Gasar Olympic Ta Tokyo 2020: Ƴan tseren Afrika da za ku kalla

  • Taoufik Makhloufi, 33

    Aljeriya Ɗan wasan gudu

    Taoufik Makhloufi ɗan tsere matsakaicin zango ne (na tseren mita 800 da mita 1,500).

    Ya fara zuwa Gasar Olympic ne a gasar 2012 da aka yi a london inda ya zo na ɗaya da kyautar kambun zinare a gasar gudu ta mita 1,500, sannan ya ci kyautar azurfa biyu a gasar da aka yi ta Rio a 2016

  • Wali Bidani, 27

    Aljeriya Ɗaga kayan nauyi

    Wali Bidani ɗan Aljeriya ne da ya fara bayyana a Gasar Olympic ta London 2012 sai kuma gasar Olympic ta Rio 2016.

  • Azenaide Carlos, 31

    Angola Wasan ƙwallon hannu

    Azenaide Carlos ƴan wasan ƙwallon hannu ce kuma mamba a ƙungiyar wasan ƙwallon hannu ta mata ta Angola da ake kira Pearls.

    Sau uku ta halarci Gasar Olympic tun shekarar 2008

  • Nijel Amos, 27

    Botswana Dan wasan tsere

    Nijel Amos dan wasan tseren kasar Botswana ne kuma mai rike da lambar yabo ta azurfa na gasar wasan tseren maza na mita 800 a wasannin Olympic na shakarar 2021 da aka yi a birnin London

    Gasar wasan Tokyo na shekarar 2020 ne karo na uku da yake fita wasan Olympics

  • Hugues Fabrice, 28

    Burkina Faso Dan wasn tsallen nesa

    Hugues Fabrice da wasan tsallen nesa ne na kasar Burkina Faso wanda ya samu lashe lambar yabo ta tagulla a gasar wasan motsa jiki na duniya na shekarar 2019

  • Francine Niyonsaba, 28

    Burundi Yar wasan tsere

    Francine Niyosaba 'yar wasan tseren kasar Burundi ce wacce ta samu lambobin yabo na azurfa a gasar wasannin tseren mita 800 na mata a birnin Rio a shekarar 2016 da 2017

  • Cheik Cisse, 27

    Cote D' Ivoire Dan wasan Taekwondo

    Cheik Cisse ya kafa tarihi a lokacin da ya ciyo wa kasar Ivory Coast lambar zinari ta farko a gasar wasan Olympic ta shekarar 2016 a birnin Rio.

    Ya kuma zama dan Afirka na farko da ya taba samun lambar zinari a wasan Taekwondo.

  • Marie-Josee Ta Lou, 32

    Cote D'Ivoire Yar wasan tsere

    Marie-Josee Ta Lou 'yar wasan tseren kasar Ivory Coast ce wacce ta yi gudun mita 100 da mita 200

    Ta samu lambar yabo ta Tagulla a gasar steren mitoci 100 ta mata a gasar wasan motsa jiki ta duniya a shekarar 2016 kuma ta zama ta 4 a gasar wasan Olympics ta io a shekarar 2016 a duka gasar gudun mitoci 100 da kuma 200

  • Haydy Morsy, 22

    Masar Wasan Pentathlon

    Haydy Morsy 'yar wasan motsa jiki da pentathlon ce da tafi shahara a wasan ninkaya da sukuwar doki.

    Gasar wasan Olympics na shekarar 2020 a Tokyo shi ne karo na biyu da ta ke shiga gasar.

  • Azmy Mehelba, 30

    Masar Harbi

    Azmy Mehelba Dan gasar wasan harbi ta kasar Masar ce da waNDA gasar wasan Olympics na shekarar 2020 a birnin Tokyo ya zama karo na uku da ya ke fitowa.

    Ya lashe kyautar lambar zinari a gasar wasan cin Kofin Duniya na harbi ISSF a cikin watan Mayun shekarar 2021.

  • Giana Farouk, 21

    Masar Karate

    Giana Farouk 'yar wasan damben karate ce ta kasar Masar wacce ta ya zama karo na biyu da ta ke shiga gasar wasan Olympics na Tokyo a shekarar 2020.

    Ta lashe kyauta lambar Zinari a shekara ta 2026 da lambobin Tagulla a gasar shekara ta 2018 ta wasan damben Karate na Duniya kowannensu.

  • Merhawi Kudus, 27

    Eriteria Tseren Keke

    Merhawi Kudus mai shakaru 27, dan kasar Eritrne anda ya zama na uku a gasar rangadin tseren keken shekarar 2021 a kasar Turkiyya.

    Ya lashe gasar tsere Time Individual Trial ta kasar Eritrea a shekarar 2021 kana na biyu a Tokyo a karon sa na farko na shiga gasar wasan Olympics.

  • Amanuel Gebreigzabhier

    Eritrea Tseren keke

    Amanuel Gebreigzabhier ya shiga gasar wasan Olympics din sa karo na biyu. Dan wasan tseren keken na kasar Eritrea ya zo na daya a gasar zakaru ta African Road Championships a shekarar 2018

  • Mosana Debesay, 27

    Eritrea Tseren keke

    Mosana Debesay 'yar wasan tseren kekuna ce ta kasar Eritrea wacce ta lashe gasar tseren African Road Championships a shekarar 2019.

    Kanwar dan wasan tseren kekuna Mekseb Debesay ce.

  • Letesenbet Gidey, 23

    Ethiopia Gudun Fanfalaki

    Letesenbet Gidey 'yar wasan Gudun Fanfalaki ta kasar Ethiopia ce kuma mai rike da kambun yabo na duniya na gasar gudun mita 5,000 na mata kana a baya bayan nan ta sake yin fice a duniya na gudun mita 10,000.

    Ta lashe lambar azurfa a gasar mata ta gudun mita 10,000 a gasar wasan motsa jiki na duniya na shekarar 2019,

  • Selemon Barega, 21

    Ethiopia Dan wasan tsere mai nisa

    Selemon Barega dan wasan tsere mai nisa na kasar Ethiopia ne wanda ya lashe kyautar lambar azurfa na gasar maza ta gudun mita 5,000 a gasar wasan motsa jiki na duniya na shekarar 2019.

    Ya yi gasarsa ta biyu a wasan Olympics a birnin Tokyo shekarar 2020.

  • Yomif Kejelcha, 23

    Ethiopia Dan wasan tseren mai nisa

    Yomif Kejelcha dan wasan tsere na kasar Ethiopia ne wanda wasan Olympics na Tokyo ne karo na biyu da yake shiga gasa.

    Kejelcha ya taba lashe kyautar lambar zinari a gasar gudun mita 3,000 ta maza a gasar wasan motsa jiki ta duniya.

    Ya kuma lashe kyautar lambat azurfa a gasar gudun mita 10.000 ta maza a shekarar 2019.

  • Lelisa Desisa, 31

    Ethiopia Wasan gudun fanfalaki

    Lelisa Desisa dan wasan gudun fanfalaki na kasar Ethiopia ne kuma wanda ya lashe kyautar lambar zinari a gasar gudun fanfalaki na maza a gasar wasan motsa jiki na shekarar 2019.

  • Shura Kitata, 25

    Ethiopia Dan wasan Gudun Fanfalaki

    Shura Kitata dan wasan Gudun Fanfalaki na kasar Ethiopia ne.

    A gasar wasan Gudun Fanfalaki na birnin London a shekarar 2020, ya lashe kyautar lambar zinari bayan da ya samu galaba kan abokin karawarsa tauraron gasar gudu Eliud Kipchoge wanda ya taba zo wa na biyu a gasar shekarar 2018.

  • Gudaf Tsegay, 24

    Ethiopia Yar wasan tska-tsaki na tsere mai nisan zango

    Gudaf Tsegay 'yar wasan tsaka-tsaki ta gudu mai nisan zango ce ta kasar Ethiopia wacce ta ciri tuta wajen samun galaba a gasar wasan gudun mita 1,500 ta mata a kasar Faransa a shekarar 2021.

    Ta lashe kyautar lambar tagulla a gasar World Championships a shekarar 2019.

  • Gina Bass, 26

    Gambia Yar wasn tsere

    Gina Bass 'yar wasan tsere ta kasar Gambia ce wacce ta lashe kyautar lambar zinari a gasar mata ta gudun mita 200 a birnin Rabat a gasar kasashen Afirka ta shekarar 2019.

    Gasar wasan Olympics daaka gudanar a birnin Tokyo ne karo na biyu da ta ke shiga gasa.

  • Julius Yego, 32

    Kenya Dan wasan jifan mashi na Javelin

    Juliusu Yego na wasan jifan mashi na Javelin ne na kasar Kenya wanda samu galabar lashe kyautar lambar azurfa a gasar wasan Olympics na birnin Rio a shekarar 2016.

    Ana kuma yi masa lakabi da Mr YouTube saboda ya kasaita wajen fasaharsa ta wasannni ta hanyar kallon bidiyo ta manahajar YouTube.

  • Brigid Kosgei, 27

    Kenya Yar waan Gudun Fanfalaki

    Brigid Kosgei 'ya wasan Gudun Fanfalaki ceta kasar Kenya wacce ta lashe gasar shekara ta 2018 da 2019 na gudun fanfalaki a birnin Chicago da kuma shekarar 2019 da 2020 a gasar wasan gudun fanfalaki na birnin London.

    Kosgie ta rike babban kambu na duniya, a cikin lokaci 2;14;04 ta samu galaba a Gudun Fanfalakin birnin Chicago. Kuma ta shiga gasa karo na biyu a gasar wasan Olympics na birnin Tokyo.

  • Eliud Kipchoge, 36

    Kenya Dan wasan Gudun Fanfalaki

    Eliud Kipchoge kwararren dan wasan tsere mai dogon zango ne.

    Tauraron wasan motsa jikin na kasar Kenya a mai rike dakabu na gasar wasan Gudun Fanfalaki na Duniya a kan lokaci na 2;01:39 a ranar 16 ga watan Satumbar shekarar 2018 a gasar shekara ta 2018 da aka gudanar a birnin Berlin.

    Ya kuma lashe kyautar lambar zinari a gasar wasan Olympics na shekarar 2016 a birnin Rio.

  • Beatrice Chepkoech, 29

    Kenya Yar wasan tsere na steeplechase

    Beatrice Chepkoech ita ce a yanzu tauraruwa mai rike da kambun wasan steeplechase ta duniya.

    Yar wasan tseren dogon zango ta kasar Kenya mai rike da lambar zinari ce ta gasar gudun mita 3,000 na steeplechase a gasar wasan motsa jiki ta duniya a shekarar 2019.

  • Faith Kipyegon, 27

    Kenya Yar wasan tseren dogon-zango

    Faith Kipeyegon 'yar wasan tseren dongon-zango na mita 1500 ce ta kasar Kenya wacce ta lashe kyautar labar zinari a gasar wasan Olympics ta birnin Rio a shekarar 2016.

    Ta kuma lashe kyuatar lambar azurfa a gasar wasan motsa jiki ta duniya a shekarar 2017 da karin wata lambar azurfar a gasar zakarun wasan motsa jiki na shekarar 2019.

  • Khadija Mardi, 30

    Morocco Yar wasan dambe

    Khadija Mardi 'yar wasan daben kasar Morocco ce da ta shiga gasar wasan Olympic na shekarar 2016 a birnin Rio, amma ta kasa samun galaba a gasar damben ta mata masu nauyin kilo 69 zuwa 75 na kusa na daga kai sai karshe na biyu.

    Ta kuma samu galabar samun kyautar lambar tagulla a gasar damben mata na shekarar 2019.

  • Rababe Arafi, 30

    Marocco Yar wasan tsere

    Rabebe Arafi 'yar wasan tseren Morocco ce da ta lashe lambar zainari a gasar wasan tseren mita 1500 ta na mata IAAF Diamond League na shekarar 2019.

    Gasar wasan Olympics ta shekarar 2020 a birnin Tokyo shi ne karo na biyu da ta ke shiga gasar.

  • Ramzi Boukhiam, 27

    Morocco Dan wasan Zamiya

    Ramzi Boukhaim kwararren na wasan zamiya ne.

    Zai shiga gasar wasan zamiaysar na biyu inda zai wakilci Morocco a gasar wasan zamiya ta farko za a yi.

  • Soufiane El Bakkali, 27

    Morocco Dan wasan tseren steeplechase

    Soufiane El Bakkali dan Moroko ne da ya lashe kyautar ta gulla ta tseren kilomita 3,000 na maza a 2017 a gasar zakaru ta IAAF

    A 2016 ya fara halartar gasar Olympics

  • Maria Machava,

    mozambique Ninƙaya

    Maria Machav dan Mozambique ne wanda zai fara halartar gasar Olympics da za a yi a Tokyo a karon farko a rayuwa

  • Deisy Nhaquile

    Mozambique sayarwa

    Deisy Nhaquile 'yar wasan ruwa ce ta Mozambque wadda za ta fara halartar gasar Olympics a karon farko ta Tokyo 2020.

    Ta lashe gasar ninƙaya ta 2019 a ajin Radial 420

  • Denise Parruque

    Mozanbique Ninƙaya

    Desine Parruque yar wasan Mozambique ce da ke wasan ninƙaya wadda za ta halarci gasar Olympics da za a yi a Tokyo a karon farko ta 2020.

    Tare da ƙawarta Maria, wadda ta lashe gasar ajin Afrika ta 2019 ta regatta 470

  • Maike Diekmann, 27

    Namibia Tseren kwale-kwale

    Maike Diekmann 'yar Namibia ce da ke tseren kwale-kwale wadda za ta fara wakiltar ƙasar a gasar Olympics a karon farko

  • Aminatou Seyni, 24

    Nijar Yar tsere

    Aminatou Seyni 'yar tseren gudun Nijar ce da ta wakilce ta a 2019

  • Blessing Okagbare, 33

    Najeriya Yar dogon tsalle ce da gudu

    Blessing Okagbare 'yar tsere da dogon tsallen Najeriya ce tare da dan gajeren gudu

    Ita ce ke rike da kambun gudun mita 100 wanda ta kai cikin sakan 10.75, ta kuma kafa wani sabon tarihin a irn wannan gudun wanda ta kai a sakan 10.63 a watan Yuni 2021

    A wannan lokacin ta kafa sabon tarihin Najeriya da Afrika yanzu kuma 'yar Jamaica Shelly-Ann ce ke jan ragamar gasar ta 2021

  • Elizabeth Anyanacho, 22

    Najeriya Kokawar Takwando

    Elizabeth Anyanco ita ce mace 'yar Najeriya ta biyu a tarihi kuma 'yar shekara 16 da ta samu damar halartar gasar Olympics a wasan Takwando

  • Divine Oduduru, 24

    Najeriya Yar tsere

    Divine Oduduru ya fara wasansa ne a gasar Olympics da aka yi a Rio a 2016.

    Wannan ɗan steren shi kadai ne dan Najeriya da taɓa zuwa wasan daf da na akrshe a cikin maza yan gudu.

  • Tobi Amusan, 24

    Najeriya yar gudu

    Tobi Amusan yar wasan tsallake ce da kuma gudu na karamin zango wadda ta taba lashe gasar zinare ta mata a matakin gudu mita 100 da kuma gasar tsallake a 2018 a gasar kasashen rainon Ingila da aka yi a Australia

    Ta fara wasa ne a 2016 a Rio kuma taje wasan daf da na karshe, kadan ya hana ta zuwa wasan karshe, amma dai ta kare a matsayi na uku cikin sakan 12.91

  • Ese Brume, 25

    Najeriya Wasan gudu

    Ese Brume na daya daga cikin mata masu tsalle da suka muce mita 7 ko sama da haka.

    Itama ta fara zuwa gasar Olympics ne a 2016 a Rio inda ta gama a matsayi na 5.

    ta sam kyautar tagulla a 2019 a gasar tsalle-tsalle ta duniya

  • Chukwuebuka Enekwechi, 28

    Najeriya Wasan jifa

    Chukwuebuka Enekwechi dan Najeriya ne da ke wasan jefa dutse wanda ya ci kyautar tagulla agasar kasashe rainon Ingila 2018.

    Haka kuma ya zo matsayi na takwas a gasar duniya ta 2018 shi ne kadai dan Najeriya da yaje nan.

  • Usheoritse Itsekiri, 23

    Najeriya Dan gudu

    Usheoritse dan tseren fanfalakin Najeriya ne kuma ya lashe kyautarsa ta farko da tagulla a wasan duniya na tseren maza na mita 100 da aka yi a Rabbat in da ya kammala a sakan 10.02

  • Esther Toko, 21

    Najeriya Yar tseren kwale-kwale ce

    Esther yar tseren jirgin kwale-kwale ce da ta lashe kyautar tagulla da azurfa a CapeVerde a 2019 a Afrika.

    Gasar Tokyo da za a yi za ta zama ta farko da za ta fara halarta kuma ta zama 'yar wasan gida ta farko da za ta fara wakiltar Najeriya

  • Ayomide Emmanuel Bello, 19

    najeriya Tseren kwale-kwale na mutum daya

    Ayomide ta fara halartar Olympics dinta na farko ne a matsayin 'yar wasan tseren kwale-kwale daga Najeriya bayan samun gurbi da ta yi

    Ta taba cin kyautar zinare sau hudu a Rabat a 2019

  • Rodney Govinden, 35

    Seychelles Ninƙaya a kwale-kwale

    Rodney zai wakinci kasarsa Seychelles a gasar Olymcpics da za a yi a Tokyo a 2020.

    Wannan ne Olympics na biyu da zai halarta bayan wanda ya je a 2016 da aka yi a Rio. Ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kowanne a Seychelles a 2019.

  • Wayde Van Nierkerk, 29

    Afrika Ta Kudu Dan tseren gudu

    Wayde dan tseren fanfalakin Afrika Ta Kudu ne ya lashe kyautar zinare a gasar Rio da aka yi a 2016 ta tseren mita 400

    Ya kama wani sabon tarihi a duniya inda ya kammala dugun a sakan 43.03 ya wuce mai rike da kambun dan America Michael Johnson.

  • Chad Le Clos, 29

    Afrika Ta Kudu Ninƙaya

    Chad dan wasan ninƙayar Afrika Ta Kudu ne ya lashe kyautuka da yawa ciki harda zinare daya a Landan a 2012 da kuma azirfa a 2016 a Rio.

  • Akani Simbine, 27

    Afrika Ta Kudu Dan tseren gudu

    Akani dan steren fanfalakin Afrika Ta Kudu ne wanda ya lashe kyautar zinare a gasar kasashen rainon Ingila a 2018.

    Ya zo matsayi na hudu a gasar duniya da aka yi a 2019

  • Caitlin Rooskrantz, 19

    Afrika Ta Kudu Yar motsa jiki ce

    Caitlin Ta shirya tsaf domin fara halartar gasarta ta Olympics da za a yi a Tokyo ta 2020.

    Yar wasan motsa jikin ta Afrika Ta Kudu ta lashe kyauta a 2018 da kuma a 2019 wdda aka yi a Hugary a gasar duniya ta motsa jiki

    Ita ma za ta fara halartar gasar Olympics ne a 2020 da za a yi a Tokyo

  • Erin Sterkenburg, 18

    Afrika Ta Kudu Hawan tsauni

    Erin dan hawan tsaunin Afrika Ta Kudu za kuma ta halarci gasar Olympics ta Tokyo 2020.

    Ta lashe kyauta a gasar Afrika ta IFSC 2020

  • Henri Schoeman, 29

    Afrika Ta Kudu Tsalle-tsalle da guje-guje

    Henri dan wasan Afrika Ta Kudu ne a bangaren tsalle-tsalle da guje-guje Ya kuma lashe zinare yayin gasar maza ta kasashen rainon Ingila da aka yi a 2018.

    Ya kuma lashe gasar tagulla ta maza a 2016 da aka yi a Rio

  • Boipelo Awuah, 15

    Afrika Ta Kudu Sululu akan takalmin taya

    Boipelo ita ce yar Afrika Ta Kudu ta farko da ta halarci Olympics a matsayin yar wasan sululun takalmin taya kuma ita ce mafi kankantar shekaru daga Afrika da ta halaci gasar

  • Blitzboks

    Afrika Ta Kudu Wasan zari zuga

    Tawagar Afrika Ta Kudu ta wasan zari zuga ta mutum bakwai wadda aka fi sani da Blitzboks sun lashe tagulla a gasar Olympics da aka yi Rio a 2016.

    Sun taɓa zuwa matsayi na biyu a gasar cin kofin duniya a wasan zari zuga a 1997

  • Oussama Mellouli, 37

    Tunisia Ninƙaya

    Oussama dan wasan ninƙaya ne na dogon zango daga kasar Tunisia, ya lashe kyautar zinare ta maza ta mita 1500 a Olympics da aka yi a Beijing a 2008 da kuma wadda aka yi a Landan a 2012.

  • Marwa Amri, 32

    Tunisia Kokwawa

    Marwa Yar kokwawa ce daga ƙasar Tunisia kuma ta lashe gasar tagulla a wasan Olympics da aka yi a Rio a 2016, ita ce mace ta farko da ta lashe kyautar tagulla daga Afrika a wasan kokwawa.

  • Ines Boubakri, 32

    Tunisia

    Ines yar wasan kare ce daga Tunisia ta kuma lashe kyauta a wannan gasar a Olympics da aka yi a Rio a 2016

  • Jacob Kiplimo, 20

    Uganda Tseren gudu

    Jacob ɗan tseren fanfalaki ne da ya taka rawa a gudun maza na mita 3000 a gasar IAAF ta 2020.

    Idan ya je gasar Tokyo ta 2020 za ta zama Olympics na biyu da ya halarta

  • Ronald Musagala, 28

    Uganda Tseren gudu

    Ronald dan tseren fanfalaki ne daga kasar Uganda wanda ya fara halartar Olympics a Rio a 2016, ya kuma yi gudu na maza na mita 1500

    Ya lashe kyautar zinare a 2019 da aka yi a Landan da Paris

  • Joshua Cheptegei, 25

    Uganda Tseren gudu

    Joshua dan tseren fanfalaki ne da ya samu nasarar lashe kyautar zinare ta maza ta mita 10,000 a 2019 ya kuma kafa sabon tarihi a duniya yayin gudun mita 5,000 a Manaco a 2020

  • Peruth Chemutai, 22

    Uganda Tsalle-tsalle

    Peruth yar wasan tsalle-tsalle ce daga Uganda ta yi was a Rio 2016 a tseren mata na mita 3,000

    Ta kuma zo ta biyar a tseren mata ta mita 3,000 a wasan karshe da aka yi na duniya a 2019

  • Copper Queens

    Zambia Kwallon kafa

    Tawagar kwallon kafar Zimbia wadda ake kira da Copper Queens za ta fara halartar gasar Olympics a 2020 da za a yi a Tokyo

  • Scott Vincent, 29

    Zimbabwe Golf

    Scott ya fara halartar Olympics ne a 2019, ya kuma kammala a matsayi na hudu a gasar da aka yi a Japan.

  • D'Tigers

    Nijeriya Kwallon kwando

    Tawagar maza ta kwallon kwandon Najeriya da aka fi sani da D'Tigers ita kaɗai ce tawagar Afrika da ta samu gurbi a Tokyo 2020.

    Tawagar maza ta kwallon kwandon Najeriya da aka fi sani da D'Tigers ita kaɗai ce tawagar Afrika da ta samu gurbi a Tokyo 2020.

    Zakarun nahiyar Afrikan sun doke Astralia da Amurka a watan Yuli 2021 a wasannin sada zumunta.

  • The Pearls

    Angola Kwallon hannu

    Tawagar kwallon hannu ta kasar Angola da ake kira The Pearls ita ce ta lashe gasar kwallon hannu ta kasashen Afrika ta 2021.

    Sun tsaya a matsayi na takwas a gasar Rio a 2016 lokacin da aka cire su a wasan kusa da daf da na karshe