Isra'ila ta rusa dubban gidaje a Gaza tun bayan ficewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas a watan Maris, kuma a makonnin da suka gabata ta sanya alamar rusau a garuruwa da ƙauyuka da dama waɗanda a baya suke ɗauke da dubban mutane.
Hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna yadda aka ɓarnata wurare da dama kuma sojojin Isra'ila sun sanya alamar ikirarin cewa wuraren na "ƙarƙashin aikin sojinsu".
Mafi yawan gidajen an sanya alamar rusau, kuma da dama daga ciki sun riga sun lalace, amma akwai wasu da suka rage a tsaye.
Hotunan da aka tantance sun nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe, bayan sojojin Isra'ila sun kai hare-hare a manyan gine-gine da makarantu da sauran ababen more rayuwa.
Masana shari'a da dama sun bayyana wa BBC cewa akwai alamun Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi idan aka yi la'akari da yarjejeniyar Geneva, wadda a ciki aka haramta wa ƙasar da ke mamaya ɓarnata ababen more rayuwa.
Kakakin rundunar tsaron Isra'ila ya ce suna aiki tare da la'akari da dokokin duniya, inda ya ce Hamas na ɓoye "makamai" a cikin fararen hula, sannan suna "rusa gine-gine ne kawai idan ta zama dole."
An gani a zahiri yadda Rafah ya lalace a kusa da bakin iyakar Masar
A ƴan makonnin da suka wuce, sojojin Isra'ila da ƴan kwangilar rusau sun sanya alamar rusau a gidaje da dama
Nazarin masa irin su Corey Scher da Jamon Van Den Hoek ya nuna cewa ɓarnar da aka yi a Gaza tun daga watan Afrilu ya yi muni a yankin.
Akwai manyan motocin katafila jigbe a yankunan
A watan Yuli, ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana tsare-tsarensu na kafa abin da ya kira "birnin aikin ceto" a Rafah, inda za a fara da ajiye Falasɗinawa 600,000 a sansanin.
Yunƙurin na shan suka sosai. Tsohon firaministan ƙasar, Ehud Olmert ya shaida wa BBC cewa tsarin zai yi kama "kafa sansanin ajiye waɗanda ba a so."
Isra'ila ta yi ikirarin cewa sojojinta "suna aikin soji" ne a wurare da dama a zirin Gaza
BBC Verify ta tabbatar footage of infrastructure being demolished in 40 locations since the ceasefire ended in March
Faifan bidiyo na nuna makaranta - kamar haka makaranta a Tel al-Sultan - ana rushe ta, tare da wasu gine-gine al'umma da na gwamnati.
Tel al-Sultan na cikin biranen da suka fi yawan mutane a yankin Rafah. Akwai tarin mutane kuma a garin ne asibitin kula da yara da marayu da yaran da aka tsinta suke rayuwa.
Hotunan tauraron ɗan'adam da ke nuna yadda hare-haren sojojin Isra'ila ya ɓarnata yankin duk da akwai gomman gine-gine da suka tsira.
Zuwa ranar 13 ga Yuli, hare-haren sun riga sun munana, inda ake samun manyan gine-gine sun rufta baki ɗaya. Asibitin na cikin ƴan tsirarun gine-ginen da suka rage.||
Haka kuma an sanya alamar rusau a gine-ginen da ke kusa da garin Saudi - garin da ke ɗauke da babban masallaci da makarantu da dama.
Wani faifan bidiyo da aka tabbatar ya nuna wata tanka na tafiya a titin Rafah wasu ma'aikata kuma suna diga.
Haka kuma Isra'ila ta yi rusau a wasu sassan zirin waɗanda suka tsira daga hare-haren farko.
Birnin Khuza'a da ya yi fice da noma, wanda ke da da nisan kilomita 1.5 (mil 0.9) daga bakin iyakar Isra'ila.
Kafin fara yaƙin, birnin na da mutum 11,000, kuma yana da ƙasar noma mai kyau da ake noma tumatir da fulawa.
Tauraron ɗan'adam na watan Mayu da ke nuna gine-gine da suka rage a birnin a tsaye.
A tsakiyan watan Yuni ne sojojin Isra'ila suka fi kai hare-hare a Khuza'a
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta rusa gine-gine 1,200 a Khuza'a, waɗanda ta yi zargin kadarorin "ƴanta'adda" ne da Hamas ke amfani da su.
An samu labarai irin haka a birnin Abasan al-Kabira, inda kusan mutum 27,000 ke rayuwa kafin yaƙin. Hotunan da aka ɗauka a 31 ga Mayu da 8 ga watan Yulin sun nuna yadda aka ɗaiɗaita yankin a cikin kwana 38.
Isra'ila ta ƙirƙiri "sansanonin tsaro" a tsakanin wasu yankunan Gaza, kuma ta lalata gine-gine da dama a tsakanin su. Wurin da ta kai farmaki na kusa-kusan nan shi ne gab da gabashin Khan Younis, ciki har da Khuza'a da Abasan al-Kabira.
Haka kuma tun farkon yaƙin, masana suke hasashen Isra'ila na yunƙurin kafa "cibiyoyin tudun mun tsira" ta hanyar rusa gine-gine da ke gab da bakin iyakarta.
A Qizan Abu Rashwan - yankin da ya yi fice da noma mai nisan kusan kilomita 7 daga bakin iyakar Isra'ila - kusan kowane gini da ke tsaye an rusa shi daga ranar 17 ga Mayu.
Sashen BBC Verify ya gabatar da sakamakon bincikensa ga IDF ciki har da wuraren da ta rusa, inda aka buƙaci ta yi bayani, amma ba ta yi ba.
"Kamar yadda aka sani ne, Hamas da sauran ƙungiyoyin ƴanta'adda na ɓoye makamai a cikin fararen hula," in ji kakakin IDF. Sannan ya ƙara da cewa IDF na "ganowa tare da ɓarnata kadarorin ƴanta'adda da suke cikin gine-ginen ne."
Lauyoyin kare haƙƙin ɗan'adam da dama da BBC Verify ta zanta da su sun ce akwai alamun Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi.
Eitan Diamond - wani babban lauya da ke aiki a cibiyar agaji ta Diakonia International Humanitarian Law Centre da ke Jerusalem - ya ce akwai ƴar hujja da ta kafe da shi a cikin yarjejeniyar Geneva ta huɗu.
"Dokokin duniya sun haramta waɗannan mamayar da ɓarnata kadarorin fararen hula a lokacin yaƙi, sai dai idan ya matuƙar zama dole," in ji Mr Diamond said.
"Amma ɓarnata kadarori saboda kawai zargin yiwuwar za a yi amfani da su a gaba ba ya cikin uzurin da aka tsara a yarjejeniyar."
Farfesa Janina Dill, darakta a cibiyar shari'a da yaƙi ta Oxford Institute for Ethics, Law & Armed Conflict ta ce ƙasar da ta yi mamayar dole ta killace wani yankin domin kare wasu mutane - wadda ta ce ba zai yiwu a yi amfani da ƙarfin soji ba."
Amma wasu masanan sun kare rundunar IDF.
Gine-gine da dama da IDF ta rusa sun zama kufai, "in ji Farfesa Eitan Shamir, darakta a cibiyar BESA Center For Strategic Studies da ke Isra'ila kuma tsohon jami'i a ma'aikatar tsare-tsare. Ya bayyana wa BBC Verify cewa gine-gine sun barazana ga masu komawa garuruwan su saboda za su iya rushewa a kowane lokaci".
Haka kuma Farfesa Shamir ya ce akwai rashin tsari.
"Wuraren sun zama na yaƙi," in ji shi. "Ko da ma IDF ta mamaye wurin, da zarar Isra'ila ta janye, mayaƙan suna komawa su dasa bama-bamai ko su ɓoye a ciki."
Babu alamar janyewa a yunƙurin na rusau. Kafofin watsa labarai na Isra'ila sun ce IDF ta ɗauko manyan katafila da ake kira D9 daga Amurka.
Kuma sashen BBC na BBC Verify ya gano gomman tallata guraban aiki da aka watsa a zaurukan Facebook na ƴan Isra'ila da ake neman ma'aikata da za su yi aikin rusau a Gaza, waɗanda aka riƙa yaɗawa tun a watan Mayu.
Wasu rubuce-rubucen sun bayyana wuraren da za a yi aikin a Gaza kamar "yankin Philadelphi" da "yankin Morag" - duk a ƙarƙarshin IDF.
Da BBC Verify ya tuntuɓi wani ɗan kwangila, sai ya ce, "ka je (wasu maganganu) da kai da Gaza."
Wani masani - Adil Haque na tsangayar shari'a ta Rutgers - ya yi hasashen rushe-rushen IDF ba za su rasa nasaba ba da yunƙurin kafa "yankin soji" da za ta "mamaye daga baya" ba.
Wasu masana kuma sun ce rusau ɗin share fage ne domin kafa "cibiyar agaji" a Rafah - Shugaban cibiyar nazarin tsaro da tsare-tsare ta Institute for Strategy and Security da ke Jerusalem - ya ce wataƙila suna so ne su tursasa wa Falasɗina barin zirin baki ɗaya.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya taɓa bayyana wa a baya a wani taro da ƴan majalisa cikin sirri cewa IDF za ta rusa gine-gine ne domin ya zama Falasɗina ba su da wurin komawa".
Amma a wajen ƴan Gaza, matsala ce babb.
Moataz Yousef Ahmed Al-Absi from Tel al-Sultan ya ce an mayar da gidansa kufai.
"na koma gidan ne kimanin shekara biyu kafin a fara yaƙin, inda nake tsammanin zan cigaba da rayuwa. Amma yanzu ya zama kufai," in ji shi.
"Na rasa komai, yanzu ban san yadda zan yi ba."
@YinonMagal/X, @Philipp27960841/X and Abu Ali Express/Telegram
Mohamed Shalaby