Kotun ta ce idan ba a bi umarninta ba to za ta kama sifeto janar na 'yan sanda na wancan lokaci, Ibrahim Idris da ministan Shari'a, Abubakar Malami da Darakta Janar na SSS, Lawal Daura, da laifin rasahin girmama kotu kuma za su iya fuskantar zaman gidan kaso idan suka ci gaba da yin burus da umarnin na kotu na Disamba 2, 2016.