Makomar ruwa a Afirka:Kuna da fargabar ƙarewar ruwa nan gaba a birni da ƙasarku?

Yayin da al'ummar duniya ke ƙaruwa, buƙatar ruwa mai kyau da tsafta kuma mai sauki na ƙaruwa ita ma, abin da ke sa matsi da raguwar ruwan da ake da shi. Wannan shi ne ake kira ''matsin ruwa''.

Zuwa shekara ta 2025, rabin al'ummar duniya za su kasance suna rayuwa a yankunan da ke fama da matsalar matsin ruwa, kmar yada Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.

Ba za a iya ci gaba da samar da ruwa mai daɗi ba daidai da buƙatar duniya da ke karuwa ba. Ba a samun ruwa daidai-wa-daida a fadin duniya, kuma zai kasance da matukar wuya a riƙa samo ruwa mai daɗi kuma zai yi tsada a rika safararsa.

Ƙaruwar jama'a da bunkasar birane da sauyin yanayi na daga cikin abubuwan da ke haddasa ƙarancin, ta hanyar rashin ruwan ko kuma gurɓata hanyoyin da ake da su na samun ruwan.

Bari mu mayar da hankali a kan Afirka

Zuwa shekara 30 nan gaba an yi hasashen yawan al'ummar Afirka zai ninka biyu zuwa biliyan 2 da rabi in ji Ƙungiyar Hadin kan Tattalin Arziki da Ci-gaba (OECD).

Tuni daman rabin al'ummar Afirka na zaune ne a birane, kuma sama da rabinsu suna zaune ne a unguwanni na talakawa.

Ƙwararru sun yi gargagaɗin cewa matukar ba a ɗauki mataki ba mutane sama da miliyan ɗari daya a birane za su fuskanci matsanancin ƙarancin ruwa.

Yadda rabe-raben yanayi yake a wurare masu ƙarancin ruwa a duniya

Taswirar da ke nuna rabe-raben yanayi na wuraren da ake da babu ruwa sosai

Bayani daga: Rabe-raben yanayi na ƙungiyar Köppen-Geiger

Afirka ce nahiya mafi ƙarancin ruwa a duniya. Kusan biyu bisa uku na sararinta ko dai mai karancin ruwa ne ko kusa da haka.

Rabe-raben yanayi na yankuna masu ƙarancin ruwa

Taswirar rabe-raben yanayin yankin da babu ruwa sosai.

Bayani daga: Rabe-raben yanayi na ƙungiyar Köppen-Geiger

Ɗaya daga cikin mutum uku a yankin Afirka kudu da hamadar Sahara na rayuwa ne a wurin da ake fama da ƙarancin ruwa.

Yanayin tsananta amfani da ruwa a kowa ce ƙasa ta Afirka (2019)

Taswirar da ke nuna yadda ake da tsananin amfani da ruwa a kasashen Afirka (2019)

Daga: OECD 2021

Eritrea da Botswana na daga cikin ƙasashen Afirka da dama da ke fama da matsalar ruwa.

Manyan matsalolin wadatar ruwa

Sauyin yanayi na haddasa yanayi da ba za a iya hasashe ba da ya hada da fari da ambaliya. Kyawun ruwan da ake samu daga ƙarkashin ƙasa ya ragu a yankuna da yawa

Ana asarar miliyoyin ranaku na aiki da nazari a kowa ce sheakara saboda rashin lafiya wadda rashin ruwa ko rashin kyawunsa ke haddasawa.

Samun ruwan famfo mai kyau a birane

A cikin shekara ashirin da ta gabata an samu ci gaba sosai wajen samar da ruwan famfo mai sauki da tsafta a faɗin Afirka

Amma duk da haka har yanzu akwai manyan matsaloli

Ruwa mai kyau shi ne wanda ake samu cikin sauƙi wanda kuma bai gurɓata ba. Kashin yawan mutanen birni da ke samun ruwa mai kyau a Afirka ya kama daga kashi 9 cikin ɗari a Laberiya zuwa kashi 99 cikin ɗari a Afirka ta Kudu, kamar yadda Hukumar lafiya ta Duniya, WHO da Asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF suka bayyana.

SDG 6 : Ƙalublen samar da ruwa mai kyau da tsafta ga kowa

A 2015 Babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙuduri aniyar tabbatar da samar da ruwa da tsafta ga kowa a matsayin ɗaya daga cikin buruka17 masu ɗorewa na ci gaba (SDGs)

Ana kirn wannan SDG 6

Djibouti da Moroko da namibia da Masar na daga cikin ƙasashen da ka yi hasashen za su iya fuskantar tsananin ƙarancin ruwa

To amma kum dukkanin ƙasashen Afirka na fuskantar manyan ƙalubale wjen cimma burin na SDG 6

Wani nazari da aka yi a 2019 ya gano wasu ƙasashen Afirka na ƙoƙari, amma a rabinsu babu wani ci gaba.

Tsarin duba yanayin samun ruwa mai kyau da tsafta (SDG 6) a ƙasashen Afirka (2019)

Har yanzu akwai manyan ƙalubale
Yana ɗan ƙaruwa
Babu ci gaba
Ana kan hanya
Taswirar da ke nuna tsarin duba yanayin samun ruwa mai kyau da tsafta (SDG 6) a ƙasashen Afirka (2019)
Yanayi
Taswirar da ke nuna yanayin sa ido a kan samun ruwa mai kyau da tsafta (SDG 6) a kasashen Afirka (2019)
Matsayi

Matakan na mayar da hankali ne a kan ɓangarori uku: gyara ruwan da amfani da shi da kuma da kuma sake amfani da ruwan da aka riga aka yi amfani da shi; inganta ayyukan gona; da zuba jari a ayyukan injiniya da ake amfani da kankare da ƙarafuna, waɗanda suka dogara ga tsirrai da sauran halittu da muhallinsu.