Karin bayani Latsa nan don karin bayani

image
Akere Muna
Jam'iyyar FPD
Ranar haihuwa
August 18, 1952
Aiki
Lauya
Usuli
  • An haifi Akere Muna a ranar 18 ga watan Augustan 1952.Da ne a wajen tsohon Firai minista Salomon Tandeng Muna, kuma dan uwa a wajen dan takarar shugabancin kasa a zaben 2011 wato Bernard Muna, sannan kuma dan uwa a wajen ministar raya al'adu ta Kamaru Ama Muna, wadda ta rike mukami a tsakanin shekarun 2007 zuwa 2015.
  • Akere Muna, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ne ta Kamaru.Kuma ya rike mukamin shugaban kungiyar lauyoyi ta UPA.
  • A shekarar 2005, ya zamo shugaban kungiyar da ke yaki da cin hanci ta kasa da kasa. Yanzu haka yana neman takarar shugabancin kasar a 2018 inda zai yi gogayya da shugaba Paul Biya.
image
Garga Haman Adji
Dan takarar jam'iyyar ADD
Ranar haihuwa
27 ga watan Janairu, 1944
Aiki
Ma'aikacin gwamnati kuma ma rubuci
Usuli
  • Tsohon minista ne, kuma mamba ne a kungiyar musulmai ta kasar Kamaru. Ya fito ne daga yankin Arewacin kasar. An haifi Garga Haman Adji a ranar 27 ga watan Janairun 1944 a Maroua, babban birnin Diamare.
  • Ya yiwa kasa hidima tun yana da karancin shekaru. A shekarar 1981, shugaba Ahidjo ya nada shi a matsyin mataimakin sifeto na kasa. Ya rike wannan mukamin a lokacin mulkin shugaba Paul Biya na farko bayan Ahmadou Ahidjo ya yi murabus a ranar 4 ga watan Nuwambar 1982.
  • A ranar 6 ga watan Afrilun 1984, aka zarge shi da kitsa wa shugaba Paul Biya juyin mulki. An tsare shi a babban gidan yarin Yaounde domin gudanar da bincike, amma daga bisani aka sake shi bayan an wanke shi. Garga Haman Adji bai taba rike wani mukamin ofis ba.
  • Ya kirkiri jam'iyyarsa ta ADD a ranar 4 ga watan Yunin 1991, bayan an dawo da tsarin jam'iyyu masu yawa a Kamaru.Bai samu nasara ba a zabukan 2004 da 2011 na shugaban kasa da aka yi.
image
Maurice Kamto
Jam'iyyarta MRC
Tsohuwar minista ce
Aiki
Farfesa ce a Jami'a
Usuli
  • Maurice Kamto sanannen dan siyasa ne a Kamaru, babban kusa ne jam'iyyar adawar kasar. Maurice ya fito ne daga Baham da ke yammaci kasar.
  • A shekarar 1983, ya samu lambar girmamawa ta Dakta wanda tsangayar nazarin shari'a da Siyasa na jami'ar Yaounde ya bashi.
  • Maurice Kamto ya taba kasancewa lauyan Kamaru a gaban kotun ICJ. Sannan kuma mamba ne a hukumar da ke sasanta rikicin Najeriya da Kamaru a kan yankin Bakassi ta Majalisar Dinkin Duniya. Gudunmuwar da ya bayar a hukumar ita ake ganin ta taimaka gaya wajen nada shi a matsayin mataimakin minista da mukaddashin Firai minista da kuma Ministan Shari'a a Kamarun a shekarar 2004.
  • A watan Nuwambar 2011 ne, ya zabi ya yi murabus daga mukaminsa, sai ya shiga siyasa a shekarar da ta zagayo ta 2012 a jam'iyyar MRC.
image
Cabral Libii
Jam'iyyar Universe
Ranar haihuwa
29 ga watan Maris, 1980
Aiki
Dan Jarida ne
Usuli
  • Cabral Libii, an haife shi a ranar 29 ga watan Maris din 1980 a Ekoamaen, da ke tsakiyar Kamaru.Shi ne ma mafi kankantar shekaru a cikin jerin 'yan takarar shugabancin kasar.
  • Dan jarida ne, kuma kusa a kasar, Cabral Libii ya tsaya tsayin daka a kan sharhin da ya ke game da siyasa a kafafan yada labaran kasar Kamaru.
  • Ya yi aiki a jami'ar Yaounde ta 2 a shekarar 2005.A lokacin da ya ke dalibi, dalibai 'yan uwansa sun zarge shi da taimakawa mahukuntan jami'ar wajen dakatar da yajin aikin da ake yi a lokacin. Amma kuma ya musanta hakan.
  • Ana ganin kamar an turo Cabral Libii ya yi takara ne domin rarraba kawunan 'yan adawa.
image
Serge Espoir Matomba
Jam'iyyar PURS
Ranar haihuwa
30 ga watan Satumba 1979
Aiki
Dan kasuwa ne
Usuli
  • Serge Espoir Matomba, sakataren farko na jam'iyyar PURS. An haife shi a ranar 30 ga watan Satumbar 1979 a Douala
  • Ya kasance Kansila a wata mazaba a Douala tun daga 2013. Shi ne matashi na farko a kasar da ya kalubalanci gwamnatin Kamaru ta yanzu.
  • A 2008, aka kafa jam'iyyar '' Your Super Cameroon'', bayan Serge Espoir ya hadu da Daniel Proenca de Carvalho, wani tsohon minista a Portugal kuma shugaban kamfanin mai Multinational Galp Energie.
  • A 2008, ya dawo Kamaru inda ya ke duba yi wuwar kafa wata kungiya mai zaman kanta wadda a shekarar 2010 ta koma jam'iyyar siyasa mai suna PURS, inda aka zabe shi a matsayin sakataren jam'iyyar.
  • A babban taron jam'iyyar karo na biyu wanda aka kammala a ranar 10 ga watan Yunin 2017, an zabi Serge a matsayin wanda zai tsayawa jam'iyyar takarar shugabancin kasa a zaben 2018 da za a yi a cikin watan Oktoba.
image
Joshua Nambangi Osih
Jam'iyyar SDF
Opposion leader
Ranar haihuwa
9 ga watan Disamba 1968
Usuli
  • Shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar SDF, babbar jam'iyyar adawa a Kamaru, kuma shi ne dan takarar shugabancin jam'iyyar a zaben 2018. An haife shi a ranar 9 ga watan Disambar 1968. Mahaifnsa dan kasar Kamaru, mahaifiyarsa kuma 'yar kasar Switzerland.
  • Ya fara aikinsa ne a kamfanin jirgin sama na Luftahnsa a matsayin dillali, daga nan kuma sai ya koma Switzerland, kasar mahaifiyarsa inda ya yi aiki a kamfanin jirgin sama na Swissair da ke Geneva. Ya koma Kamaru a a 2000, inda ya bude kamfanoni biyu, wato African Travel Management da kuma Swiss Camport PLC.
  • Ya shiga jam'iyyar SDF a watan Maris din 1991. Joshua Osih ya kasance dan majalisar wakilai a Kamaru tun shekarar 2013, inda kuma ya rike mukamin mataimakin shugaban jam'iyyarsu.
  • A shekarar 2013, ya zamo dan kasar Kamaru na farko daga yankin masu amfani da harshen Ingilishi da ya wakilci Douala a majalisar wakilan Kamaru.
  • An tsayar da Joshua a matsayin dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar SDF a zaben 2018 da za a yi a Kamaru.
image
Adamou Ndam Njoya
Jam'iyyar DUC
Ranar haihuwa
8 ga watan Mayu, 1942
Aiki
Marubuci, malamin jami'a kuma tsohon minista.
Usuli
  • An haife shi a ranar 8 ga watan Mayun 1942, a Foumban na Kamaru.Adamou Ndam shi ne shugaban jam'iyyar UDC, wadda ta kasance babbar jam'iyyar adawar Kamaru a 1991.Ya taba zama dan takarar shugabancin kasar a 1992 da 2004 da kuma 2011.
  • Bayan kammala karatun firamare da na Sakandire a Kamaru, ya wuce kasar Faransa inda ya yi karatun digirin digirgir a can a bangaren bangaren siyasa.Ya dan taba aiki a ofishin jakadancin Faransa da ke London da kuma aiki a Geneva, kafin ya dawo Kamaru a 1969.
  • Ndam Njoya ya dan yi aiki a ma'aikatar harkokin wajen Kamaru daga tsakanin shekarar 1960 zuwa 1970, kafin daga bisani ya koma tsangayar nazarin shari'a a Yaounde.Yanzu ya yi ritaya.
  • A shekarar 1975, aka nada shi a matsayin mataimakin ministan harkokin wajen Kamaru. A watan Janairun 1982, Ahidjo ya kore shi daga aikinsa.Sai ya koma koyarwa, sannan kuma ya zama mamba a UNESCO.
  • A watan Disambar 1990, shugaba Paul Biya ya dawo da da jam'iyyun hamayya cikin kasar inda Ndam Njoya kuma ya fara tattara kan 'yan siyasa masu son kawo sauyi, hakan ya sa aka kama shi shi da wasu 'yan siyasar, amma kuma ba su jima ba aka sake su.
  • A watan Satumbar1991, ya sanar kafa jam'iyyar DUC.
image
Paul Biya
Jam'iyyar CPDM.
Ranar haihuwa
13 ga watan Fabrairun, 1933
Aiki
Shugaba mai barin gado
Usuli
  • An haife Paul Biya a ranar 13 ga watan Fabrairun 1933 a Mvomeka da ke Kudancin Kamaru. Dan siyasa ne a kasar, kuma ya rike mukamin Firaminsita daga 1975 zuwa 1982.
  • Ya fito daga kabilar Beti. A 1961 ya yi aurensa na fari inda ya auri Jeanne- Irene Biya wadda ta rasu a 1992. Sun haifi da daya tare da ita mai suna Franck Biya. Daga nan sai ya auri Chantal Pulcherie Vigouroux wadda suka dauko yara biyu suka mayr da su nasu daga wajen wasu 'yan uwansu. A aurensa na biyu sun haifi 'ya'ya biyu wato Paul karami da Anasthasia Brenda Eyenga.
  • Bayan ya kammala karatun sakandirensa a Yaounde sai ya wuce zuwa Paris inda ya yi karatun nazarin kimiyyar siyasa.
  • A 1962, aka nada shi a matsayin wakilin shugaban kasan kasa Ahmadou Ahidjo. A 1968, aka bashi mukamin minista. A ranar 30 ga watan Yunin 1975, shugaba Ahmadou Ahidjo ya ya yi murabus, sai ya nada shi a matsayin Firaminista.Ya zamo shugaban Jamhuriyar Kamaru a ranar 6 ga watan Nuwambar 1982.
  • A ranar 6 ga watan Aprilun 1984, ya tsallake wani yunkurin juyin mulkin da ake yi masa. An kama mutane d adama a wannan lokaci har an hukunta wasu.
  • A farkon shekarun 1990, wato lokacin saba dokokin da gwamnati ta kafa, an samu tashe- tashen hankula da rikici, hakan ya sa ya amince da samar da jam'iyyu masu yawa a kasar. A zaben farko da aka yi na jam'iyyu d ayawa ya lashe inda ya kayar da abokin hamayyarsa John Fru Ndi. Ya kuma lashe zabukan shugaban kasa a 1997 da 2004 da 2011.
image
Ndifor Afanwi Franklin
Jam'iyyar CNCM
Aiki
Fasto ne.
Usuli
  • Shekarun Ndifor Afanwi Franklin 39, kuma bai taba siyasa ba.
  • Faston ya ce ya yi amanna cewa siyasa ce babbar matsalar da kasar Kamaru ke fama da ita, don haka ya ce a shirye ya ke ya ceto kasar daga halin da ta shiga.
  • A ranar 28 ga watan Afrilun 2018 ne, Faston ya kafa jam'iyyarsa ta CNCM.
Yan takarar da za su fafata a zaben
image
Ranar haihuwa
Aiki
Usuli

Hakkin mallakar hotuna

Getty, Facebook, Twitter