Abubuwa nawa za ku tuna a shekarar 2018?
Ga kacici-kacici
Amsoshin na kasa

Wace waka ce Umar M Shariff ya fi so?
1. Mariya
2. Madubin Dubawa
3. Jirgin Soyayya
4. Jinin Jikina

Wace Daula ce a Najeriya Sayyidina Umar ya taba aika sako?
1. Daular Borno
2. Daular Sakwatto
3. Masarautar Kano
4. Masarautar Zazzau

Nawa aka sako daga ‘yan matan Dapchi da aka sace?
1. 107
2. 105
3. 106
4. 104

Wane dan siyasar Najeriya ne yace ya tuba da yin magudin zabe?
1. Sanata Dino Melaye
2. Honarabul Abdul-Aziz Namdaz
3. Sanata Ibrahim Mantu
4. Sanata Bukola Saraki

Wane gwamnan Najeriya ne ya zagi sanatocin jiharsa a bainar jama'a?
1. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
2. Gwamna Kashim Shettima
3. Gwamna Ayodele Fayose
4. Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa'i

Wace kasa ce ta fitar da Najeriya daga gasar cin kofin duniya ta 2018?
1. Argentina
2. Rasha
3. Senegal

Wace kungiyar kwallon kafa ce ta sayi gola mafi tsada a duniya?
1. Liverpool
2. Manchester United
3. Leicester City
4. Arsenal

Wane jigon Boko Haram aka kama a wannan watan?
1. Maje Kabir
2. Maje Yusuf
3. Maje Lawal
4. Maje Isa

Me yasa aka rufe filin jirgin sama na Abuja?
1. Saboda gyara
2. Saboda hatsari
3. Saboda ruwan sama
4. Saboda shugaban kasa

A ina aka gano gawar Janar Idris Alkali?
1. Du
2. Gushwet
3. Jos
4. Barikin Ladi

‘Yan mata nawa ‘yan boko haram suka sace a Nijar a wannan watan?
1. 13
2. 14
3. 15
4. 16

Me yasa ma'aikaciyar BBC ta kashe kanta?
1. An kore ta aiki
2. Mijinta ya mutu
3. Matsalar damuwa
4. Albashinta ya yi kadan
Amsoshi
amsa: Jirgin Soyayya
Umar ya ce duk a wakokin da ya yi, ya fi son wakar Jirgin Soyayya wacce aka yi a fim din Mansoor.amsa: Daular Borno
Daular Borno ta yi zamani da Sahabbai, kuma masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce daular ta kafu ne tun kafin zuwan Annabi SAW.amsa: 104
Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan matan sakandaren Dapchi 104 kungiyar Boko Haram ta sako.amsa: Sanata Ibrahim Mantu
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ya ce yana da hannu cikin magudin zabukan da aka yi a baya amma ya ce ya tuba daga aikata magudin zabe.amsa: Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa'i
Gwamna Nasir Ahmad el-Rufai ya zargi Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi da Sanata Danjuma Laah da hada baki domin hana majalisar dattawan Najeriya amincewa da bukatarsa ta cin bashi daga Bankin Duniya inda ya ce "wadannan dattijan [sanatocin Kaduna] banza ne... domin su makiyan jihar Kaduna ne, ba sa son ci gaban jihar."amsa: Rasha
Argentina ta cire Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya, inda Najeriyar ta samu maki uku,kuma matsayi na uku a rukunin D, abin da ya fitar da ita daga Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Rashaamsa: Liverpool
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sayi golan Roma, Allison a kan fam miliyan 66.8 (Yuro miliyan 72.5), abin da ya sa ya zama golan da ya fi tsada a duniya.amsa: Maje Lawal
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta cafke Maje Lawan a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Banki a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.amsa: Saboda gyara
Hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) ta ce an bude filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan rufe shi da aka yi na wasu sa'o'i sakamakon wani hatsari.amsa: Gushwet
Rundunar sojojin Najeriya ta gano gawar Janar Idris Alkali mai ritaya a wata rijiya da ke Gushwet a gundumar Shen ta karamar hukumar Jos South a jihar Filato.amsa: 15
Wasu 'yan bindiga da ake tunanin 'yan Boko Haram ne sun sace 'yan mata 15 a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar.amsa: Matsalar damuwa
Vicki Archer, 41, 'yar kimanin shekara 41, na da matsalar damuwa kuma sau biyu tana yunkurin kashe kanta, in ji wani bincike da wata kotu ta yi.