zamani, wacce ita ce ke tafiyar da al'amuran cututtuka masu yaduwa.

    Har ila yau ita ce kan gaba a yakin da kasar ta yi da cutar kwaronabairos ta kuma kwashe shekaru tana inganta kula da masu lalurar HIV a Singafo kuma ta jagoranci ayarin da suka yi nasara a kan cututtuka daban-daban masu yaduwa harda Sars. tana hada aikinta da aikinta na uwa mai 'ya'ya 3.

    > Cutar Kwaronabairos ta shafi rayuwar kowa da kowa. Sai dai bata sauya alkiblar jagorancin mace ba. Wadanda suka kasance kan gaba a yakar cutar yawanci mata ne kuma suna haka ne ba tare da wani tsoro ba.

  • Michelle Yeoh

    Malesiya Yar wasa michelleyeoh_official

    Michelle Yeoh ta soma yin wasanni ne inda ta yi wasan ta a "man's world" na fina finan fada na Honkon. Sai ta shiga fina-finan Amurka a matsayin yarinyar Bond (ta fito a fim Din Tomorrow Never Dies) tana daya daga cikin 'yan wasa kalilan da suka fito daga yankin Asiya da suka dade suna wasannin fina-finai a Amurka.

    Bayan ta kwashe fiye da shekara 30 ta na wannan sana'a Michelle na samun fita mai tsada a sabbin fina-finan Avatar da Kuma wani fim na farko da wani fitaccen dan wasa Shang-Chi yake jagoranta na Kamfanin Marvel. ta na yawan korafi a kan yadda ba'a samun wakilcin 'yan yankin Asiya a fina-finan Amurka kuma a matsayinta ta jakadar fatan alheri ta majalisar dinkin duniya ta na aiki tukuru domin kawar da fatara nan da shekarar 2030.

    > Cutar kwaronabairos ta shafi dukkanmu sai dai a kan mata yake karewa. Tuna ba mu kadai bane idan muna jin a killace muke, dole mu fito domin ba da goyon baya. Samun kungiyar kawance na goyon baya ta fi muhimmanci fiye da kowani lokaci.

  • Aisha Yesufu

    Nijeriya Yar Gwagwarmaya

    Aisha Yesufu 'yar gwagwarmayar tabbatar da shugabanci nagari a kasarta.

    Tana cikin wadanda ke gwagwarmayar Bring Back Our Girls (A dawo mana da 'yan matanmu) da aka kaddamar a 2014 biyo bayan sace 'yan mata su fiye da 200 daga wata makarantar sakandare a Chibok dake Nijeriya da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi. har ila yau jigo ce a Zanga-zangar EndSars, a zanga-zangar da aka ga 'yan Nigeriya a tituna suna neman kyautata aikin dan sanda, da somawa da rushe rundunar nan ta musamman ta yaki da 'yan fashi da makami (Sars) da ake zargi da kisa, fyade da yi wa farar hula fashi.

    > Shawara ta ga mata ita ce suyi cikakkiyar karbe matsayinsu a duniya ba tare da shayin kowa ba. ya kamata mata su daina tambayar gurbi a waje/wuri - ya kamata su kirkiro da nasu wajen.

  • Gulnaz Zhuzbaeva

    Krgyzstan Yar Gwagwarmaya Mai Lalurar Nakasa gulnazzhuzbaeva

    A Kyrgyztan, akwai mutane su fiye da 5000 da ke fama da lalurar makanta, sai dai basa iya kaiwa ga yawancin muhimman takardun gwamnati. Gulnaz Zhuzbaeva wacce ta kirkiro da Kyrgyz Tarayyar Masu lalurar makanta, na ta aiki tukuru don samar da wadannan takardu a tsarin keken rubutu na makafi.

    Ayarinta ke tafiyar da wani shiri na masu lalurar makanta domin koya musu kwarewar da ake bukata domin shiga kasuwar aiki. Daga cikin wadanda shekarunsu suka kai na balaga su 22 da suka kammala shirin a 2020, 6 a halin yanzu haka sunyi nasarar samun aiki kuma 2 daga cikinsu sun sami shiga jami'a

    > Rayuwa na cike da kalubale; dauke ta kawai a matsayinta ta yadda ta zo miki.