Jerin ayyukan Nnamdi Kanu da ƙungiyar IPOB

Shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu Getty

Ya kafa kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da ta ɓalle daga the Movement for the Actualization of the Sovereign State of Biafra (MASSOB), wadda ta yi suna a shekarun 2000 tare da ƙungiyar Biafra Zionist Movement (BZM).

Tun bayan fara fafutukar IPOB a 2012, an gudanar da zanga-zangar son kafa ƙasar Biafra a wasu ƙasashen Turai da Afirka. Hotunan Getty

Hukumar Tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS ta kama Kanu tare da gurfanar da shi a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kan laifin tunzura jama'a da cin amanar ƙasa da mallakar makamai ba bisa doka ba da kuma shigar da kayan aiki na gidan rediyo ƙasar.

An ci gaba da tuhumarsa a wata Kotun Majistare a Abuja kan zarginsa da kitsa munanan laifuka da tsokana da kuma zama mamba na wata haramtacciyar ƙungiya.

Kama Kanu da shari'arsa sun janyo faɗa tsakanin magoya bayansa da ƴan sanda, inda aka kashe ƴan sanda biyu a wajen zanga-zanga a Anaca da ke jihar Anambra.

Wata Babbar Kotu a Abuja ta bayar da umarnin sakin Kanu amma gwamnatin tarayya ba ta cika umarnin ba.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake shigar da sabuwar ƙara inda take tuhumar Mr Kanu da laifuka shida, tana mai cewa yana yi wa tsaron ƙasa barazana, inda ta nemi kotun da ta aika shi gidan yari na Kuje.

Kanu ya shigar da ƙarar gwamnatin Najeriya a kotun ECOWAS, inda yake zargin Shugaba Muhammadu Buhari kan ci gaba da riƙe shi duk da umarnin da kotu ta bayar cewa a sake shi.

Bayan ci gaba da riƙe shi fiye da shekara ɗaya ba tare da yi masa shari'a ba, an sake gurfanar da Nnamdi Kanu da tuhumarsa kan kitsa munanan laifuka, da zama mamba na wata haramtacciyar ƙungiya da kuma takalar faɗa.

Nnamdi Kanu da ankwa a hannunsa yayin da aka gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya ta Abuja kan tuhumarsa da cin amanar ƙasa a 2016.

An sake shi a karon farko cikin a ƙalla wata 18 da ya yi a tsare, bayan da Mai Shari'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya ta bayar da belinsa saboda rashin isasshiyar lafiya.

Sojoji sun shiga gidansa a Afara-Ukwu kusa da Umuahia a jihar Abia. Kanu ya samu beli ya kuma tsere ya bar ƙasar. Shiga gidansa da sojoji suka yi ya janyo rikici tsakanin magoya bayansa da sojojin da ke sintiri a kusa da gidan nasa.

Gwamnatin tarayya ta samu umarnin wucin gadi na ayyana ƙungiyar IPOB a matsayin ta ta'addanci. An yi watsi da ƙoƙarin ɗaukaka ƙara da ƙungiyar ta yi.

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarnin a yi wa Nnamdi Kanu shari'arsa daban da sauran mutum huɗun da ake tuhumarsu tare: Chidiebere Onwudiwe da Benjamin Madubugwu da David Nwawuisi da kuma Bright Chimezie.

Babbar Kotun Tarayyar da ake shari'ar Mr Kanu kan zargin sa da cin amanar ƙasa da ta'addanci. Hotunan Getty

Wani bidiyo da ke nuna Kanu yana addu'a a wajen ibadar Yahudawa na Baitul Muƙaddas. Wannan ne karo na farko da aka ga shugaban IPOB ɗin tun bayan tserewarsa daga Najeriya a 2017.

A yayin da yake gudun hijirar, Kanu ya ci gaba da fafutukarsa ta adawa da gwamnatin Najeriya. A can Najeriyar kuwa magoya bayansa sun ci gaba da fafutuka da kuma karawa da jami'an tsaro.

Kanu ya koma Birtaniya daga Isra'ila.

Mr Kanu ya yafa mayafin addu'ar Yahudawa a lokacin da yake barin gidansa a Umuahia, a kudu maso gabashin Najeriya, ranar 26 ga watan Mayun 2017. Hotunan Getty

Mai shari'a Binta Nyako ta janye belin da ta bai wa Mr Kanu, inda ta bayar da izinin a kamo shi.

Kanu ya yi kira da a kashe tare da sare kawunan jami'an tsaron Najeriya a wani bidiyo da ya yi a shafin Facebook da aka nuna kai tsaye.

Babban Atoni Janar na gwamnatin Najeriya kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami, ya zarge shi da son haddasa husumar da ta jawo kisan fiye da mutum 100 da suka haɗa da ƴan sanda da kai hare-hare kan hukumomin gwamnati da na jami'an tsaro a yankin Kudu maso Gabashin ƙasar.

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta fara gudanar da shari'ar Kanu a bayan idonsa. Mai shigar da ƙarar ya gabatar da shaidu biyar da za su bayar da shaida kan abubuwan da yake yi.

Facebook ya dakatar da Nnamdi Kanu bayan da ya yaɗa wasu jerin bidiyo na hare-haren da ƴan bindiga suka kai wa wata al'ummar Fulani. Shafin Facebook ɗin ya ce Kanu ya sha nanata laifin take dokokinsa da suka haɗa da cutar da wasu da yaɗa kalaman ƙiyayya.

Wani ofishin ƴan sanda a Ebonyi da aka yi zargin ƴan IPOB ne suka ƙona shi. An ci gaba da kai hare-hare kan jami'an tsaro da hukumomin gwamnati da fadin yankin kudu maso gabas da kudu maso kudancin ƙasar.

An kama Kanu a Kenya tare da mayar da shi Najeriya don ci gaba da shari'arsa. Kotu ta bi umarnin gwamnatin tarayya na tsare Mr Kanu a hannun hukumar DSS har zuwa 26 ga watan Yuli.

An sake ɗaga shari'ar zuwa 21 ga watan Oktoba, sannan an sake ɗaɗɗagawa saboda gaza gabatar da Mr Kanu da DSS suka yi a gaban kotu.

Ipob ta ayyana zaman gida na dole a duk ranar Litinin har sai gwamnati ta saki Nnamdi Kanu.

Ipob ta sanar da cewa ta soke umarnin zaman gida na dole da ta sanya, wanda ya durƙusar da harkokin kasuwanci a kudu maso gabas a duk ranar Litinin, ya kuma jawo ɗalibai a yankin suna rasa muhimman jarabawowi. Sai dai duk da haka an ci gaba da yin zaman gidan, inda mutane masu ɗauke da makamai ke tursasa yin hakan, suna kashe mutane tare da ƙona dukiyoyi a faɗin yankin.

Gwamnatin tarayya ta sake gabatar da ƙarin tuhume-tuhume a kan Kanu daga bakwai zuwa 15.

Nnamdi Kanu ya ƙi amsa laifin sabbin tuhume-tuhumen da ake yi masa. Mai shari'a Binta Nyako ce ta jagoranci shari'ar. Sannan Mai shari'a Benson Anya na Babbar Kotun Tarayya ta Abia ya bai wa gwamnatin tarayya umarnin biyan Kanu naira biliyan ɗaya a matsayin diyya na kutsawa gidansa da aka yi a 2017, biyo bayan ƙorafin da lauyansa ya shigar a watan Agustan 2021.

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta sake ɗaga ƙarar ɗan awaren zuwa 8 ga Afrilu. An yi zaman sauraron shari'ar ne don tabbatar da, ko kore sahihancin gyare-gyaren da aka yi wa zarge-zargen ta'addanci da cin amanar ƙasa da gwamnatin tarayya ke yi wa Mistra Kanu.

Alƙalin da yake shari'ar a Babar Kotun Tarayya ya soke takwas daga cikin tuhume-tuhume 15 da gwamnatin Najeriya ke yi wa Kanu.