Mata Dari na BBC na Shekarar 2021

  • Lima Aafshid

    Afghanistan Mawakiyar baka

    Fitacciyar mawakiyar baka ce, kuma marubuciya wadda rubuce-rubucenta ke kalubalantar al'adar maza masu danne haƙƙin mata a Afghanistan.

    Bayan ta karanci aikin jarida, Lima Aafshid ta yi aiki jarida na zaman kanta sannan ta rika sharhi akan al'amuran yau da kullum na sama da shekara biyar.

    Mamba ce a Sher-e-dabeshgah da Kungiyar marubuta wakar baka ta Kabul Potry Association wanda ta rika shirya taro ta yanar gizo a lokacin annobar covid-19 domin rage wa mambobinta sama da 200 kadaicin zaman gida.

    *Faduwar Afghanistan kamar yana neman ya mayar da hannun agogo baya bayan mun sha fama da fita daga matsalolin da suka dabaibaye mu na kusan shekara 20. Amma ina da tunanin za mu sake fitowa da karfinmu domin kai wa ga gaci.

  • Halima Aden

    Kenya Mai ayyukan jin ƙai kuma tsohuwar mai tallan kayan ƙawa

    Mai tallan kayan ƙawa ta farko da ta fara sanya hijabi, Halima Aden ƴar asalin Somaliya ce amma an haife ta ne a sansanin ƴan gudun hijira a Kenya. A shekarar 2017 ne ta ƙulla yarjejeniya da daya daga cikin manyan kamfanonin tallan ƙawa na duniya, IMG Models, inda ta sanya sharaɗi kan kwantiragin nata cewa ba za a saka ta cire hijabi ba a yayin da take tallan kayan ƙawar.

    Ita ce mai tallan kayan ƙawa ta farko da aka wallafa hotonta a bangon mujallar British Vogue tana sanye da hijabi. Aden tana fafutuka don ƙara wayar da kai da kuma fito da matan Musulmai kuma ita ce jakadiyar Unicef kan haƙƙoƙin yara.

    A 2020, ta dina tallan kayan ƙwa saboda a ganinta bai dace da tsarin addininta na Musulunci ba, amma ta ci gaba da yin tasiri a ciki da ma wajen masana'antar kayan ƙawa ta duniya.

    *Mun ga ma'aikatanmu na jin ƙai sun ɗauki matakai masu tsauri don ganin ba abin da ya same mu a lokacin annobar cutar korona kuma ina fatan cewa mun yaba wa ƙoƙarinsu. Za mu iya dawo da duniya yadda take a da ta hanyar nuna godiya.

  • Oluyemi Adetibe-Orjia

    Najeriya Shugabar Gidauniyar Headfort

    Lauya ce, kuma wadda ta assasa Gidauniyar Headfort, wadda ta mata ce kawai da take bayar da taimakon kare marasa karfi a kotu ba tare da sun biya ba.

    Mazauniyar Legas ce, kuma su hudu ne suke ziyarar fursunoni domin taimakon marasa karfi da aka kulle ba bisa ka'aida ba, ko suka kasa samun beli, ko kuma wadanda aka kulle ba tare da an yi shari'a ba. (A Najeriya, wadanda aka kulle ba tare da an yi shara'a ba sun kai kusan kashi 70 na wadanda suke kulle a fursuna). Oluyemi Adetiba-Orija tana bi domin taimakon irin wadannan mutane su shaki iskar 'yanci.

    Daga lokacin da ta fara a shekarar 2018 zuwa yanzu, gidauniyar ta taimakawa sama da mutum 125 a kotu.

    *Idan muna so duniyar nan ta gyaru, dole sai kowa ya bayar da tasa gudunmuwar. Kowa ya yi magana, ya yi fafutika sannan ya bayar da gudunmuwa ga duk wani abu mai kyau domin tabbatar da 'yanci da lafiyar duniya.

  • Muqadasa Ahmadzai

    Afghanistan Mai fafutikar walwala da jin dadin jama'a

    Ta shirya wata kungiya ta matasan mata 400 daga yankin Nangarhar a Gabashin Afghanistan suka rika tafiye-tafiye zuwa garuruwa makwabta domin taimakon wadanda suka shiga rikice-rikicen gida.

    A matsayinta mai fafutikar neman alalar mutane, Muqadasa Ahmadzai ta kuduri aniyar tallafawa mata da garuruwansu musamman a lokacin annobar covid-19. Tsohuwar mamba ce a Majalisar Matasa ta Afghanistan, inda ta rika fafutkar kwato hakkin mata da kananan yara.

    A shekarar 2018, an ba ta karramawar N-Peace na Majalisar Dinkin Duniya da ake ba matan da ta yi zarra wajen samar da zaman lafiya.

    *Ban taba ganin irin wannan sauyin cikin kankanin lokaci ba kamar babu gwamnati baki daya. Yanzu burinmu shi ne matasanmu da za su maye gurbinmu wajen kawo gyara, amma wannan ba zai yiwu face da tallafin kasashen waje.

  • Rada Akbar

    Afghanistan Mai zayyana

    Danne hakkin mata yana cikin abin da ke damun wannan mai zayyanar. Rada Akbar ta dade tana amfani da zane-zanenta wajen bayyana ra'ayinta kan bukatar mata su fito a dama da su.

    Tun a 2019 take shirya taron 'Superswomen' duk shekara domin murnar ranar Mata ta Duniya a duk 8 ga Maris da kuma bayyana gudunmuwar da mata suka bayar a tarihin kasar. Kafin kwanan nan, ta fara kokarin bude wajen tarihin mata a Kabul da wani wajen.

    Tana da tunanin cewa zane-zanenta zai taimaka wajen kawo karshen dokokin da suke danne mata a siyasance da tattalin arziki da addinni.

    *Masu tsattsauran ra'ayi da shugabanni duniya sun i zarafin mutanen Afghanistan kuma an danne hakkinsu na gomman shekaru. Amma ba mu taba daina fafutika ba domin cigaban kasar nan, kuma muna sa ran za mu sake samun Afghanistan da za mu rayu cikin aminci da walwala.

  • Abia Akram

    Pakistan Shugabar masu lalurar naƙasa

    Abia Akram ta fara fafutuka kan ƴancin masu naƙasa tun 1997 saboda irin abubuwan da suka faru da ita, ta fara hakan ne a lokacin tana ɗaliba inda ta ƙirƙiri wani shiri Special Talent Exchange Program (STEP).

    Ita ce mace ta farko da aka zaɓa daga Pakistan a matsayin mai tsara shirin matasa masu naƙasa na ƙungiyar ƙasashe renon Ingila wato Commonwealth Young Disabled People's Forum. Akram ce ta ƙirƙiri ƙungiyar mata masu fama da naƙasa ta Women with Disablities kuma ta yi fafutuka kan ganin an aiwatar da taro kan ƴancin masu naƙasa na Majalisar Dinkin Duniya.

    Tana kuma aiki don ganin an sanya batun masu naƙasa a Shirin MDD na 2030 da kuma muradun ci gaba masu ɗorewa.

    *Domin mayar da duniya yadda take a da bayan annobar korona, dole mu haɗa ƙarfi wajen inganta dukkan ɓangarorin al'ummominmu inda za a samar da 'sabuwar rayuwar yadda za a zauna da cutar korona' kuma ya kamata mu ga ci gaban da zai haɗo da kowa da kowa a matsayin sakamako.

  • Leena Alam

    Afghanistan Jarumar fim

    Fitacciyar jarumai fim ce kuma mai rajin kare hakkin dan Adam da ta yi fice a harkokin kare hakkin mata da shirye-shiryenta a gidajen talabijin na Afghanistan kamar Shereen da Killin of Farkhunda wanda ke bayar da labarin wata 'yar Afghanistan da aka yi wa kazafin kona Qur'ani sannan aka kone ta a bainar jama'a.

    Alam ta bar Afghanistan a shekarun 1980s sannan yanzu tana zama ne a Amurka, amma tana cigaba da bayar da labarin kasarta.

    A shekarar 2009 aka nada ta Ambasadar tallafi na Majalisar Dinkin Duniya a Afhganistan.

    *Mun yi gomman shekaru muna gyara ta hanyar sadaukarwa da zubar da jinane. Ganin yadda muka koma gidan jiya cikin kankanin lokaci abin takaici ne, amma dole mu cigaba da fafutikar nan. Amma wannan karon da karin kwazo za mu fara.

  • Dokta Alema

    Afghanistan Mai fafutika kuma masaniyar fasahar tunani

    Fitacciyar malama ce a bangaren Philosophy and Social Science, kuma ta rike karamar Ministar kare hakkin dan Adam da kungiyoyi a Ma'aikatar Zaman Lafiya. Kuma ita ce ta kirkiri Kwamitin tabbatar da mata suna shiga siyasa ta Independent Women's Political Paricipation da kuma fitacciyar kungiyar Women's righ advocate.

    A matsayinta na mai digiri uku a bangaren tunani daga Jamus, Dokta Alema tana da kwarewar sama da shekara 20 a bangaren binciken yake-yake.

    Ta rubuta littafai game da alaka tsakanin Jamus da Afghanistan da tallafawa mata a Afghanistan, sannan kwararriyar mai bada horo ce kan ayyukan jin kai musamman ga 'yan gudun hijira.

    *Burina shi ne Afghanistan ta dawo mulkin dimokuradiyya, inda za a rika girmama hakkin dan Adam ta hanyar amfani da kundin tsarin mulki, inda kuma za a rika girmama hakkin mata a duk bangaren rayuwa.

  • Sevda Altunoluk

    Turkiyya Yar wasan kwallon jefa ka ruga

    An haife ta ne da matsalar gani, amma Sevda Altunoluk ba ta gajiya ba sai da ta zama fitacciyar 'yar wasan kwallo jefa ka ruga na makafi da ake kira goalball. (Wasan da kungiyoyi biyu na mutum uku masu matsalar gani ko kuma su rufe idanunsu za su rika jefa kwallo yana kara suna bin shi ta hanyar jin karar har a jefa a zare).

    Tana cikin fitattun 'yan kwallon goalball a duniya, ta samu karramawar 'yar wasa na wata a shekarar 2018 na kamitin Olympic na nakasassu, sanan ya lashe gasa biyu da gasar Turai sau hudu. Altunuluk ta taimakawa matan Turkiyya lashe gasar nakasassu a Olympic ta Riao 2016 da Tokyo 2020.

    An haife ta ne a Tokat, amma ta gama digirinta a physical education a Ankara.

    *Naƙasa bai kamata ta zama matsalar cimma burin rayuwa ba, kamata ya yi ta zama dama ta cika burin rayuwar.

  • Wahida Amiri

    Afghanistan Ma'aikaciyar dakin karatu kuma 'yan zanga-zanga

    Ma'aikaciyar dakin karatu kuma masoyiyar littafai, ahida Amiri 'yar zanga-zanga ce da ta karanci shara'a a jami'a. Lokacin da Taliban ta kwace Afghanistan, sai ya kasance ba ta iya aiki ba, sai ta shiga zanga-zanga a titunan Kabul-sannan daga baya mata da dama suka biyo ta inda suka yi zanga-zangar neman tallafin kasashen duniya ga matan Afghanistan domin su samu damar yin aiki da karatu.

    Tunda Taliban ta haramta zanga-zanga, sai Amiri ta hannu da sauran matan domin habaka karance-karance da tattaunawa.

    Dakin karatunta ya kasance yana aiki tun a shekarar 2017, sannan Amiri ta ce idan ba ta tare da littafanta, kamar ba ita ba ce take ji.

    *Duniyar nan ba ta girmama mu a matsayinmu na 'yan Adam. Amma a daidai lokacin da Afghanistan ke fuskantar rugujewa, sai muka dan dawo wa mutane da hankalinsu ta hanyar zanga-zanga da neman a yi adalci da nusar da mutane muhimmancin karatu.

  • Monica Araya

    Costa Rica Mai fafutuka kan harkar sufuri marar gurɓata muhalli

    A matsayinta na ƙwararriya kan yanayi da ke aiki don ganin an samar da harkar sufuri marar gurɓata muhalli, Monica Araya ta jagoranci kamfe-kamfe a Amurka da Turai har ma da ƙasarta inda ta ƙaddamar da kamfe mai taken 'Costa Rica Limpia', da ya taimaka wa ƙasar tata fito da matsayinta na jagorar sabunta makamashi.

    Araya ce mai ba da shawara ta musamman a kwamitin MDD da ke fafutukar tabbatar da gyare-gyare kan sauyin yanayi a ɓangaren sufuri, wani shiri na tabbatar da rage hayaƙi mai gurɓata muhalli kuma mamba ce a cibiyar ClimateWorks.

    An kalli wani shirinta na TEDTalks sau kusan miliyan huɗu, an kuma fassara shi zuwa yaruka 31. A 2016, Araya ta bi wani rangadi mafi girma na mata zalla zuwa Antarctica.

    *Lokaci ya yi na sauya abin da muke gani a matsayin daidai. Yana da muhimmanci mu rage buƙatunmu na man fetur da dizel, kuma zai taimaka wajen ƙarfafa tsarin siyasa ga al'ummomin da suka fi buƙatar sauye-sauye a al'ummominsu.

  • Natasha Asghar

    Ingila Mamba a Majalisar Wales

    Ta kafa tarihi a bana bayan da ta zamo mace ta farko mai launin fata daban da aka zaba a matsayin 'yar majalisa a kasar Wales tun kafata a shekarar 1999.

    Mamba ce a Jam'iyyar Conservative kuma mamba a majalisar sashe na Kudancin Wales, Natasha Asghar ministar wucin gadi ce ta tafiye-tafiya da fasaha. Tana da burin kafa kamfanin sufuru domin jawo hankalin mutane su rika amfani da sufurun haya da kuma taimakawa ajen habaka tattalin arzikin Wales.

    Kafin ta shiga siyasa, ta aiki a banki da aikin jarida sannan ta rubuta littafai gguda biyu.

    *Idan muka hada kanmu. Za mu iya wuce komai duk wuyarsa har mu kai ga tudun mun tsira sannan mu samu damarmaki masu yawan gaske da za mu rayu da su kuma mu yi aiki da su.

  • Zuhal Atmar

    Afghanistan Yar kasuwa, masana'ntar sabunta kayayyaki a Gul-e-Mursal

    Gul-e-Mursal ce masana'antar sana'anta da takardun da aka yi amfani da su ta farko, wanda 'yar kasuwa Zuhal Atmar ta assasa. Kasancewar tana da masaniya a kasuwanci, sai ta bude kamfanin wanda na mata ne zalla a Kabul a shekarar 2016, inda ta samar da aiki ga mutum 100, inda kashi 30 ya kasance ga mata daga cikin kamfanin zuwa kasuwancinsa.

    Kamfanin na aikin tattara datti da takardu, sannan ta sana'anta su, inda suke samar da kusan tan 35 na takardu a duk mako, sannan ta hada takardar shiga bandaki da ake sayarwa a cikin kasar.

    Atmar tana bayyana ra'ayinta akan wahalar da mata suke ciki na neman tallafin kudade da suke bukata domin fara kasuwanci a Afghanistan.

    *Wace alama muka gani nan gaba za a shiga? buruka da tsare-tsaren matasanmu duk an wargaza su.

  • Marcelina Bautista

    Mexico Shugabar Kungiya

    Marcelina Bautista ta taba yin aikace-aikacen gida a gidan wasu, amma yanzu darakta ce a Cibiyar Tallafawa da Horar da Masu Aikace-aikacen Gidaje wato Mexico's support and training center for domestic orkers (CACEH), cibiyar da ta kirkira shekara 21 da suka gabata. Tana fafutikar kwato hakkin masu aikace-aikacen gidaje ne kamar su alawus dinsu da hutun rashin lafiya da sauransu kamar yadda sauran ma'aikata suke cin moriya.

    Shirinta ya hada da ilimantar da masu aikace-aikace da masu daukarsu aikin da mutanen gari. Bautista ta kasance a cikin na gaba-gaba wajen muhawarar da sa gwamnatin Mexico ta shiga yarjejeniyar duniya ta ma'aikata da ta bukaci a kula da hakkin masu aikace-aikacen gida domin kada a ci zarafinsu da kuma danne musu hakki.

    Ta taba lashe karramawar kare hakkin dan Adam na duniya na Friedrich-Ebert-Stiftung na Jamus a shekarar 2010

    *Canja duniya na nufin canja tsarin aikin miliyoyin masu aikace-aikacen gida, wadanda yawancinsu mata ne da suke a gidajen wasu, alhali wasu mutanen na can suna aiki domin cigaban kansu. Wannan bambancin rayuwar zai zo karshe ne idan masu aikace-aikacen gida suka samu lura yadda ya dace.

  • Crystal Bayat

    Afghanistan Mai fafutikar hakkin dan Adam

    Mai fafutikar hakkin dan Adam, Crystal Bayat ta yi fice bayan zanga-zangar da ta jagoranta na nuna kin karbar mulkin Taliban na shekarar 2021.

    Tana cikin mata bakwai da suka yi zanga-zanga a Kabul na 19 ga Agustan, wanda shi ne ranar 'Yancin Kan Afghanistan. Bayan ta fara karatun digiri na uku a wannan shekarar, amma aka samu tsaiko bayan Taliban ta ƙwace kasar.

    Yanzu haka tana zaune ne a Amurka, inda daga can take cigaba da fafutikar tabbatar da kare hakkin dan Adam a Afghanistan. Tana kuma burin ganin ta kammala digirinta uku, sannan ta rubuta littafi.

    *Lallai ina da burin shiga duk wani kokari da zai kawo dimokuradiyya mai inganci a Afghanistan. Burina shi ne in yi magana a taron Majalisar Dinkin Duniya domin ina da tunanin ya kamata duniya ta ji asalin halin da mutanen Afghanistan, musamman ma mata suke ciki.

  • Razia Barakzai

    Afghanistan Mai zanga-zanga

    Bayan aikin da ta yi a Fadar Shugaban Kasa na wasu shekaru, Razia Brakzai ta kasnace ba tare da aiki ba tun bayan da Taliban suka kwace mulki.

    Tun lokacin take shiga harkokin zanga-zanga a birnin Kabul inda mata da dama suka zuwa domin nuna rashin amincewarsu kan hana su zuwa aiki da neman ilimi. Tana cikin matan da suka fara amfani da #AfghanWomenExist, wanda ke nuna cewa matan Afghanistan suna nan sannan yake nuna da cewa tsoro na tursasa matan Afghanistan barin amfani da kafofin sadarwa.

    Barakzai ta yi digiri a shari'a da Kimiyyar Siyasa, kuma ta yi digiri na biyu a MBA. A wata wasika da ta rubuta zuwa ga BBC a game da abubun da ta fuskanta, ta ce, "mutuwa a wajen neman 'yanci ya fi zama cikin bauta."

    *Matasa da masu ilimin kasar nan-musamman masu karfin zuciya a cikinsu da mata sadaukai na Afghanistan-watarana su za su daga tutar 'yanci. Ina ganin alamar hakan kullum a wajajen zanga-zanga a titunan.

  • Nilofar Bayat

    Afghanistan Yar wasan kwandon guragu

    Ita ce kyaftin ta tawagar kwallon kwandon Afghanistan, kuma fitacciyar mai fafutikar kare hakkin mata nakasassu. Nilofar Bayat ta bar Afghanista bayan Taliban sun kwace kasar tare da mijinta wanda shi ma gurgun dan wasa ne da suke aiki tare da kungiyar International Red Cross.

    Tana da shekara biyu ne aka jefa musu nakiya a gidansu, inda dan uwanta ya rasu, ita kuma ta samu rauni a kashin bayanta. Bayat ta buga wasanta na farko na kwallon kwando a tsakiyar birnin Kabu, wanda ya kasance kamar bude ido ga sauran mata 'yan wasa. Ta zama muryar masu gudun hijira da suke barin garuruwansu sannan ta kafa kungiyar Matan Afghanistan.

    Bayat na da burin ta cigaba da buga kwallon kwando nan gaba.

    *Ina fata an gama wasan ke nan a Afghanistan, kuma ba za mu sake shiga yaki ba ko da na dakika daya. Ina fata zan ga murmushi na gaskiya a fuskar mutanena.

  • Jos Boys

    Birtaniya Mai zanen gine-gine

    Ita ce mataimakiyar darakta ta shirin The DisOrdinary Architecture, wanda zai haɗo dukkan masu zane-zane da ke da lalurar naƙasa don ƙirƙirar tsarin yadda za a shigar da kowa harkar gine-ginenmu.

    Jos Boys tana haɗa aikinta na zanen gine-gine da fafutuka, kuma ita ce ta ƙirƙirishirin Matrix Feminsit Design Collective a shekarun 1980 kuma tana ɗaya daga cikin mawallafan littafin Making Space: Women and the Man Made Environment. Ta yi aiki a matsayin malama a makarantun ƙasashen duniya da dama, inda take bayyana ra'ayinta na fafutukar kare ƴancin mata a fannin zanen gine-gine a ƙoƙarinta na magance matsalar da ta dabaibaye hakan.

    A tsawon shekara 40 da ta yi na aikinta, ta yi ta wayar da kai kan yadda za a iya amfani da zamantakewar yau da kullum don taimaka wa mutane masu lalurar naƙasa.

    *A shekara ɗayan da ta gabata, muna buƙatar sanya iliminmu na al'ummomi daban-daban kan mutane masu naƙasa da sauran mutane da ake nuna wa wariya: mu fahimci wannan a matsayin wata basira ta dawo da gine-ginen yankunanmu wuraren nuna kulawa da dogaro.

  • Catherina Corless

    Ireland Masaniyar tarihi

    Matashiyar mai binciken tarihin ce da ta bandako mutuwar kananan yara 796 a gidan rainon Bon Secours Mother and Baby Home Galway, inda ta dauki shakeru tana binciken wanda har ta kai ga gano babban ramin da aka binne yaran a kusa da tsohuwar Cibiyar Iyaye Mata Marasa Aure na Ireland inda daruruwan jarirai suka bace a tsakanin shekarun 1920s zua 1950s.

    A bana, rahoton binciken nan wanda aka dade ana tsimayi, wanda yawanci masu yi wa coci hidima ne suka gudanar, ya bankado mutuwar jarirai sanadiyyar cututtuka da dama, wanda ya sa dole Gwamnatin Ireland ta fito ta nemi afuwa.

    Corless ta karba kambun kare hakkin dan Adam na Kungiyar Lauyoyin Ireland duba da aikinta da cigaban al'umma.

    *Idan har akwai yadda zan yi in gyara duniya, zan hana amfani da kalmar 'kunya". Kamus ya ce kunya ita ce jin tsoron tozarci, wannan kalma ce mai haruffa biyar da ke da matukar karfi.

  • Faiza Darkhani

    Afghanistan Masaniyar tsabtace muhalli

    Daya daga cikin mutane kadan da suke aikin tsabtace muhalli, Faiza Darkhani Matimakiyar Farfesa ce kuma tsohuwar darakta a hukumar tsabtacem muhalli ta National Environmental Protection Agency da ke yankin Badakhshan. Kuma ta yi fice wajen bayyana ra'ayinta kan kare hakkin mata.

    Darkhani ta yi digiri na biyu ne a Jami'ar Putra da ke Malaysia, inda ta karanci zane-zanen gidaje. Ta wallafa bincike-bincike da dama kan kan tsarin birane da fasahar kirkira kamar su fasahar tsabtace abinci da samar da shi a biranen kasar.

    Tana da yakinin wayar da kan mutane akan tsabtace muhalli da kuma gudanar da shirye-shiryen cigaban al'umma da suka jibinci mata.

    *Nuna kai a bainar jama'a babban mataki ne da ke bukatar karfin rai. Dole ne mutum ya bi muradun ransa tare da tabbatar da cim musu, ni kuma burina shi ne a samu tsabtataccen muhalli da babu yaki a ciki kuma babu gurbacewar muhalli.

  • Azmina Dhrodia

    Canada Mai jagorantar tsare-tsaren kariya

    Ja gaba kuma ƙwararriya a kan batun jinsi, fasaha da haƙƙin ɗan adam, Azmina Dhrodia a yanzu ita ce mai jagorantar tsare-tsaren kariya na wata manhaja ta soyayya mai suna Bumble. Ta shirya wata buɗaɗɗiyar wasiƙa a Yulin 2021, wacce mata masu faɗa a ji fiye da 200 suka sanya wa hannu, da suke kira da ɗauki ƙwararan matakai don magance cin zarafi a shafukan sada zumunta.

    Sannan ita ce mawallafiyar littafin Toxic Twitter: Violence and Abuse Against Women Online, wani rahoto kan yadda ake cin zarafin mutane da kuma wani ɓangare nasa da ya yi maganar matsayi da ƙabila.

    Dhrodia a baya ta yi aiki a matsayin mai tattara bayanai kan ƴancin jinsi, sannan ta yi aiki da kamfanonin fasaha da dama don samar da kariya ga mata da al'ummomin da ake nuna wa wariya.

    *Ina son duniyar da mata za su iya amfani da intanet cikin daidaito ba tare da tsoro ko tsangawama ba.

  • Pashtana Durrani

    Afghanistan Malama -Cibiyar Learn Afghanistan

    Pashtana Durrani, ita ce ta kirkiri LEARN, kuma ita ce Babbar Darakta. Malama ce da ta sadaukar da lokacinta wajen kirkira hanyoyin samar da ilimi da 'ya'ya mata da hakkinsu. LEARN ta bude makaranta a Kandahar, sannan ta horar da malamai da dalibai.

    Ta hanyar amfani da Manhajar Rumie (wanda ke wanda ke amfani da shi a wayar salula na farko damar amfani da minti 6 wajen koyon) kungiyar ta saukakawa mata samun ilimi da bidiyoyi da wasannin ilimi. Sun kuma horar da mata a kauyuka hanyoyin karbar haihuwa.

    Durrani wakiliyar matasa ce a Majalisar Dinkin Duniya, kuma ta karbi kambun Malala Fund Education Champion Award domin ayyukanta na taimakon yara mata na Afghanistan su samu ilimi.

    *Akwai mamaki yadda duniyar take neman cire mu daga asalinmu. Amma komai wuya da tsoro da raunukan da za mu ji, za mu hakura-kuma komai nisar hanyar.

  • Najla Elmangoush

    Birtaniya Ministar Harkokin Wajen Libya

    Mace ta farko da aka nada Ministar Harkokin Wajen Libya a bana. Masaniyar harkokin diflomasiyya ce kuma lauya. A lokacin juyin juya halin Libya na shekarar 2011, Najla Elmangoush tana cikin National Transitional Council kuma ta yi aiki domin samar da hadaka tsakanin kungiyoyi.

    Ita ce wakiliyar Libya a Makarantar Zaman Lafiya ta Amurka kuma ta yi aikin shirye-shiryen samar da zaman lafiya a Cibiyar World Religion, Diplomacy and Conflict Resolution. Rikicin siyasar kasar ya sa dole Elmangoush ta yi murabus, sannan kwanan nan aka hana ta tafiye-tafiye.

    Tana da digiri a shari'a daga Jami'ar Benghazi kuma ta yi digirin-digirgir a Jami'ar George Mason.

    *Duniya ta ga sauye-sauye a shekarar 2021. Zan so duniyar ta dawo farko, domin ta zo da ma'ana ga rayukanmu sannan kuma ta fi amfanar da al'umma.

  • Shila Ensandost

    Afghanistan Malama

    Wayar da kan mata da 'yan mata shi ne babban aikin da malama Shila Ensandost ta sanya a gaba. Ta yi digiri a addini, kuma ta koyar a makarantu.

    Ta kasance gaba-gaba wajen daga gudunmuwar mata a siyasa da sauran sha'anin al'umma, sannan ta fito a kafafen yada labarai na Afghanistan da dama tana magana akan hakkin mata na neman limi da aiki. Kwanan nan Ensandost ta shiga zanga-zangar da aka gudanar a Kabul inda ta sanya likafani a wajen zanga-zangar domin kalubalantar danne hakki mata da ake yi a kasar.

    Ta kasance a cikin kungiyoyi da dama na matan Afghanistan kuma tana koyarwa

    *Ina son ganin mata sun shiga siyasa da sauran al'amuran yau da kullum, sannan a tabbatar da hakkin mata sannan a yi watsi da nuna bambanci ga mata.

  • Saeeda Etebari

    Afghanistan Mai zanen kayan kwalliya

    Kayan kwalliyar da ta hana sun shiga kasuwar Smithsonian na Washington DC, kuma tana amfani da yanayin al'adar kasarta Afghanistan ne tare da amfani da abubuwan da ake samar wa a kasar wajen hada kayayyakin kwalliyar.

    Saeed Etebari 'yar kasuwa ce, kuma fitacciyar mai hada kayan kwalliya a duniya.

    Ta zama kurma tana da shekara daya bayan ta kamu da cutar bakon dauro a sansanin gudun hijira, sannan ta yi karatu a makarantar korame wanda mahaifinta ya dauki nauyi. Daga nan sai Etebari ta shiga makarantar koyon zane ta Turqoise Mountain Institues for Art and Architecture, inda ta kware a hada kayan kwalliya.

    *Yanzu mata ba su da aikin yi, sannan maza ne kawai za su iya yin aiki. Yanzu an samu sauyin mulki, burina na ganin an samu Afghanistan mai kyau yanzu ya zama kawalwalniya.

  • Sahar Fetrat

    Afghanistan Mai fafutikar kare hakkin mata

    Sahar Fetrat matashiyar 'yar gwagwarmaya ce da kasance kan gaba wajen zanga-zanga da dama da aka shirya domin kalubalantar nuna wariya ga mata. Ta kasance 'yar gudun hijira tana karama a Iran da Pakistan lokacin mulkin Taliban na farko. Ta dawo Kabul ne a shekarar 2006, inda ta cigaba da gwagwarmayar kare hakkin mata tana karama.

    Ta sanya manufofin kare hakkin mata ta hanyar amfani da rubuce-rubucenta da fina-finanta. Misali a fim dinta na yadda ake cin zarafin mata a tituna mai suna Do Not Trust My Silence na shekara 2013. Fetrat ta yi aiki da sashen ilimi na UNESCO a Afghanistan da kuma Human Right Watch.

    Ta yi digirinta na biyu a Jami'ar Central European Univeristy inda ta karanci Critical Gender Studies, kuma a yanzu haka tana karatu a a sashen nazarin yake-yake na King's College da ke Landan.

    *Ina fatan zan ga ranar da za a ba ilimin 'ya'ya mata a matsayin abin da suka cancanta, ba wai abin da za a rika fafutika a kai ba. Ina fatar ganin lokacin da matan Afghanistan za su rika fafutikar cimma burinsu manya da suka girman tsaunuka.

  • Melinda French Gates

    Amurka Mai taimakon al'umma kuma 'yar kasuwa

    Mai taimakon al'umma kuma 'yar kasuwanci kuma mai rajin kare hakkin mata da kananan 'yan mata na duniya. Melinda French Gate ce ta jagoranci assasa babbar gidauniyar taimakon al'umma a matsayinta na daya daga cikin ciyamomin Gidauniyar Bill & Melinda Gate.

    Ita ce kuma ta kirkiri Pivotal Ventures, kamfanin da yake aiki domin walwalar mata da iyalai, sannan ta rubuta littafin The Moment of Lift.

    French Gates tana da digiri a kwamfuta sannan ta yi digiri a MBA a Jami'at Duke. Ta yi shekaru tana hada abubuwanda za a iya gani a kamfanin Microsoft kafin ta bar kamfanin ta mayar da hankali kan iyalanta da ayyukan jin kanta.

    *Annobar covid-19 din ta kara fito da yadda ake ware wasu mutane fili. Sanya mata da 'yan mata a kokarinmu na dawowa kamar yadda ake a da zai taimaka wajen rage radadin wahalar da ake ciki a yanzu, sannan ya assasa tubali mai kyau na gobe.

  • Fatima Gailani

    Afghanistan Mai shiga tsakani

    Tana cikin masu shiga tsakani guda hudu da suka zauna da Taliban a shekarar 2020 domin samar da maslahar siyasa a kasar. Fatima Gailani fitacciyar 'yar siyasa ce kuma mai fafutika da ta kwashe sama da shekara 43 tana ayyukan jin kai.

    Tana cikin fuskokin matan Afghanistan da suke kalubalanci mamayar Gwamnatin Siviet na shekarun 1980s, kuma ita ce kakakin mayakan Afghanistan daga inda ta samu mafakar siyasa a Landan. Ta dawo Afghanistan ne bayan Amurka da kwace kasar a 2001, inda ta kasance cikin wadanda suka rubuta sabon kundin mulkin kasar.

    Daga shekarar 2005 zuwa 2016, ita ce Shugabar Afghanistan Red Crescent Society, kuma har yanzu tana cikin daraktocinta.

    *Ina fata za a zauna a yi tattaunawar gaskiya da za ta haifar da gina kasa mai inganci.

  • Carolina Garcia

    Ajantina Darakta - Netflix

    An haifi Carolina Garcia wadda daraktar fina-finai masu dogon zango ce a manhajar Netflix a Ajantina, amma a California ta girma. Mawaƙiyar, kuma mai rawa ta fara da neman sanin makamar aiki a kamfanin Twentieth Century Fox kafin daga bisani ta shiga masana'antar.

    A matsayinta na babban jami'ar ɓangaren ƙirƙira, ta jagoranci shirya kƙyatattun fina-finai masu dogon zango a manhajar ta Netflix irinsu Stranger Things, da The Chilling Adventures of Sabrina da 13 Reasons Why da Atypical da Raising Dion.

    Kasancewarta ɗaya cikin tsirarun 'yan yankin Arewacin Amurka da suke da manyan muƙamai a masana'antar Hollywood, Garcia ta taimaka wajen jawo ƙarin mutanen yankinta tare da bayar da labarin yankin domin a yanzu haka, mutanen yankin sun kusa ɗaya bisa biyar na mutanen Amurka.

    *Shekarun da suka gabata sun matukar girgiza mu duka, amma ita kanta rayuwar 'yar kalilan ce-me zai sa mu karar da dan kankanin lokacinmu cikin fargaba? kamar yadda kakata take cewa, "dole rayuwa a yi ta yadda take" kuma lallai yanzu lokaci ne da ya kamata mu saurari shawarar kakata.

  • Saghi Ghahraman

    Iran Mawakiyar baka

    Yar asalin Iran ce mazauniyar kasar Canada, kuma marubuciya ce sannan ita ce ta kirkira kuma take shugabantar Iranian Queer Organization (IRQO)

    A yanzu tana zaune ne a Toronto, inda kungiyarta ke aiki domin kare hakkin 'yan luwadi da madigo da masu canja jinsi da suke zaune a Iran ko kuma aka tursasa su yin hijira tare da bibiyan take hakkin 'yan luwadi da ake yi a Iran.

    Ghahraman ta kirkira Gilgamishaan Books a shekarar 2010 da yake mayar da hankali kan littafan "'yan madigo da luwadi" na Iran. Babbar edita ca a duniya da ta rubuta wakokin baka a littafi mai mujalladi hhudu da mukaloli da dama. Ayyukan Ghahraman sun yi fice wajen kalubalantar masu ganin saduwa tsakanin mace da namijij ne kawai daidai.

    *Idan duniyar za ta koma yadda take a da, dole a hada da dukanmu. Duniyar nan za ta iya koma kamar jiya ne kawai idan aka fara ba 'yan madigo da luwadi damar da sauran mutane suka samu.

  • Ghawgha

    Afghanistan Mawakiya

    Ghawgha, fashiyar mawakiya kuma makidiya wadda ta yi aiki a masana'antar waka na sama da shekara biyar. Wakokinta wadanda yawanci akan matan Afghanistan ce suna da masoya na hakika, sannan tana kalubalantar halin da kasar ke ciki yanzu a wakokinta.

    A shekarar 2019, ta yi wake wakar bakar 'I kiss yoy amid the Taliban' na Ramin Mazhar, wadda cikin kankanin lokaci ta yadu a kafofin sadarwa. Wakar na karshe-karshen nan, Tabassum sadaukarwa ce ga kananan yara da yaki ya sa suka kasa cimma burinsu.

    Ghawghara ta ce tana rubuta waka ne "domin kawo karshen yake-yaken da suke ci suka ki cinyewa kuma suka ni samun natsuwa," sannan tana bayyana irin wahalhalun a wakokinta.

    *Sararin samaniyar kasata a rufe take da nakiyoyi. A kullum ina cikin tunanin mutanen kasar, musamman ma mata da kananan yara. Fargabar da nake yi shi ne halin da suke ciki.

  • Angela Ghayour

    Afghanistan Malama, kuma shugabar makaranta a yanar gizo

    Makarantar Herat ta yanar gizo ta Angela ta kirkira na da dalibai kusan 1,000 da sama da malamai 400 da suke koyarawa kyauta. Ta fara makarantar ta yanar gizo ce a lokacin da Taliban suka ce mata da 'yan mata su zauna a gida. Yanzu haka makarantarta tana da ajujuwa sama da 170 da ake karatu a manhajar Telegram ko Skype kuma ana karantar da darussan lissafi da waka da abinci da zane da sauransu.

    Ita kanta Ghayour ta taba guduwa zuwa Iran daga garinta Herat a shekarar 1992 lokacin da aka fara Yakin Basasa, inda ta rasa shekara biyar a cikin shekarun karatunta saboda matsalar bisa da suka fuskanta.

    Daga baya sai ta zama malamar sakandire, kuma ta yi ta canja kasashe kafin yanzu take zaune na dindindin a Ingila.

    *Ban yarda in amince da wannan zaluncin ba: Za a samu walwalar mutane ne kawai idan duniya ta yaki zalunci ta hanyar kin amincewa da Taliban ko sauran zalunci da ake yi.

  • Jamila Gordon

    Somalia Babban Jami'ar Gudanarwar kamfanin Lumachain

    Jamila Godon sananniya ce a bangaren fasahar zamani ta Artificial Intelligence (AI), kuma shugabar kamfanin Lumachain, wanda shi ne kamfani na farko irinsa a duniya da aka yi amfani da fasahar basirar na'ura Artificial Intelligence, domin ƙoƙarin ganin abinci ya zagaye duniya cikin sauƙi.

    An haife ta ne a wani ƙauye a Somalia, kafin suka yi gudun hijira zuwa Kenya domin guje wa Yakin Basasar kasarsu tana ƙarama. Daga can ne ta tafi Austreliya, inda ta fara sha'awar harkokin fasahar zamani. Kafin ta ƙirƙiri Lumachain, ta kasance Jami'ar IBM, sannan ta riƙe Babbar Jam'iar Yada Labrai ta Qantas.

    Ta taɓa lashe gasar Mata 'Yan Kasuwa na Duniya na Kamfanin Microsoft na shekarar 2018, sannan ta zama Mace Mai Kirkirar Austreliya da New Zealand ta shekarar 2021 a gasar fasahar AI.

    *Ina da sakankancewar cewa fasahar Artificial Intelligence za ta taimaka wa mutane marasa galihu su kai ga cimma burukansu, sannan za ta taimakawa kasuwanci matuka.

  • Najilla Habibyar

    Afghanistan Yar kasuwa

    Najilla Habibyar ce ta assasa Blue Treasure Inc da Ark Group domin taimakawa matan Afghanistan wajen sana'ar saka da kasuwancsa zuwa kasashen ketare ba tare da wahala ba. Ta jagoranci shirye-shiryen USAID da Bankin Duniya masu alaka da tallafawa mata da sauyin yanayi.

    A tsakanin shekarar 2012 da 2015, Habibyar ta rike Babbar Jami'ar Hukumar Fitar da Kayayyaki Ketare, inda ta yi kokari wajen inganta harkokin cinikayya tsakanin Afghanistan da kasashen waje.

    Ta kuma yi ayyukan gidauniya na sama da shekara 13, inda suka tallafawa karatun mata sannan suka kirkiri kungiyar Afghan Veracity Care for Unsheltered Families.

    *Duk da bakar wahalar da na sha a kasancewata 'yar Afghanistan, ina da burin bayar da gudunmuwata wajen kawo karshen gadar da yake-yake ga jikokinmu.

  • Laila Haidari

    Pakistan Shugabar Mother Camp

    Ta hanyar amfanI da cibiyar Kabul drug rehabilitaion center, da Mother Camp, Laila Haidari ta taimaki kusan 'yan Afghanistan 6,400 tun bude wajen a shekarar 2010 duk da kyamatar masu ta'ammuli da kwayoyi da ake yi a kasar. Da kudinta ta bude cibiyar sannan ta cigaba da gudanar da ita da kudin da take samu daga wajen cin abinci da ta bude da wadanda ta gyara wa tunanin suke aiki a ciki, wanda aka rufe bayan Taliban sun kwace Kabul.

    Asalin Hadairai mutanen Bamyan ne, amma an haife ta ne a sansanin gudun hijira a Pakistan. Ta yi aure tana da shekara 12, sannan ta yi fice wajen fafutikar kare hakkin mata.

    Ta fito a shirin Laila at the Bridge a shekarar 2018, inda a fim din ta bayyana gwagwarmayar da ta sha wajen cigaba da gudanar da cibiyarta duk da kokarin da wasu suka yi ta yi na ganin bayan cibiyar.

    *Zan so wannan wayar da kan ya cigaba yadda za mu samu duniya mai amnci. Muna rayuwa a duniya da kusan a hade take yanzu, ta yada kuri'ar mutumi Amurka zai iya canja rayuwar dan Afghanistan.

  • Zarlasht Halaimzai

    Afghanistan Shugabar Refugee Trauma Initiative

    Zarlasht Halaimzai tsohuwar 'yar gudun hijira ce da ta hada hannu da wasu suka assasa Refugee Trauma Initiative da take shugabanta domin gyara tunanin masu gudu hijira da taimaka musu wajen yaki da damuwar da suke ciki.

    Kafin assasa RTI, ta yi aiki a tsakinin bodar Syria da Turkiyya, inda take taimakon yara marasa galihu su samu ilimi tare da ba gidauniyoyi shawara akan tallawa 'yan gudun hijira su samu ilimi da kuma jin dadinsu.

    Halaimzai tana cikin daliban farko na Obama Foundation Fellows na 2018, inda aka zakulo mutum 20 a duniya masu fasahar kirkira wanda tsohon Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya dauka nauyi.

    *Burina shi ne a nan gaba a kawo karshen rikice-rikicen da muke ciki a wannan kasar domin rikice-rikice na kawo cikas ga rayuwar mutanen Afghanistan.

  • Shamsia Hassani

    Iran Mai nishadantar da jama'a

    A garin da yake-yake ya dabaibaye, Shamsia Hassani ita mace ta farko 'yar Afghanistan da take rawar kan titi. Tana amfani da gine-ginen da aka yi watsi da su a Kabu wajen zane-zanen jikin bango da harkokinta na nuna mata a matsayin masu karfin iko kuma masu dogon buri.

    A Iran aka haife ta, amma iyayenta 'yan Afghanistan ne, kuma ta yi karatun Visual Arts a Kabul, sannan ta koyar a Jami'ar Kabul, sannan ta yi zane-zanenta a kasashe sama da 15. Tana cikin mutum 100 masu zurfin tunani na Mujallar Foreign Policy, sannan ta rubutunta ya fito a cikin littafin kananan labarai na Rebel Girls.

    Duk da kwace kasar da Taliban suka yi, har yanzu Hassani tana cigaba da yade zane-zanenta a kafofin sadarwa

    *A shekara 15 da suke wuce, duk lokacin da na fara tunanin samun nasarar kasarmu, sai abubuwa su kara lalacewa. Ba na tunanin za a samu wata nasara- Ya fi kyau mutum daina tsammanin, maimakon zama mara tsammanin.

  • Nasrin Husseini

    Afghanistan Likitar dabbobi

    Da take karatun zama likitar dabbobi a Jami'ar Kabul, Nasrin Husseini tana cikin mata biyu kacal da suke karatu a cikin dalibai 75. Ta taso ne a matsayin mai gudun hijira a Iran, amma ta dawo Afghanistan ta cigaba da karatu, sannan daga baya ta koma Canada bayan ta samu tallafin karo karatu daga Jami'ar Guelp.

    Yanzu haka Husseni tana aiki da bangaren gwaje-gwajen jini, sannan takan yi amfani da sauran lokacin da take da shi ta yi aikin sa kai da Gidauniyar Hazara Humanitarian Services, inda take taimakon mazauna Hazara da sauran garuruwan aka danne daga Afghanistan da suke da burina komawa da zama a Canada.

    Tana kuma aiki da shirin matasa na Bookies, inda suka habaka karatu da rubutu a tsakanin matasan Afghanistan.

    *Mata da 'yan matan Afghanistan suna cikin fargabar halin da suke ciki a yanzu na rashin tabbas, amma akwai alamar nasara. Kamar yadda Bob Marley yake cewa, "Ba za ka san karfin zuciyarka ba sai lokacin da karfin zuciyar ce kawai ta rage maka."

  • Momena Ibrahimi

    Afghanistan Yar sanda

    Momena Ibrahimi, wadda aka fi sani da Momena Karbalayee 'yar sanda ce da wani na gaba da ita a aikin dan sanda ya ci zarafinta shekera uku bayan ta fara aikin. Sai ta yanke shawarar fitowa fili ta yi magana kan cin zarafin tare da bayyana sauran zarge-zarge cin zarafin da ke faruwa a cikin aikin dan sandan Afghanistan.

    Tun lokacin take fafutikar kwato wa kanta 'yanci da sauran wadanda aka yi wa fyade da sauran cin zarafi duk kuwa da barazanar da ake mata. 'Ina da tunanin ya kamata wani ya fito ya yi magana, kuma ina ganin ni ce wanna mutumin, ko da kuwa zan rasa raina,' kamar yadda ta bayyanawa BBC.

    Ibrahimi tana cikin dubban mutanen da aka kwashe zua Ingila bayan Taliban ta kwace kasar a Agustan da ya gabata.

    *Ina ma a ce matan da suka sha gwagwarmaya suka yi karatu suka fara cimma burukansu za su dawo su daura daga inda suka tsaya sannan su samu 'yanci daga masu uzura musu.

  • Mudgha Kalra

    Indiya Daya daga cikin wadanda suka assasa Not That Different

    Mai fafutikar kare hakkin zabiya, kuma uwar 'yar shekara 12 da ita ma zabiya ce, Muhdha tana cikin wadanda suka assasa Not That Different, wadda gidauniya ce da aka assasa domin tabbatar da hakkin masu bambancin halitta.

    Kalra ta kwashe sama da shekara 20 tana aikin jarida.

    Ta kuma yi aiki da rediyon intanet na Bakstage, inda take gabatar da shirye-shiryen kai-tsaye.

    *Annobar nan ta sa biliyoyin mutane sun koma rayuwa iri daya, kowa na duniyarsa daban, amma kuma an samu hadaka a wahalar da aka shiga. Zan so wannan wahalar aka shiga ta sa mu kara jin tausayin junanmu.

  • Freshta Karim

    Afghanistan Shugabar Charmanghz Mobile Library

    Gidauniyar Charmaghz ta taimakawa wajen mayar da motocin bas zuwa dakunan karatu, sannan suka yi zagaye a garuruwa makwabtan Kabul domin tattara littafai da zane-zane domin amfanar da daruruwan yara kanana/

    Freshta Karim, wadda mai rajin kare hakkin kananan yara ce, ta kirkiri Charmagzh a shekarar 2016 ne bayan ta kammala digirinta na biyu daga Jami'ar Oxford, inda ta karanci Public Policy.

    Ta fara aiki ne tana da shekara 12, inda take tara yara kanana a gidan talabijin suna gudanar da shiri, sannan take fitar da rahotannni kan halin da yara kanana suka ciki a Afghanistan kuma har yanzu tana cigaba da hakan.

    *Ina aiki da yara ne domin ina ganin su ne ginshikin goben Afghanistan domin magance zalunci da rikice-rikice tare da bude hanyar zaman lafiya da canja yanayin siyasar kasar.

  • Amena Karimyan

    Afghanistan Masaniyar ilimin taurari

    Injiniyar zane-zanen gini ce kuma malama a kwalejin Herat Technical Institues, kuma ta kasance cikin matan farko da suke mayar da hankali kan cigaban ilimin taurari a kasar.

    Ita ce Shugaban Kayhana Astronomical Group, wanda ta assasa a shekarar 2018 sannan take kokarin karfafa gwiwar sauran mambobinta su koya harkar.

    A Yulin 2021, Karimyan da kungiyarta da dukkan mambobinta mata ne suka lashe karramawar Astronomical Union ta duniya a gasar masana taurari ta duniya da aka gudanar a Poland, bayan suna zama na na daya a cikin kungiyoyi 255 daga sama da kasashen duniya 50 da suka higa gasar.

    *A daidai lokacin da Taliban suka 'ya'ya mata karatu, yanzu ya kamata mu kara karfi da karfe sama da-Kungiyar Kayhana Astronomical Group na taro kullum ta yanar gizo. Burina kawai ina bude wa matasan kasarmu kofa.

  • Aliya Kazimy

    Afghanistan Malama

    A aikin kwato hakkin dan Adam da ilimantar da su, Aliya Kazimy ta sadaukar da lokacinta kafin Taliban suka kwace kasar. Ta yi aiki da kungiyar Red Cross na sa kai na shekara uku, sannan ta bude gidan biredi da abinci ga matan da suka karanci digiri na biyu akan Bunkasa Kasuwanci a 2020. Ta koyar a jami'a.

    Bayan Taliban sun kwace kasar a 2021, sai ta koma Amurka inda a yanzu take kokarin fara karatun digiri na uku.

    Ta rubuta wasika zuwa ga BBC, inda ta bayyana ra'ayinta kan 'yancin mata, musamman kan yadda suke sha'awar sanya tufafi.

    *Burina ga Afghanistan kawai shi ne a samu zaman lafiya. Zaman lafiya muka fi bukata.

  • Baroness Helena Kennedy QC

    Birtaniya Darakta-Internationan Bar Association's Human Right Institues

    Lauya ce 'yar asalin Scotland da ta yi fice wajen kare hakkin mata da wadanda aka danne musu hakki. Baroness ta yi aikin lauyanci a bangaren laifuffuka na tsawon shekara 40. Ita ce darakta yanzu a Internationan Bar Association's Human Right Institues, wanda yake taimakon mata a Afghanistan.

    Ita ce shugabar Kwalejin Mansfield a Jami'ar Oxford na shekaru da yawa, sannan ya taimaka wajen kirkirar Bonavero Institute of Human Rights a kwalejin.

    Baroness Kennedy ta rubuta littafai akan shara'a r da suka shafi mata sannan a shekarar 1997 aka nada ta wakiliyar kwadago a House of Lord.

    *Fafutikar kare hakkin dan Adam bai da ma'ana har sai an samu lauyoyi masu aiki da kyau da alkalai maza da mata masu cin gashin kansu.

  • Hoda Khamosh

    Iran Mai wayar da kan mata kan jinin al'ada

    Jinin al'ada ba abin kyama ba ne shiri ne da Hulda Khamoosh ta assasa domin wayar da kan mutane da kuma bayar da damar tattaunawa akan jinin al'ada a makarantun Afghanistan.

    A Iran aka haife ta bayan iyayenta sun yi gudun hijira amma ta dawo Afghanistan tana karama inda mahaifiyarta ta cigaba da tallafawa karatunta duk da rashin amincewar 'yan uwanta. Haka kuma mawakiyar baka ce kuma 'yar jarida da ta zama mai gabatar da shirye-shirya a rediyo a shekarar 2915, inda shirye-shiryenta suka mayar da hankali kan rashin adalcin da ake yi a mata, sannan ta fara shirin ilimantar da mata a kauyenta.

    Tun bayan da Taliban suka kwace Afghanistan, sai take gudanar da karatuttuka ga kananan yara mata da ke aji bakwai zuwa sama da ba a yanzu a bari suna zuwa makaranta.

    *Duk da rashin duhun da ta zo da shi, 2021 shekara ce da mata suka tsaya tsayin daka suka cire tsoron bulalai da alburusai suka dage wajen kwato hakkinsu daga wadanda suka kwace musu. Na kira wannan shekarar da shekarar nasara.

  • Mia Krisna Pratiwi

    Indonesiya Masaniyar muhalli

    Mai fafutukar magance matsalolin muhalli a tsibirin Bali ta hanyar amfani da gidauniyarta ta Griya Luhu. Tare da gudunmuwar mutanen garin, gidauniyarta ta kirkira manhajar "digital waste bank' da ake amfani da shi wajen tattara bola a sana'anta shi tare da tattara bayanan da za a yi amfani da su wajen magance matsalar yawaitar bola.

    Tana da digiri a tsabtace muhalli daga Jami'ar Instut Teknologi Bandung, kuma ta yi aiki a matsayin manajar gudanarwa da take kula da harkokin yau da kullum na kula da bolar.

    Haka kuma mai bincike ce a kan tsabtace muhalli a Cibiyar Tsabtace Muhalli ta birnin Denpasar da ke Indonesia.

    *A madadin kokarin tsarin Balinese na Tri Hita Karana, ina so a dawo da daidaito a duniyarmu. Watakila mu ne muka jawo matsalar, amma za mu iya nemo maganinta.

  • Heidi J. Larson

    Amurka Darakta- Shirin The Vaccine Confidence

    Farfesa Heidi J. Larson wadda masaniyar halayyar dan Adam ce kuma darakta a shirin The Vaccine Project a Kwalejin lafiya na Hygiene & Tropical da ke Landan, ita ce ta jagoranci binciken abubuwan da suke kawo cikas ga tallafin da ake ba bangaren lafiya, kuma yanzu haka ta fi mayar da hankali a harkokin bincikenta kan rage yada jita-jita da kuma wayar da hankalin mutane kan rigakafi.

    Ita ce ta wallafa littafin STUCK: How Vaccine Rumors Start- da Why They Don't Go Away, sannan ita ke jagorantar bincike yadda masu juna biyu ke amincewa da rigakafi a duniya.

    An bai wa Dakta Larson karramawar Edinburg ta shekarar 2021 bayan la'akari da aikinta kan daƙile yaɗa jita-jita.

    *Annoba ta zo mana a lokacin da duniyar take cikin ruɗu. Babu rigakafin da zai tseratar da mu daga abubuwan da suka raba kanmu; aikinmu ne a matsayinmu na ɗaiɗaikun mutane ko al'umma ko shugabanni zai iya taimakonmu.

  • Iman Le Caire

    Misra Shugabar Trans Asylias

    Yar rawar zamani ce a dandalin Cairo Opera House kuma mai koyar da rawa. Dole ta sa Iman Le Caire ta bar Misra saboda 'yan sanda na kyamatar 'yan madigo da luwadi. Ta koma Amurka ne a shekarar 2008, inda aka ba ta mafaka kuma yanzu take zama a New York a matsayin 'yar rawa, jaruma sannan kuma mai fafutikar kare hakkin 'yan madigo da luwadi.

    Le Caire manajan kula da alaka ce tsakanin Larabawa, kuma mamba ce a TransEmigrate, wanda kungiya Turai ce mai taimakon masu canja jinsi da suka gudo daga kasashensu.

    A watan Maris na bana, ta assasa gidauniyarta mai suna Trans Asylias, wanda aikins shi ne shigar da wadanda suka gudo daga kasashensu saboda canja jinsi cikin mutane masu kaunarsu tare da ba su tallafi.

    *Annobar nan ta kara jefa mutanen da suka canja jinsinsu cikin damuwa a duniyar nan, da kuma kara jefa su cikin damuwa fiya da da ta yadda ya turasasa su zama da iyalan da ba sa sonsu na dole kuma ba a jin kokansu. Yanzu ya kamata duniyar ta taimake su.

  • Sevidzem Ernestine Leikeki

    Kamaru Mai fafutikar canjin yanayi

    Ta hanyar amfani da kimiyyar tattara zuma wajen rage wutar daji, kungiyar da Sevidzem ta assasa ta koyar da sama da masu kiwon zuma 2,000 hanyoyin samar da zuma ingantacciya, sannan ta dasa sama da bishiyoyi 86,000 da kudar zuma ke so domin rage matsalar canjin yanayi a sanadiyar sare itatuwa.

    Leikeki tana cikin mambobi na farko a Kungiyar Lura da Bambancin Jinsi da Muhalli ta Kamaru (CAMGEW), wadda ke fafutikar nemo hanyoyin magance matsalolin da kasar ke fuskanta kan muhalli da bambancin jinsi. A matsayinta na mai fafutikar samar da yanayi mai kyau, tana mayar da hankalinta ne kan tallafawa mata da kuma sanya su a cikin harkokin kula da albarkatun kasa.

    Tana da fahimtar cewa dazuka-kamar dajin Kilun-Ijim mai girman hekta 20,000- za a iya killace shi ta hanyar hada karfi da karfe domin ya amfanar da al'umma da shi.

    *Ina son a rika lura da gudunmuwar mata yadda ya kamata na kula da dazuka da zamantakewa da tattalin arziki.

  • Elisa Loncon Antileo

    Chile Shugabar Contitution Convention

    Elisa tana cikin wadanda aka zaba a shekarar 2021 a matsayin daya daga cikin mutum 17 da za su rubuta sabon kundin mulkin Chile. Elisa masaniyar harsuna ce kuma malama. Ita ce shugaban Constitutional Convention, karo na farko da dan kasar Chile zai kasance a wakilin kasarsu.

    Loncon 'yar kabilar kasar Chile mafi girma ce, wato Mapuche, sannan tana fafutikar abin da ake kira 'plurination state' wanda ke kokarin ganin kabilu sun samu 'yancin gudanar da al'adunsu da harshensu.

    Duk da cewa ta taso cikin talauci ne, kuma ta fuskanci kalubale wariyar kabila, ta yi karatu har matakin digirin digirgir a bangaren sanin dan Adam, yanzu kuma farfesa ce a Jami'ar Santiago.

    *Bayan ganin yadda aka riƙa mutuwa kusan kullum lokacin wannan annobar, lallai yanzu ya kamata a ba kowa hakki daidai da kowa a matsayin dan Adam. Dukanmu rayuwarmu na gudana ne da albarkatun kasa da ruwa da bishiyoyi da kudar zuma da ƙwari.

  • Chole Lopes Gomes

    Faransa Yar rawa

    A matsayinta na baƙar fata ta farko mai rawar ballet da babban kamfanin Staatsballett Berlin ya dauka a shekarar 2018, Chloe Lopes Gomes wadda tsohuwar ɗalibar makarantar Mosco Bolshoi Academy ce, ta sha fama da matsalar nuna wariyar launin fata a tsakanin masu rawar ta ballet, wadda ta bayyana da abun da yake tattare da 'nuƙu-nuƙu kuma na masu hannu da shuni'.

    Bayan ta fara fitowa a idon duniya, sai bakaken fata da ruwa biyu a cikin masu rawan suka fara goya mata baya.

    Lopes Gomes ta shigar da karar Staatsballett lokacin da suka ƙi sabunta kwantiraginta a shekarar 2020. A dalilin hakan, sai kamfanin ya fara binciken nuna wariyar launin fata a tsakanin ma'aikanta wanda a sanadiyar hakan, kamfanin ya nemi afuwarta sannan aka biya ta diyya.

    *Abin bakin ciki shi ne yadda muke da bambanci a duniyar nan, sannan samun nasarorinmu yana ta'allaka ne da yanayin kabilarmu da karfin ikonmu. Ina son ganin duniyar da za a ba kowa dama iri daya wajen cimma burinsa.

  • Mahera

    Afghanistan Likita

    Dakta Mahera har yanzu tana cigaba da aikin lura da marasa lafiya a bangaren karbar haihuwa a sibitin da take aiki.

    Tana zirga-zirga zuwa yankunan da a yanzu babu asiboti tun bayan da Taliban suka kwace mulki, inda take aikin lura da marasa lafiya da shawarwari.

    Ta taba yin aikin kula da wadanda aka nuna wa wariyar jinsi, amma yanzu ta daina wannan aikin tun bayan da Taliban suka kwace kasar.

    *Duk da cewa yanzu babu alamar wata nasara, amma matan Afghanistan ba haka suke ba a shekara 20 da suka wuce, kuma yanzu za su iya kare hakkinsu daidai gwargwado. Damuwata kawai ita ce hana mata karatu na har abada.

  • Maral

    Afghanistan Mai fafutika

    Iyayen Maral ba sa so ta shiga fafutikar kare hakkin mata ko ta shiga wata kungiya. Suna da tunanin bai kamata tana zuwa aiki ba a matsayinta na 'ya mace, amma sai da ta yi.

    Tun a 2004, Maral take ta hada kan mata a unguwanni sannan take karfafa musu gwiwa su nemi ilimin hakkinsu sannan su fito su rika zuwa aiki kuma su nema kudadensu.

    Ta kuma yi aiki da mata a kauyuka da suka fuskanci rikice-rikcen gida, inda take tabbatar da sun samu mazauni, sannan sun kwato hakkinsu.

    *Na yi zaton mun rasa komai, kuma babu wata nasara, amma na tuna duk abubuwan da muka yi, sai na kara samun kwarin gwiwa. Don haka ba zan fidda rai ba-zamanin gaba yana ga wadanda suke son zaman lafiya ne.

  • Masouma

    Afghanistan Lauya

    A matsayinta na lauya a Afghanistan, Masouma ta yi aiki a bangaren shara'a inda take tattara hujjoji. Tana cikin wadanda suka samu damar karatu a shekara 20 da suka gabata, kuma tana alfahari da taimakon mutane da take yi, inda ta yi aiki na sama da shekara biyar a ofishin Babbar Jojin kasar.

    Lokacin da Taliban ta kwace kasar a Agustan bana, sai suka saki fursunoni, ciki har da dubban manyan masu laifuka da 'yan ta'adda. Kungoyiyin kare hakkin dan Adam na duniya sun ruwaito kisan gilla da garkuwa da mutane duk da cewa Taliban ta ce ta ta shiga yarjejeniya da ma'aikatan gwamnati.

    Masouma yanzu a boye take rayuwa ba tare da sanin me gobe za ta haifar ba.

    *Mata da 'yan mata ne rabin mutanen duniya, sannan idan suka samu dama, za su amfanar da mutane da kasarsu kamar maza.

  • Fiame Naomi Mata'afa

    Samoa Firayi Minista

    Mace ta farko da ta zama Firayi Ministan Samoa, kuma Shugabar Jam'iyyar Fa'atuata i Le Atua Samoa us Tasi (FAST). Fiame Naomi Mata'ata ta fara siyasa ne tana da shekara 27, kuma ta rike Mataimakiyar Firayi Minista, da Ministar Mata da Jin dadin al'umma sannan ta rike Ministar Shari'a.

    Tana kuma da sarauta babba (matai), kuma abar koyi ce ga matan Samoa da suke neman kujerun siyasa.

    Tana mayar da hankalinta sosai kan gyaran muhalli da yaki da gurbacewar yanayi a wani yanki na duniya da ke fama da gurbacewar.

    *Idan har akwai hadin kai, to lallai akwai nasara ga jikokinmu.

  • Salima Mazari

    Iran Yar siyasa kuma tsohuwar gwamnar yanki

    Daya daga cikin mata uku da suka taba rike matsayin gwamnan yanki a Afghanistan, Salima Mazari ta ja hankalin mutane ne a bana bayan ta jagoranci kungiyar goyon bayan gwamnati da ke yaki da kungiyar Taliban kai tsaye.

    Lokacin tana 'yar gudun hijira ne ta yi digirinta na farko a Iran kafin ta dawo Afghanistan. A 2018 ce ta zama gwamnar yankin Charkint a lardin Balkh, inda ta yi yarjejeniyar sulhu da 'yan Taliban sama da 100 da suka mika wuya. Yankinta ya matukar wahalar da 'yan Taliban a 2021 har lokacin da aka ci Kabul da yaki, yankinta na cikin kadan da 'yan Taliban ba su mamaye ba.

    An yi tunanin an kama ta, amma ta samu ta tsere zuwa Amurka inda a yanzu take zaune.

    *Ina da burin lokacin da ba zai zama laifi ba don mata sun yi magana a Hazara ko a Shia ko a Persia-kasashen duk inda da jibi da su.

  • Depelsha Thomas McGruder

    Amurka Shugabar kungiyar Moms of Black Boys Utd.

    Kungiyarta ta tattaro 'iyaye mata bakaken fata' a duk fadin Amurka. Depelsha Thomsa McGruder ita ce ta kirkira kuma shugabar kungiyar iyaye mata ta yara baƙaƙen fata (MOBB) na Amurka da kuma MOBB United domin samar da walwala wadda aka kirkira domin sauya dokoki da tunani zuwa yadda bakaken fata maza ke fuskantar wariya a wajen jami'an tsaro.

    Yanzu haka ita ce Babban Jami'ar Aiwatarwa kuma Ma'ajiya ta Gidauniyar Ford Foundation, inda take lura da aiwatar da shirye-shiryen gidauniyar da harkokin kudadensa.

    A baya, McGruder ta yi shekara 20 tana aikin watsa labarai, inda ta yi aiki daga mai dauko rahoto har ta kai ga rike babban mukami a MTV da Black Entertainment Television (BET)

    *Burina shi ne idan aka gama batun wannan annobar, mutanen duniya za su koyi jin ƙan juna, ta yadda mutane za su fahimci cewa kowa daban yake, tare da koyon tausayi da taimakon wadanda suke cikin matsala.

  • Mulu Mefsin

    Habasha Ma'aikaciyar jinya

    Ma'akaciyar jinya ce ta sama da shekara 10 da suka wuce, inda ta yi aiki da Cibiyar One Stop da ke Mekelle, wanda wani sashe ne na Babban Birnin Habasha, Tiagray. Cibiyar na bayar da tallafin magani da shawarar kwantar da hankali da nemo hakkin wadanda aka ci zarafinsu a kotu.

    Shekara uku da suka wuce, Mefsin ta fara fafutikar ganin an kawo karshen cin zarafin kananan yara a Tiagray, lamarin da yake ci gaba da tayar da kura tun farkon Yakin Basasar kasar da aka fara a karshen shekarar 2020.

    Duk da ta sha fama da matsalar damuwa ita kanta, Nas Mefsin tana so ta cigaba da aiki da burin ganin zaman lafiya ya dawo.

    *Ina son ganin an daina yake-yake an koma zama lafiya a samu kasashe suna aiki tare domin samar da zaman lafiya maimakon yarjejeniyar sayar da makamai, sannan a yi dokokin hukunta masu fyade da cin zarafin mata.

  • Mohadese Mirzaee

    Afghanistan Direbar jirgin sama

    A matsayinta na farkon matukiyar jirgin sama ta farko a Afghanistan, Mohadese Mirzaee ta tuka jirgin Kam Air Boeng 737 lokacin da kasarta ta kafa tarihin jirgin sama na farko da duk ma'atakan ciki mata ne a bana. Bayan ta zama matukiyar jirgin saman fasinja a Satumban 2020, ta tuka jiri zuwa Turkiyya da Saudiyya da India.

    Lokacin da Taliban suka shiga Kabul, Mirzaee tana filin jirgin sama ne tana shirin tashi, tashin ba zai taba faruwa ba. Maimakon tukin, sai ta shiga cikin fasinjojin da suke barin kasar. Mirzaee ta ce, "tsayawa ya kamata a yi domin tabbatar da cewa mata da maza za su iya yin aiki a tare".

    Tana da burin ganin ta cigaba da tuka jirgin sama.

    *Kada ka jira! babu wanda zai zo ya kawo maka kayan aikinka idan ba ka dage ba. Na yi fafutikar kwato nawa, ke ma ki yi na ki, sannan idan muka hada hannu, to babu wanda zai iya tsayawa a gabanmu.

  • Fahima Mirzaie

    Afghanistan Yar rawar rausaya

    Ita ce mace ta farko kuma har yanzu ita kadai ce 'yar Afghanistan da take rawar rausaya - rawar da ke cikin Bikin Sama na 'yan darikar Sufi. Fahima Mrizaie ta assasa kungiyar rawa ta maza da mata mai suna Shohood Cultural and Mystical Organizatio.

    Tana ganin rawa a matsayin wata hanya za ta samu walwala a cikin al'umma mai tsattsaurar ra'ayin addini, inda harkokin da ke hada mata da maza ake masa kallon haram. Ta hanyar hada taruka a fadin kasar, tana da burin ta sa kaunar juna a tsakanin mutanen Afghanistan.

    A shekarar 2021, dole ta sa ta bar kasar bayan Taliban sun kwace Afghanista domin a wajen Taliban, rawar da take yi ya saba wa shara'ar Musulunci.

    *Ina da sha'awar sanya addini a gaban komai: Yana da kyau mu samar da aminci a zukatanmu, sannan wannan amincin da muka samar ya wanzu zuwa sauran duniya.

  • TIaleng Mofokeng

    Afirka ta Kudu Jami'ar yada labarai ta Majalisar Dinkin Dunya kan hakkin samun ingantacciyar lafiya

    Dokta T, kamar yadda ake kiranta, likita ce, kuma mai fafutikar wayar da kan mata kan lafiyar saduwa da haihuwa, wadda ke fafutikar ganin an samu ingantacciyar lafiya a duniya kuma an samu maganin HIV da tazarar haihuwa.

    Dokta TIaleng a yanzu ita ce Jami'ar Yada Labarai akan hakkin kula da lafiyar jiki da kwakwalwa ta Majlisar Dinkin Duniya - ita ce mace ta farko daga Afirka, mutum na farko daga Afirka, sannan daya daga cikin mutane masu kananan shekaru da suke rike matsayin. Sannan ita ce ta wallafa littafin Dr T: A Guide to Sexual Health and Pleasure wanda ya yi kasuwa sosai.

    Mofekong tana cikin wadanda suka lashe kyautar '120 Under 40) na gwarazan matasa masu wayar da kan mutane kan tazarar haihuwa na makarantar lafiyar Institue for Population and Reproductive Health Bill & Melinda Gates na shekarar 2016.

    *Yaya nake son ganin duniyar ta gyaru kamar yadda take a da? sai dai ta hanyar horar da junanmu son junamu da son al'ummarmu.

  • Tanya Muzinda

    Zimbabwe Yar tseren babur

    Ta shiga wasa wanda maza ne suka yi fice a cikinsa na tseren babura, Tanya ce mace ta farko daga kasarta da ta lashe gasar tseren babura. Ita ce kuma mace ta farko da ta lashe gasar tun farkonta a shekarar 1957.

    Ta gaji tseren baburan ne daga mahaifinta wanda shi ma dan tseren ne. Ta fara atisayen koyo ne tana da shekara biyar. Yanzu a shekara 17, Muzinda na da burin da burin lashe gasar tseren babura na duniya. A shekarar 2018, ta lashe kambun matashiyar 'yar wasa ta shekara na African Union.

    Da kudin da take samu daga tseren babura take amfani wajen taimakon mutane ta hanyar biya musu kudin makaranta, inda take biyan kudin makarantar dalibai kusan 100 a yanzu haka a Harare.

    *Ba na son mayar da duniya yadda take a da. Dama duniyar ba ta taba zama daidai dari bisa dari ba. A koda yaushe akwai abubuwan daidai akwai wadanda ba daidai ba. Kawai mu gyara yau domin wasu su ji dadi a gobe.

  • Chimamanda Ngozi Adiche

    Najeriya Marubuciya

    Fitacciyar marubuciya ce, kuma mai fafutikar kare haƙƙin mata, wadda aka fassara rubutunta da harsuna sama da 30 a duniya. Chimamanda Ngozi Adiche ta koma Amurka ne tana da shekara 19 domin karatun jami'a, inda ta karanci Kimiyyar Siyasa da Sadarwa.

    Littafinta na farko, Purple Hibiscus (2003) ya lashe gasar Commonwealth, sannan a shekarar 2013, littafinta Americanah ya kasance a cikin littafai goma manya na jaridar New York Time.

    Jawabin Adiche na TEDTalk 2012 mai taken, "We Should All Be Feminists' ne ya sa aka fara tattaunawa akan fafutikar kare hakkin mata, sannan aka buga jawabin a matsayin littafi a shekarar 2014. Ba da dadewa ba ta wallafa littafin Notes on Gried (2021), wanda ta'aziya ce zuwa ga mahaifinta da ya rasu.

    *Ya kamata mu fara tunanin yadda za a samar da ingantacciyar lafiya ga kowa a ko ina a fadin duniya a yanzu-wanda abu ne da mutum ya cancanci samu a matsayinsa na wanda yake raye, ba wai batun ko yana da kudi ko babu ba.

  • Lynn Ngugi

    Kenya Yar jarida

    Lynn Ngugi, fitacciyar 'yar jarida ce da ta samu kyaututtuka da dama musamman da ayyukanta a kafar TUKO, inda take gabatar da shirye-shirye masu tasiri matuka ga cigaban al'umma.

    Ta fara aiki ne na kyauta wajen lura da masu fama da ciwon daji, sannan a shekarar 2011 ta fara aikin da Kiwo Films, sannan daga baya ta koma Qatar Foundation. Haka kuma fitacciya ce a kafofin sadarwa kuma tana cikin fitattun 'yan jarida a kasarta.

    Ta lashe kyautar 'yar jarida mai rahoton kan cigaban al'umma na shekarar 2020 (Cafe Ngoma humanitarian journalist of the year) , sannan a bana ta lashe karramawar Ambasadar 'I Change Nations Community.'

    *Zan so duniyar ta gyaru yadda kowa zai kasance cikin aminci.

  • Amand Nguyen

    Amurka Yar fafutikar walwalar al'umma

    Ita ce Babbar Jami'ar Gudanarwa ta Rise, wadda kungiya ce mai fafutikar kare hakkin wadanda aka ci zarafinsu.

    Amanda N. Nguye mai rajin kare hakkin dan Adam da samar da walwalar al'umma ce da ta ƙirƙiri kungiyar Rise bayan an mata fyade lokacin da take karatu a Jami'ar Harvard, sannan aka ce an ba ta wata shida kacal ta gabatar da shaidu ko a yi watsi da karar. Ta ba da gudunmuwa wajen shirya dokar hakkin wadanda aka yi fyade na 'Sexual Assault Survivors Right wadda ke taimakawa wadanda aka yi wa fyaden wajen tattara shaidu domin nemo haƙƙinsu.

    A shekarar 2021, bidiyonta na yaki da nuna wariya ga mutanen yankin Asia ya yadu sosai a Amurka, wanda ya taimaka wajen dakatar da nuna wariya ga mutanen na Asia

    *Idan muka zama tsintsiya, babu wanda zai zama mai rauni a cikinsu. Babu wanda zai gagare mu idan har mun bukaci ganinsa.

  • Basira Paigham

    Afghanistan Mai rajin kare hakkin jinsi

    Aiki da kungiyar 'yan madigo da luwadi a Afghanistan akwai wuya da fargaba, amma duk da kalubalen, Basira Paigham ta kasance mai fafutikar kare hakkin jinsi a shekaru takwas da suka gabata.

    Tana shirya tarukan wayar da kan mutane kan jinsi da saduwa, sannan kuma tare da abokan aikinta, suna bayar da tallafin kudi ga 'yan kungiyar madigo da luwadi da aka ci zarafinsu. Suna kuma taimakon 'yan kugiyar da suke fuskantar damuwa ko suke tunanin kashe kansu da shawarwar gyara tunani.

    A yanzu tana zaune ne a Ireland, inda take cigaba da fafutikarta na ganin Afghanistan ta amince da kungiyar 'yan madigo da luwadi kuma a kare hakkinsu.

    *Afghanistan a shake take a yanzu, ya kamata a barta ta sarara; Amma za ta sarara ne kawai idan aka kowa damar gudanar da rayuwarsa cikin farin ciki ba tare da la'akari da jinsi ko kabila ko addini ba.

  • Natalia Pasternak Taschner

    Brazil Masaniyar kwayoyin halitta da kimiyyar kimiyyar sadarwa

    Ta kawo wa miliyoyin mutane bayanan kimiyya masu muhimmanci, inda ta ceci rayuwar mutane a Brazil a lokacin annobar covid-19 ta hanyar amfani da shafinta na jarida da shirye-shiryenta na rediyo da talabijin.

    Natalia Pasternak marubuciyar kimiyya ce kuma masaniyar kwayoyin halitta da take da digirin digirgir a kwayoyin halittar bacteria daga Jami'ar Sao Paulo. Aikinta ne ya sa fitaccen marubucin kimiyya Stuart Firestein ya gayyace ta zuwa Jami'ar Columbia da ke New York.

    Paternak ce ta kirkiri kuma a yanzu take shugabantar Instituto Questao de Ciencia (Question of Science Institues), wanda gidauniya ce da aka assasa domin yada binciken kimiyya ga jama'a.

    *A matsayina na jikar wanda aka kashe, na san abin da gwwamnatin kama-karya za ta iya yi wa mutane. Maganganuna a lokacin annobar covid-19 a Brazil ne gudunmuwata domin ciyar da muradun "Never Forget"

  • Monica Paulus

    Papua, New Gunnea Mai wayar da kan mutane kan matsalolin maita

    Domin taimakon mutane wadanda aka zarga da maita da makamantansu (SARV), Monica Paulus, wadda mai fafutikar kare hakkin dan Adam ce, sai ta hada hannu da wasu wajen assasa kungiyar Highlands Women Human Rights Defenders Netork. Aikin kungiyar ya ƙunshi samar da mazauni da ƙwato hakkin matan da aka zarga maita da kuma kai rahoton halin da suke ciki zuwa Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin duniya.

    Aikinsu ya taimaka wajen tursasa gwamnatin Papua ta kafa kwamitin duba matsalolin rikice-rikicen maita da makamantansu.

    A shekarar 2015, Paulus tana cikin matan UN 'Women of Achievements, sannan ta karɓi karramawar mata masu karfin zuciya na Papua, New Guinea. Sannan Kungiyar Amnesty International ta bayyanata a matsayin daya daga cikin mata masu karfin zuciya na duniya.

    *Akwai bukatar mu fahimci cewa dukanmu mutane ne, don haka bambancin jinsi bai kamata ya raba mu ba.

  • Rehana Popal

    Afghanistan Lauya

    Rehana Polpal kwararriyar lauyar shigi da fice ce da yanzu haka take aiki da masu fassara na Afghanistan da suke rage bayab Turawan Birtaniya sun bar Aghanistan.

    Popal ce lauyar Afghanistan ta farko da ta yi aikin lauya a Ingila da Wales. Ta zo Ingila na gudun hijira tana da shekara biya, inda ta karanci shara'a, kuma yanzu take aikin kwato wa mutane 'yanci.

    A 2019, an karramata a matsayin Lauyar Shekara a taron Inspirational Women in Law Awards.

    *Ina da burin ganin a nan gaba mata da 'yan matan Afghanistan sum samu 'yancin neman ilimi su yi aiki kuma su yi rayuwarsu ba tare da fargaba ba.

  • Manjula Pradeep

    Indiya Mai fafutikar kare hakkin dan Adam

    Lauya ce, kuma mai fafutikar kare hakkin garuruwan India da suke fama da matsalolin rashin ababen more rayuwa. Manjula Pradeep ta taso ne daga dangin Dalit na yankin Gujarat, ta yi fice a ayyukanta na yaki da nuna wariyar launin fata ko wariya yanayin siffa, wanda ya fi kamari a India. Ta kuma taba yin aiki a matsayin Babbar Darakya na Navsarjan Trust, wanda shi ne babban kungiyar kare hakkin kabilar Dalits (wanda a da ake kira abu mara tabuwa)

    A bana, ta hada hannu da wasu domin assasa National Council of Women Leaders. Haka kuma ta assasa Wise Act of Youth Visoning and Engagement, wanda ke fafutikar nemo hanyoyin da za a karfafa wa matasan kasar da aka danne su.

    Ta kasance a cikin mambobin International Dalit Solidarity Network, wanda ke kokarin kawo matsalolin Dalit ga Majalisar Dinkin Duniya a taronta na yaki da nuna wariyar fata.

    *Ina son duniya ta dawo yadda take a da inda akwai son juna da kaunar juna, inda kuma mata daga kananan garuruwa za su jagoranci samar da amintacciyar al'umma.

  • Razman

    Afghanistan Mawakiya

    Razma fitacciyar mawakiya ce a Afghanistan da take amfani da kayan kidan da maza suka fi amfani da su. Ka karanci kida da zane-zane kuma ta fito ne daga gidan kida. Ta yi aiki da fitattuna masu nishadantarwa a Afghanistan da wasu kasashen duniya.

    Ta ce ta hanyar amfai da wakokinta, tana da burin nuna wa duniya wani bangaren na mutanen Afghanistan ba wai rikice-rikice ba kawai. A matsayinta na mawakiya da a yanzu ba za iya yin waka ko kida ba, yanzu tana cikin damuwa.

    An hana kida waka a lokacin mulkin Taliban na farko a tsaknin 1996 zuwa 2001, hakan ya sa Razma take fargabar taihin zai maimaita kansa akan mawakan Afghanistan.

    *Idan ina tuna yadda mutane za su zauna ba tare da waka da kida ba, sai in kara shiga damuwa. Ina fata muryoyin matan kasar nan za su hadu domin bayyana ra'ayinsu.

  • Rohila

    Afghanistan Daliba

    Rohila daliba ce da hana 'ya'ya mata karatu da Taliban suka yi ya shafe ta. Ta fi son karatun Kimiyya da Turanci, sanna duk safiya tana gogoriyon bin 'yan uwanta maza zuwa makaranta.

    Rohila ta ce kadan daga cikin kwayenta ne suka shiga intanet, sannan tana ta kokarin koyon ilimi ba tare da malami ba.

    Burinta shi ne ta karanci Psychology sannan ta samu tallafin karatu ta tafi kasar waje.

    *Yanzu an cire Afghanistan daga sauran duniya, sannan burina na samun ilimi yanzu ya zama na banza. Ina fata kasashen dunya ba su manta da mu, sannan ina fata kokarin da muka yi na shekaru bai tafi a banza ba.

  • Alba Rueda

    Ajantina Mai fafutikar kare hakkin masu canja jinsi

    Ita ce mace ta farko da ta canja jinsi da ta rike babban mukamin gwamnati a kasarta. Alba Rueda ce karamar sakatariya a bangaren dokokin fahimtar juna na Ma'aikatar Mata da Jinsi da Fahimtar Juna.

    Ita ce fuskar mata da suka canja jinsi a Ajantina, kuma mai fafutika ce kuma malama wadda take fafutikar ganin an ware wa wadanda suka canja jinsi kashi daya na ayyukan gwamnatin kasar. A watan Yunin shekarar 2021 din nan ne kudurinta ya zama doka bayan ta samu goyon bayan majalisa.

    A 2019, Rueda ta kai wani fasto kara kotu saboda ya ki canja sunanta da ke coci ya yi daidai da yadda sunanta yake a takardunta na kasa.

    *Shekarar 2021 ta bayyana matsalolin tsare-tsaren da suke tattare da nuna bambanci. Ya kamata mu rika karfafa dokoki da suke la'akari da wadanda suka canja jinsi da zai ba mu dama mu kulla wasu alakar da kuma taimakon al'umma.

  • Ruksana

    Afghanistan Likitar tiyata

    Dokta Ruksana kwararriyar likitar tiyata ce kuma Mataimakiyar Farfesa. Ta assasa wata gidauniya da za ta rika ba masu gudun hijira tallafi kula da lafiyarsu.

    Ta yi aiki a garuruwan da suka fi shiga rikici a lokacin yake-yake, inda ta rika aikin kula da marasa lafiya marasa galihu. Tana aikin sa kai a hukumar kula da cutar kansa, wato National Cancer Control Programme, kuma a yanzu haka tana aikin wayar da kan mutane kan cutar kansa.

    Tana matukar son aikin da take yi na tiyata sannan tana da burin zama abar koyi da daliban likitanci na Afghanistan.

    *Duk wani sauyi da aka samu yana da alaka ne da kokarin shugaba. Ba dole ba ne in zama shugaba, amma zan tsaya a Afghanistan in cigaba da kawo sauyi ga bangaren lafiyar kasar nan da ya tabarbare.

  • Halima Sadaf Karimi

    Afghanistan Yar siyasa kuma tsohon tsohuwar 'yar majalisa

    Tsohuwar 'yar majalisa daga yankin Arewacin Jowzjan, Halima Sadaf Karimi 'yar siyasa ce da ta dade ana damawa da ita.

    Tana cikin kusan mata 70 'yan majalisa a kasarta, kuma mace daya tal daga yankinta na Uzbek inda ta yi fafutikar kwato hakkin mutanenta. Tana da digiri a kimiyyar siyasa da tattalin arziki. Ta yi fice sosai a fafutikar kare hakkin mata, kuma Taliban sun sha yi mata kashedin kisa, wanda hakan ya sa ta sha canja gida da dama.

    A shekarar 2020, Taliban suka kashe kaninta da ke karatu a jami'a.

    *Mulkin da aka sa son rai a ciki ba ya dadawa. Burina shi ne matan Afghanistan su samu 'yancinsu ta hanyar shiga ana damawa da su a harkokin siyasa da al'ada da tattalin arziki da walwalar jama'a-Idan aka yi haka, zai dakatar da matsalolin jin kai da ke fuskanto mu.

  • Roya Sadat

    Afghanistan Mai shirya fina-finai

    Ta yi gomman shekaru tana wannan aiki na shirya fina-finai aikinta ya shiga jerin fina-finan Oscar. Furodusa ce kuma darakta, kuma ita ce darakta mace ta farko a zamanin mulkin Taliban sannan fina-finan suna labari ne akan muryar matan Afghanistan da rayuwarsu da abubuwan da aka hana su.

    Fim dinta mai suna A Letter to the President a shekarar 2017 ya shiga cikin fina-finai da za su lashe gwarzon fim na shekara na harshen waje a taron Academy Award na 90.

    Sadat ce shugaba, kuma cikin wadanda suka kirkiri ROYA Film House, wanda kamfanin shirya fina-finai ne mai zaman kansa, sannan ita ta kirkiri International Women's Film Festival na Afghanistan, inda nan ma take shugabanta.

    *A farkon shekara biyar na mulkin Taliban, na yi tsammanin abin zai kawo karshe, sannan a bude mana makarantu, amma har yau, ina da yakinin muryar mutanenmu ne zai yi nasara.

  • Shogufa Safi

    Afghanistan Mai kida

    A matsayinta na makidiya, Zohra ce mace ta farko da ta fara kida na tsarin ochestra. Ita ce take jagorantar kungiyar mata mawaka masu shekaru tsakanin 13 zuwa 20, wasu daga cikinsu da talakawa ne wasu kuma marayu.

    Ana mata lakabi ne da sunan fitacciyar mawakiyar Persia, kuma tana hada yanayin al'adar Afghanistan da na Turawan domin fitar da sauti mai jan hankali, sannan ta yi kida a gida da kasashen waje tun a shekarar 2014.

    Tun bayan da Taliban ta kwace Afghanistan, an kulle National Institues of Music (ANIM), inda Safi take gudanar da harkokinta. Bayan ta samu damar tserewa zuwa Doha, ita da wasu abokan rawarta-da suka gudo suka baro kayan kidansu a Afghanistan- suna fatar ganin sun cigaba da harkokinsu.

    *Buruku ba sa faduwa kasa banza. Duk da tsantsar rashin tabbas, ina da yakinin zan zama abar koyi da mutanen Afghanistan.

  • Sahar

    Afghanistan Yar kwallon kafa

    Daya daga cikin matasan matan da suke da sha'awar buga kwallon kafa a Afghanistan, amma yanzu ba zai yiwu ba saboda Taliban sun kwace mulki. Saher ta buga kwallo a shekara biyar da suka wuce, sannan ta yi abokai da dama masu irin ra'ayinta.

    Lokacin da Taliban suka kwace mulki a bana, sai ta boye kanta tare da 'yan gidansu kafin suka tsere suka bar kasar.

    Har yanzu tana jin fargabar halin da 'yan uwanta 'yan kwallo mata suke ciki, amma yanzu take da burin ta koma ta cigaba da buga kwallonta.

    *Ina so in cigaba da karatu, sannan in cika burina domin iyayena da 'yan uwa su alfahari da ni. Ina so in samu nasarori ta yadda babu wanda zai kalle ni ya ce wancar yarinyar ba ta iya kwallo ba.

  • Soma Sara

    Ingila Shugabar Everyone's Invited

    Shafin kafar sadarwa na Instagram da yanar gizon 'Everyone's Invited' da Sara ta kirkira a Yunin shekarar 2020 wanda ke kokarin kwato hakkin wanda aka ci zarafinsu ya yi fice matuka. Shafin a bude yake ga duk wadanda aka ci zarafinsu domin su bayyana yadda suka shiga ta hanyar boye asalinsu ba domin kokarin yaki da fyade a makarantun Birtaniya da jami'o'i.

    An samu labarai sama da 50,000 tun kirkirar manhajar, sannan ya kara shahara bayan da aka kashe Sarah Everard bayan an yi garkuwa da ita a wani titi a Landan a watan Maris na bana.

    Soma tana da tunanin fadada fafutikarta ya wuce makarantu domin yaki da lamarin baki daya.

    *Ina so duniya ta saurare ni, ta taimaka min sannan ta rika amincewa da labarin wadanda aka ci zarafinsu.

  • Mahbouba Seraj

    Afghanistan Mai fafutikar kare hakkin mata

    Bayan kwashe shekara 20 tana zama mafakar siyasa a Amurka, Mahbouba Seraj ta koma Afghanistan a 2003 sannan ta hada hannu wajen assasa tare da shugabantar kungiyoyi da dama domin fafutikar kwato hakkin mata-ciki har da sananniyar kungiyar Afghan Women's Network (AWN), kungiyar da ta taimaka wajen sa mata su fito su bayyana ra'ayinsu.

    Ta sadaukar da rayuwarta wajen tallafawa wadanda suka fuskanci rikice-rikicen gida da kokarin nemo hakkin yara su samu ilimi da duba lafiyarsu da yaki da cin hanci. Da Taliban su dawo mulki a Agustan 2021, ta tsaye tare da mutanenta suka cigaba da bayyana damuwarsu kan halin da matan Afghanistan za su shiga a kafofin yada labarai na Afghanistan da na kasashen waje.

    Mujallar Time ta bayyana ta a cikin mutum 100 masu karfin iko a duniya na 2021 wato '100 Most Influential People 2021'.

    *Zaman lafiya shi ne abu na farko da nake son gan a kasata. Ba na son ganin alamar ta'addanci a fuskar 'yan uwana da 'ya'yana a nan gaban da babu tabbas. Tura ta kai bango.

  • Elif Shafak

    Faransa Marubuciya

    Fitacciyar marubuciyar Turkiyya da Birtaniya, kuma mai fafutikar kare hakkin mata da kungiyar 'yan madigo da luwadi.

    Elif Shafak ta wallafa littafai guda 19, ciki har da 10 Minutes 38 Seconds in This Strange World, wanda ya shiga littafan da aka lissafa a gasar Booker Prize, da The Forty Rules of Love, wanda aka zaba a cikin Littafai 100 da suka canja duniya na BBC. An fassara rubutunta a sama da harsuna 50 a duniya.

    Shafak na digirin-digirgir a Kimiyyar Siyasa kuma ta koyar a jami'o'i a Turkiyya da Amurka da Birtaniya. A shekarar 2021, an ba da kyautar karrama ta Halldor Laxness International Literary Prize a kokarinta na kawo sauyi a rubuta littafi.

    *Gabas da Yamma ko'ina, muna tsaye ne a bakin gaba. Duniyar da yanzu ba ita ba ce, maimakon kokarin komawa yadda take a da, za mu iya hada duniya mai kyau a yanzu da ba za a bar kowa a baya ba.

  • Anisa Shaheed

    Afghanistan Yar jarida

    Anisa Shaheed tana cikin fitattun 'yan jarida da ake ji da su, inda take kawo rahotani kan cin zarafin dan Adam da siyasa da rashawa. Ta yi aiki da talabijin din TOLO, wanda ke daya daga cikin manyan talabiji a kasar, kuma ta kasance tana aiko rahoto daga inda lamarin ke faruwa.

    An sha yi wa Shaheed barazanar kisa kai tsaye saboda kasancewarta 'yar jarida, wanda dan dole ta gudu ta bar kasar bayan Taliban sun kwace kasar a 15 ga Agusta. A shekarar 2020, kungiyar masu kawo rahoto suka karrama ta bisa karfin zuciyarta wajen kawo rahotanni a lokacin annobar covid-19.

    A 2021, ana karramata da kyautar 'Yar jaridar shekara, sannan kuma aka ba ta fuskar 'yancin bayyana ra'ayi na kungiyar Afghanistan Free Speech Hub Network.

    *A lokacin da damuwa da barin garuruwa suka yi kmari, inda da burin ganin zaman lafiya ya dawo Afghanistan. Ina da burin ganin mata da 'yan mata suna murmushi, sannan inda burin in dawo kasata, da gidana da kuma aikina.

  • Mina Smallman

    Birtaniya Malama

    Ita ce mace ta farko da ta kai matsayin babbar malamar coci a Cocin Ingila daga cikin bakaken fata a shekarar 2013. Yanzu ta yi ritaya daga malamtar coci da makaranta, amma Mina Smallman tana cigaba da fafutikar tsabtace titunan Birtaniya da kokarin kawo gyara a aikin dan sanda.

    Wani mai shekara 19 ne ya kashe mata 'ya'ya mata biyu a shekarar 2020: Nicole Smallman da Bibaa Henry a wajen shakatawa na London Park. Smallman ta caccaki yadda 'yan sanda suka gudanar da binciken kisan, sannan ta yi zargin watakila an kashe mata yaran ne saboda bambancin wariyar launin fata.

    Ta ce ta yafe wa wanda ya kashe mata yaran: "Idan muka cigaba da rike kiyayyar wani, ba shi kadai ba ne, har da mu ma muna cikin kunci domin tunaninka zai kasance cikin tunanin ramuwa. Ban yarda in ba shi wannan muhimmancin ba."

    *A matsayina ta malamar makaranta kuma malamar coci, na sadaukar da rayuwata wajen taimakawa yara da mutane suka raina. Ina shawartarku da ku tashi ku yi magana idan kuka ji an nuna wariyar launin fata. Za mu iya kawo canji.

  • Barbara Smolinska

    Poland Shugabar Reborn Sugar Babies

    Yar tsana da aka hada domin taimakon mata a lokacin da suke jinyar zubewar ciki ko mutuwar jariri, sannan a wasu kuma tana taimaka musu wajen yaki da matsalar damuwa da rashin haihuwa. Barbara ce ta zana 'yar tsanar da take zama kamar jaririya da ake amfani da ita a wajen jinyar marasa lafiya.

    A da mawakiya ce, amma ta taimaka wajen koyar da mata hada kayan kwalliya kuma ita ce ta assasa kamfanin Reborn Sugar Babies. An yi amfani da 'yar tsananta a fina-finai da asibitocin karbar haihuwa da makarantun kiwon lafiya.

    Smolinska tana matukar son zane-zanenta sannan tana da yakinin za su taimaka wajen inganta lafiyar kwakwalwar mata.

    *Zan so mutane su kara tausayin juna, su kara amincewa da junansu a abubuwan da suka samu sabani kamar yadda muka kirkiri 'yar tsana domin taimakon mata.

  • Ein Soe May

    Myanmar Mai fafutikar dimokuradiyya

    Bayan sojoji sun kwace mulkin kasar Myanmar, sun kama Ein Soe May (Ba asalin sunanta ba ne) inda ta yi wata shida a kulle kafin aka sako ta bayan yarjejeniyar sulhu da aka yi na kwanan nan. An tsare ta ne a wani kurkukun sojoji da ke yankin Insein da ya yi fice da azaba, sannan ta bayyana cewa ta matukar shan wahala a wwajen, inda ta yi zarghin cewa an mata azaba na jiki da na kwakwalwa.

    Tun tana daliba, matashiyar 'yar fafutikar take shiga fafutika da dama a matakan unguwanni. Bayan sojoji sun kwace mulki a 1 ga Fabrailu, sai Soe May ta shiga wata fafutika ganin karshen mulkin soji ciki har da zanga-zangar "pots and pans" na Fabrailu da ta "silenve strike" na watan Maris.

    Tun da aka sako ta, ta cigaba da fafutikarta.

    *Idan har za a dawo da duniyar yadda take a baya, to za mu so a gama yaƙar annobar nan sannan a samar da zaman lafiya. Muna fata za a fatattaki duk masu mulkin kama-karya na duniya sannan a samar da dimokuradiyya mai inganci.

  • Piper Stege Nelson

    Amurka Jami'ar Hulda da Jama'a a kamfanin The Safe Alliance

    A kamfanin The Safe Allianve na Austin da ke Jihar Texas, Piper Stege Nelson tana aiki ne tare da mutanen gari domin yaki da cin zarafin yara kanana da cin zarafin mata da wahalar da yara a gidaje da sauransu.

    Kungiyar tana ba yara kanana da aka yi wa fyade wadanda ba za su iya samun damar zubar da cikin ba shawara domin sabon dokar jihar ta hana zubar da ciki da bai wuce mako shida ba.

    Stege Nelson ta sadaunar da rayuwarta ne kan kare hakkin mata da 'yan mata. Ta yi aiki a gidauniyar Let Girls Learn na Michele Obama da kuma kwamitin siyasa na Annie's List da ke kokarin samar da nasarar mata a siyasa.

    *Annobar covid-19 ta rigata canja yanayin walwalar duniya-yanzu mutane ba sa jin nauyin fitowa fili su bayyana ra'ayinsu. Kalubalen a yanzu shi ne yadda za a ilimantar da mutane manya da yara muhimmancin sanin 'yancin jiki da na tunani.

  • Fatima Sultani

    Afghanistan Ma hawan duwatsu

    Bayan ta fara hawan duwatsu a matsayin abin da take sha'awa a shekarar 2019, Fatima Sultani sai ta fara jan ra'ayin matan Afghanistan domin su shiga harkar.

    Ta kafa tarihi tana shekara 18 inda ta hau dutsen Noshakh mai tsawon mita 7,492 a dutsen Hindu Kush, wanda shi ne mafi tsawo a Afghanistan, inda ta zama mace mafi karancin shekaru da ta ta hau dutsen. Tana cikin kungiyar 'yan Afghanistan 9 masu wasan hawa dutse, ciki har da mata uku.

    Mai matukar sha'awar harkokin wasanni, Sultani tana cikin tawagar 'yan wasan kasar na dambe da wasan taekwando da jiu jitsu na tsawon shekara bakwai da suka gabata.

    *Matan Afghanistan sun yi fafutikar kwato hakkinsu na shekara 20. Sun yi gwagwarma, kuma sun yi fice. Ina fata za su cigaba da haskakawa a ciki da wajen kasar ba tare da tsangwama ba.

  • Adelaide Lala Tam

    Mai zana abincin zamani

    Mai zane ce kuma mai zane-zanen abinci wanda ke amfani da aikinta wajen nuna irin rayuwar mutane, musamman a yanayin alakar mutane da abinci a yanzu.

    Adelaide Lala Tam, haifaffiyar China ce, kafin daga baya ta koma Hong Kong da zama baki daya, sannan yanzu take zama kuma take aiki a Netherland. Zane-zanenta na bayar da cikakken bayani kan sana'anta abinci tare da kira ga mutane da rika lura da abin da suke ci.

    A shekarar 2018, ta lashe gasar Future Food Design na mutane da na alkalai baki daya da bayan ta bayyana fasaharta na yanka shanu na zamanance. Tana cikin mutanen da suka shiga cikin 2021's '50 Next' wanda ke dauke da mutanen da suka kawo sauyi a yanayin abinci.

    *Duniyar ta canja sosai a bana, yanzu so nake duniyar nan a samu masu tausayi sosai wajen yanayin abin da muke ci.

  • Sister Ann Rose Nu Tawng

    Myanmar Ma'aikaciyar majami'a

    Mai hidimar coci ce, wadda ta kara fice lokacin da tsuguna a gaban 'yan sanda tana rokonsu domin ta tseratar da masu zanga-zangar ƙin amincewa da ƙwace mulkin da sojoji suka yi a Myanmay da suka samu mafaka a cocinta.

    Hotonta a tsugune ta daga hannayenta sama tana rokon 'yan sanda ya yadu sosai a kafafen sadarwa a watan Maris na shekarar 2021, wanda ya jawo mata yabo sosai.

    Sister Ann Rose Nu ta sha yin magana a bayyane domin kare fararen hula masu zanga-zanga, musamman kananan yara. Ma'aikaciyar unguzoma ce, sannan ta kwashe sama da shekara 20 tana yi wa coci hidima, sannan ba da dadewa ba ta yi aikin kula da masu cutar Covid a Jihar Kachin na Myanmar.

    *Ni ganau ce na abin ban haushin da ya faru a Myanmar. Idan da ina da hali, da na saki duk wadanda aka kulle a fursuna ba tare da laifi ba, sannan zan daidaita mutane ba tare da nuna bambanci ba.

  • Emma Theofelus

    Namibia Yar siyasa

    Ta kasance mace ta farko minista mai karamar shekaru a Afirka bayan ta zama minista tana da shekara 23 a bara. Emma Inamutila Theofelus Karamar Minstar Yada Labarai da Sadarwa ce, wadda aka ba alhakin hulda da jama'a game da annobar covid-19 a kasar.

    Kafin nan, ta kasance matashiyar 'yar gwargwamarya da take fafutikar samun daidaitun jinsi, hakkin yara da cigaban al'umma, kuma shugabar Majalisar Wakilai ta yara na birnin Windhoek da aka haife ta.

    Theofelus ta yi digiri a Jami'ar Namibia da difloma a Jami'ar Afirka ta Kudu inda ta karanci African feminisnm and gender studies.

    *Za a iya gyara duniyar nan ta dawo yadda take a da ta hanyar aiki ba magana ba. Akwai bukatar a fara kaddamar da tsare-tsaren da aka yi a shekarun baya. Babu lokacin jira, kai har mun ma bar lokaci ya wuce.

  • Sara Wahedi

    Afghanistan Shugabanr Start-up Ehtesab

    Ita ce ta kirkiri dandalin kasuwancin zamani na Start-uo Ehtesab wanda aikinsa na farko shi ne samar da manhajar samar da tsaro da ankarar da mutanen Kabul. Manhajar ta yi amfani matuka wajen sanar da mutanen Afghanistan halin da suke ciki ta hanyar bayar da sahihan bayani kan harin bama-bamai da hare-hare a gidaje.

    A 2020, Wara Wahedi take da burin kaddamar da taron kananan kasuwanci, wanda zai ba mutanen kauyuka damar samun damarmakin.

    Yar kasuwar zamanin tana cikin 'Shugabannin Gobe' na Mujallar Time na 2021, kuma yanzu haka tana karatu a Jami'ar Columbia, inda take karanta Human Rights and Data Science.

    *Lallai Afghanistan za ta dawo da martabarta ce da hadin kai wajen neman zabe mai inganci da kuma hukumar da za ta sake gina mana kasarmu. Idan har muna so mu kai ga hakan, dole mu dage wajen tabbatar da ilimin yara mata da maza da lafiyarsu sun zama wajibi.

  • Vera Wang

    Mai kwalliya Mai kwalliya

    Fitacciyar telar kayan amare ce wadda ta kasance a sana'ar tun shekarun 1970s. Vera ta fadada kasuwancinta inda ta hada da turare da wallafa littafai da ƙayata gida da sauransu.

    A birnin New York aka haife ta, amma iyayenta 'yan China ne. Ta kasance babbar editar kwalliya a mujallar Ralph Lauren. Ta yi wasanni da ake yi sanya da siket tana karama sosai.

    Mamba ce a Kungiyar Council of Fashion Designers of America, kungiyar da ta ba ta kambun mai kwalliyar shekara a shekarar 2005.

    *Dukanmu za mu iya fuskantar wani abu. Yanzu ne lokacin da ya kamata mu hada karfi da karfe domin cetar duniyarmu baki daya.

  • Nanfu Wang

    China Mai shirya fina-finai

    Yar asalin wani kauye ne a China, amma fitacciyar mai shirya fina-finai da yanzu haka take zaune a Amurka.

    Fim dinta na farko shi ne Hooligan Sparrow a shekarar 2016 wanda aka sa shi a cikin jerin fina-finan "best documentary feature" na karramar Academy Award. Ta bayar da umarni fim din One Child Nation a shekarar 2019 da kuma In The Same Breatj a shekarar 2021 wanda ya duba yadda Gwamantin China da Amurka suka fuskanci annobar covid-19.

    Wang ta taso ne cikin talauci, amma ta yi karatu har ta samu digiri na biyu sau uku daga Shangai da Ohio da New York. Ta samu tallafin MacArthur genius na 2020 saboda aikinta na samar da binciken gudunmuwar masu mulkin kama-karya wajen habaka cin hanci da rashawa.

    *Da alama duniyar ta kosa ta dawo cikin aminci kamar yadda take a da, amma abubuwan da a da muke ganin kamar daidai ne su ne jefa mu cikin wannan matsalar.

  • Roshanak Wardak

    Afghanistan Likitar karbar haihuwa

    Dokta Roshanak Wardak tsohuwar 'yar majalisa ce, kuma kwararriyar likitar karbar haihuwa da ta kwashe sama da shekara 25 tana kula da mata har a lokacin mulkin Taliban na farko, inda ta kasance mace likita daya ta; a yankinta na Maidan Wardak.

    Bayan mulkin Taliban ya fadi a 2001, sai ta zama 'yar majalisa. Yankinta ya kasance a karkashin Taliban na tsawon shekara 15, sannan kamar sauran kauyuka, sun sha fama da yake-yake tsakanin sojojin Nato da Taliban.

    Ta shaida wa BBC cewa kwace mulkin da Taliban suka yi da daina yakin ya zo kamar 'mafarki'. 'Na dade ina jiran ranar da za a cira masu rashawar nana daga mulki,' inji ta. Amma kwanan nan tana ta kokarin ganin an bude makarantu, sannan alkawuran da Taliban suka karya ya sa ta fara yawan magana akan hakkin 'ya'ya mata na zuwa makaranta.

    *Burina shi ne Afghanistan ta bincika gwamnatin shekara 40 da suka gabata domin su yi bayanyin ayyukansu ka kasar.

  • Ming-Na Wen

    Macau Jarumar fim

    Muryar ta ce ta ja fim ɗin Fa Mula a shirin Mulan na 'yan tsana na shekarar 1998 da Mulan II a shekarar 2014. Ming-Na Wen ta fito a fina-finai fitattu na Amurka ciki har da American Medical Drama ER, da Inconceivable, wanda yake daya daga cikin fina-finan Amurkda da aka sa dan asalin Asia da ke Amurka a matsayin wanda ya ja shirin.

    A yanzu haka ita ce ta fito a matsayin Fennes Shand a shirin Disney+ mai dogon zango, sannan za ta fito a fim din The Book of Boba Fett mai dogon zango shi ma. A shekarar 2019, Minga-Na ta lashe kyautar 'Disney Legend."

    Ta karbi kambum star a taron baje kolin Hollywood na shekarar 2022, wato Hollyood Walk of Fame.

    *Mayar da duniya yadda take a baya ba shi ne abin nema ba. Me zai sa mu yi tunanin komawa baya? Ina tunanin cewa komai akwai dalilinsa. Kulluma sabuwar rana ce, don haka mu yi rayuwar cikin godiyar Allah kawai.

  • Rebel Wilson

    Austreliya Jaruma, marubuciya kuma forodusa

    Babbar jaruma ce a masana'antar Hollywood kuma marubuciya, furodusa sannan darakta, kuma lauya ce. Ta fara shirin fim ne a Sydney stage, inda takan tsara labarinta da kanta, sannan ta yi fice a shirin fim din barkwanci na Sydney kafin ta koma Amurka a shekarar 2010.

    A fim dinta na farko a Hollywood, ta fara ne da shirin barkwanci na mata-zalla na Bridesmaids. Tana kuma cikin shirin Jojo Rabbit da ya lashe kambun Osca, amma an fi saninta da Fat Amy a fim din da ya yi fice a sinimomi na waka mai suna Pitce Perfect.

    A shekarar 2022, Wilson za ta bada umarnin fim a karon farko.

    *Fahimtar juna da girmama juna ya kamata a ba su muhimmanci sosai a duk bangaren rayuwa.

  • Benefsha Yaqoobi

    Afghanistan Mai fafutikar kare hakkin nakasassu

    Yaqoobi da mijinta dukansu makafi ne, inda suke assasa Kungiyar Rahyab domin tallafawa karatun makafi da gyara rayuwarsu a Afghanistan. Ta kuma yi aiki a matsayin kwamishina a Hukumar Kare Hakkin dan Adam mai zaman kanta, inda ta mayar da hankalinta kan ilimantar da yara makafi.

    Bayan Taliban sun kwace kasar, dole ta sa ta bar kasar, amma ta cigaba da bayyana ra'ayinta akan hakkin nakasassu, wadanda take tsoron Taliban za su rika tauye ma hakki.

    Nuna wariya babbar matsala ce a Afghanistan, kasar da take cikin kasashe masu yawan nakasassu, wanda bai rasa nasaba da gomman shekarun da aka yi ana yaki.

    *Idan har akwai nasara, to lallai bai wuce in kasata ta samar da 'yancin da ake bukata ba, tare da sanya dukanmu 'yan kasa wajen cigabanta.

  • Malala Yousafzai

    Pakistan Wacce ta ƙiƙiri Gidauniyar Malala

    Mafi ƙarancin shekarun da ta taɓa karɓar zaman lafiya ta Nobel, Malala Yousafzai ƴar fafutukar ganin yara mata sun yi ilimi ce a Pakistan kuma Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta Zaman Lafiya. Tun tana ƴar shekara 11 take magana kan ƴancin yara mata kan ilimi.

    Malala ta fara gwagwarmayarta ne ta hanyar rubuce-rubuce wa BBC kan yadda rayuwa take a ƙarƙashin Taliban a Pakistan da kuma haramcin da suka sanya na hana yara mata zuwa makaranta. A watan Oktoban 2012, wani ɗan bindiga ya tafi nemanta a motar bas ya kuma harbe ta a kai.

    Bayan da ta warke ne, sai ta ci gaba da aikinta na ƙirƙiriar Gidauniyar Malala, inda take gina muradun samar da yanayin da kowace ƴa mace za ta iya koyo da kuma yin jagoranci ba tare da tsoro ba.

    *Daruruwan miliyoyin ƴan mata a yau ba sa zuwa makaranta. Ina so na ga duniyar da kowace yarinya ta kai 12 tare da samun ingantaccen ilimi kuma cikin tsaro. Inda dukkan ƴan mata za su iya koyo tare da shugabanci.

  • Yuma

    Turkmenistan Mai kula da masu matsalar kwakwalwa

    Dole aka tursasa ta barin Rasha bayan cece-kucen da ya biyo bayan tallan da ta fito a wani babban shago da ya nuna 'yan gidansu a wani bikin 'yan luwadi. Ita mai kula da ciwon damuwa ce kuma mai fafutikar kare hakkin 'yan kungiyar madigo da luwadi. Yanzu haka tana zaune ne a Spain.

    Yuma (wadda ta bukaci a boye sunan mahaifinta) ta fara fafutika ne bayan kasar Rasha ta yi dokar hana "farfagandar 'yan luwadi" a shekarar 2013, inda kasar ta hana yada duk wani abu na saduwa idan na mace da namiji ba ga kananan yara.

    Tana bayar da shawara ga 'yan madigo 'yan Chechenya da suka ce 'yan sandan kasar Rasha sun azabtar da su a tsakanin 2017 zuwa 2018. Tana kuma goyon bayan tarukan kungiyar 'yan madigo a Rasha.

    *Yadda duniyar nan ta shiga kullen dole ya sa ya kamata a yanzu mutane su gane muhimmancin son juna. Yana da kyau mu duba abubuwan da muke yi a yanzu da kuma abubuwan da za mu yi domin ga wadanda muke so.

  • Zala Zazai

    Afghanistan Yar sanda

    Yar sanda ta farko da ta kai matsayin Mataimakiyar Babban Mai Bincike a 'yan sanda yankin Khost, yankin da ke matukar fama da matsalar harkokin 'yan bindiga. 2nd Laftanar Zala Zazai tana cikin 'yan sanda mata 4,000 da kasar ta horar a Kwalejin 'Yan sanda na Turkiyya.

    A lokacin da take gudanar da ayyukanta, ta sha fama da matsalolin tsangwama daga abokan aikinta maza, da kuma neman rayuwarta da 'yan bindiga suka rika yi.

    Bayan Taliban ta ƙwace kasar a 2021, dole Zazai ta bar Afghanistan. Tun lokacin ne ta cigaba da bayyana ra'ayinta game da halin da sauran 'yan sanda da dole ta sa suke boye a kasar.

    *Burina shi ne in sake sanya kakina a nan gaba, in cigaba da kalubalantar al'adar nan ta danne mata. Ina so in sake yi wa matan Afghanistan aiki a kauyuka inda mata ba su damar yin aiki.