Adegboyega Oyetola shi ne gwamnan Jihar Osun mai ci a yanzu.
Ɗan asalin Iragbiji na ƙaramar hukumar Boripe ne.
Yana da digiri a harkar inshora da kuma digiri na biyu daga Jami'ar Lagos.
Kafin ya zama gwamna a shekarar 2018, shi ne shugaban ma'aikata na Gwamna Rauf Aregbesola, wato mutumin da ya gada.
Sana'a: Ɗan kasuwa
Shekara: 62
A shekarar 2021 ya samu shaidar kammala karatun digiri a fannin shari'a kan manyan laifuka a Kwalejin Atlanta Metropolitan a Amurka.
Ya tsaya takarar sanatan Osun ta Yamma a 2017 a zaben cike gurbi bayan rasuwar ɗan uwansa Isiaka Adeleke.
Ya sake tsayawa takara ya fadi a zaben gwamna na 2018 na jihar Osun.
Dan asalin garin Ede ne.
Sana'a: Ƙwararren mai zanen gine-gine
Shekara: 58
An haife shi a Osogbo a 1964
Yana da digiri na farko da na biyu daga Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) a Ile-Ife.
Daga baya ya ƙara yin digiri na biyu har guda biyu a sha'anin gudanar da kasuwanci da a fannin safiyon ƙasa da fasahar zamani daga Jami'ar Ilorin da ta Ibadan.
Ya taɓa riƙe matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Shekara: 59
An haifi Akin Ogunbiyi a Ile-Ogbo, Jihar Osun.
Ya yi karatun digiri kan tsimi da tanadi a Jami'ar Obafemi Awolowo sannan ya yi digiri na biyu a Jami'ar Navarra da ke Barcelona a Spain.
Mamaba ne na Cibiyar Ƙwararru kan harkar inshora ta London.
Ya taba zama ɗaya daga cikin daraktocin Bankin Ayyukan Raya Ƙasa da na Kamfanin Mutual Benefits Assurance da sauran wasu kamfanonin.
Yusuf Sulaimon Lasun ɗan asalin ƙaramar hukumar Ilobu Irepodun ta jihar Osun ne.
Ya yi digiri na ɗaya da na biyu a kan injiniya a Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ibadan.
Shi ne kuma jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar AD na jihar a lokacin mulkin Cif Bisi Akande. An naɗa shi shugaban hukumar raya da cigaban babban birnin jihar Osun OSCTDA a 2014.
Sau biyu yana riƙe muƙamin ɗan majalisar wakilan tarayya,sannan ya yi mataimakin kakakin majalisa daga 2015 zuwa 2019.