Tura ku ci gaba da karantawa
A da wannan titi ne mai cunkoso a Buriticupu, wani birni a arewa maso gabashin Brazil.
"Yanzu manya-manyan ramukan na da zurfin mita 80, gini mai hawa 20 zai iya shiga cikinsa. "
Ana kiran wawakeken rami irin wannan a yankin da suna "voçoroca" ko "tsagaggiyar ƙasa" a harshen Tupi-Guarani.
Lamarin ya samo asali ne sakamakon yashewar ƙasa daga wawakeken rami daya daga cikin mafi girman gurbacewar kasa sakamakon ruwan sama da kuma ruwa maras kyau.
Kuma tana ƙara ta'azzara ne cikin sauri, tana lalata dubban gidaje a Latin Amurka da Afirka.
A da wannan titi ne mai cunkoso a Buriticupu, wani birni a arewa maso gabashin Brazil.
"Yanzu manya-manyan ramukan na da zurfin mita 80, gini mai hawa 20 zai iya shiga cikinsa. "
Ana kiran wawakeken rami irin wannan a yankin da suna "voçoroca" ko "tsagaggiyar ƙasa" a harshen Tupi-Guarani.
Lamarin ya samo asali ne sakamakon yashewar ƙasa daga wawakeken rami daya daga cikin mafi girman gurbacewar kasa sakamakon ruwan sama da kuma ruwa maras kyau.
Kuma tana ƙara ta'azzara ne cikin sauri, tana lalata dubban gidaje a Latin Amurka da Afirka.
Tsohon jami'in dansanda José Ribamar Silveira ya kusa mutuwa lokacin da ya fada cikin wannan ƙoramar.
Ya ɓace ne yayin da yake tuƙi zuwa gida daga wani biki da dare a watan Mayun 2023.
Yayin da ya juya motar, mutumin mai shekara 79 ɗin ya juyo ya koma baya. a lokacin an shiga lokacin duhu, babu alamun gargaɗi ko shinge a kusa da wawakeken rami, saboda haka kafin ya ankara, motarsada shi suka faɗa cikin babban rami.
"Lokacin da motar ta zame, duk da cewa tana faɗawa da sauri, tunanin ƙramin dana ne kawai ya faɗo min," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Baby Gael ya cika wata huɗu a ranar da ta gabata. Laftanar Silveira ya ce: “Na roƙi Allah ya kiyaye ni domin na samu na yi renon ɗana da kai na.
Yayi da yake faɗawa, sai ya sume kuma ya farka a kasan wawakeken rami bayan awa uku. Bayan aikin ceto mai sarƙaƙƙiya na watanni, yanzu yana iya tafiya ba tare da sandan dogara wa ba.
Abun da ya fuskanta misali ne babba na haɗarin da mazauna Buriticupu 70,000 ke fuskanta.
Yayin da wasu gungun manya-manyan ramuka suka bayyana, ana fargabar cewa birnin na jihar Maranhao, dake gefen dajin Amazon, na iya rabuwa zuwa gida biyu. A mita 350 sama da matakin teku, Buriticupu yana da kusan manya-manyan ramuka 30 , tare da guda biyu da kilomita 1 ne ya raba su.
Edilea Dutra Pereira, masanin ilimin kasa kuma farfesa a Jami'ar Tarayya ta Maranhão ta ce "Idan hukumomi ba su ɗauki mataki kan wannan lamarin ba, to ruwan ƙoramar za su taru kuma su hadu su kafa kogi."
Manya-manyan ramuka sun kasance wani ɓangare na tarihin yanayin ƙasa a miliyoyin shekaru.
Sai dai Farfesa Pereira da sauran masana da muka zanta da su sun bayyana cewe manya-manyan ramukan da ake da su na karuwa cikin sauri kuma suna fargabar za a sami sabbin ramuka irinsu saboda sauyin yanayi wanda zai iya sa ruwan sama ya yi tsanani.
Kuma a wuraren da biranen suke girma ba tare da ingantaccen tsari da abubuwan more rayuwa don magance ruwan sama ba, haɗarin yana ƙaruwa.
Brazil ta kasance ƙasa da abin ya fi shafa a yankin Latin Amurka, sai dai Mexico, Colombia, Ecuador da kuma Argentina na fama da irin wannan matsala. Ba ya ga nahiyar, ƙasashe a Afrika, kamar Angola, Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo da kuma Najeriya - inda magudanan ruwa suka tone har zuwa tsawon kilomita biyu - su ma abin ya shafe su.
Wannan irin zaizayar ƙasa na barazana ga gonaki a wasu sassan China, Amurka har ma da Turai.
Babu alkaluma a hukumance kan waɗanda suka arsa rayukansu sakamakon zaizayar ƙasa, sai dai hukumomi a Buriticupu sun ce manya-manyan ramukan sun shafi gidaje aƙalla 50 da tilastawa mutane barin muhallansu, inda gidaje suka zama kangaye babu kowa a ciki.
Gidan Marisa Cardoso Freire na kusa da wani wawakeken rami ne kuma jami'ai sun bayyana haɗarin zama a wurin a watan Mayun 2023.
Ya zama tilas ta bar gidanta don komawa wani ɓangare na Buriticupu tare da wasu iyalai 100.
City Hall ya yi alkawarin biya wa mutanen da matsalar ta ɗaiɗaita kuɗin hayar sabbin gidajen da suke zaune, sai dai Marisa ta ce hukumomin birnin ba su biya kuɗin a kan lokaci ba kuma ana barazanar tayar da ita.
Lokacin da muka tuntuɓi City Hall domin tambaya kan abin da ke faruwa, sun kasa cewa uffan.
A tsohon gidan Marisa, wasu karnukan iyalanta biyu sun faɗa cikin ramuka, abin da ya janyo mutuwarsu.
Sannan akwai wata rana da take ƙoƙarin samun ɗan ta ɗan shekara 10, mai suna Enzo, wanda ke da lalurar galahanga, domin ya dawo cikin gidan, inda ta ɗaga muryarta.
Enzo ya fusata tare da guduwa zuwa bakin wani wawakeken rami "Idan kika sake yi min ihu, zan jefa kaina cikin ramin nan," kamar yadda ya yi barazana.
"A lokacin ne na faɗa wa mijina cewa ba za mu iya zama a nan na tsawon lokaci ba, yana da haɗari"
A ce ba za ta sake zama a cikin gidan da ta gina da kanta ba.
"Lokacin da na tafi, zuciya ta yi ƙuna saboda abu ne da muka sha gwagwarmaya domin mu cimma shi."
Sare dazuka ya taka muhimmiyar rawa a wannan yanayi na zaizayar ƙasa.
Birnin Buriticupu yanzu wuri ne da yake shimfiɗe babu komai da kuma duwatsu, sai dai yana cikin wani ɓangare na dajin Amazon kuma a baya itatuwa ne suka rufe shi, kamar Cedar, West India locust da kuma ipe.
A shekarun 1990 masana'antar sarrafa katako na bunƙasa a lokacin. Akwai injunan sarrafa katakai sama da 50 da ke aiki sa'a 24 a kowace rana. Shekaru 20 bayan nan, yawancin itatuwan birane sun kare.
"Batun samar da itatuwa yana da muhimmanci, saboda lokacin damina, yana rage malalar ruwa"
Idan babu isassun tsirrai ko itatuwa da za su riƙe ruwa...
Zubar ruwan na tono tsirrai da kuma zaizayar ƙasa
Ruwan koguna da ya tafi da tsirrai.
Za a iya kirkiro da manya-manyan ramuka
Idan babu isassun tsirrai ko itatuwa da za su riƙe ruwa...
Zubar ruwan na tono tsirrai da kuma zaizayar ƙasa
Ruwan koguna da ya tafi da tsirrai.
Za a iya kirkiro da manya-manyan ramuka
Sauyin yanayi zai taɓarɓara al'amarin a yankunan da ke da zaizayar ƙasa kamar yadda zai janyo zubar mamakon ruwan sama
Buriticupu na fama da matsanancin guguwa ba kamar yadda ta saba gani ba, a cewar Juarez Mota Pinheiro, masani kan harkar sauyin yanayi a Jami'ar Tarayya ta Maranhao.
A farkon watannin 2023, jihar Maranhao ta fuskanci ɗaya daga cikin ambaliya mafi muni a tarihinta. Sama da birane 60 suka shiga cikin dokar ta-ɓaci, da ɗaiɗaita dubban mutane da mutuwar gommai.
"An yi hasashen ƙaruwar ruwan sama da kashi 10 zuwa 15 (a duniya baki-ɗaya kafin karewar karni). Hakan yana kamar wanda ba shi da yawa, sai dai idan kuka samu yawaitar saukar ruwan sama, yanayin zaizayar ƙasa na sauyawa," in ji Matthias Vanmaercke, daga Jami'ar KU Leuven a Belgium.
Shi tare da abokinsa Jean Poeson sun yi sharhi kan alkaluma daga ƙarin manya-manyan ramuka sama da 700 a faɗin duniya kuma sun karkare da cewa idan aka samu mamakon ruwan sama kamar yawan alkaluman,to hakan zai ninƙa zaizayar ƙasa da za a samu.
"Zai yi wahala a samu wani masanin kimiyya da zai ki amincewa da cewa sauyin yanayi zai iya janyo matsalar ta ta'azzara," ijn ji Farfesa Vanmaercke.
Wannan matsalar na shafar mutane da dama a faɗin duniya, ciki har da miliyoyi a Afrika.
Babban birnin Demokraɗiyyar Kongo, Kinshasa, yana da ɗaruruwan manya-manyan ramuka - ɗaya daga ciki ya kai nisan kilomita biyu. Akwai sama da magudanai da suka kai nisan kilomita 165 a birnin, wanda al'ummarsa suka kai miliyan 12.
A cikin dare guda da aka tafka mamakon ruwan sama a watan Disamban 2022, mutum 60 ne suka mutu lokacin ruwa ya tafi da gidajensu.
Alexandre Kadada na a can.
"Abin ya faru ne cikin kasa da minti 30 zuwa 40. Ramin ya fara ruftawa ne kafin sauran gidajen su bi baya. Ba za ka iya gane ko da gidan makwabta ba," in ji shi.
"Dukkan abin da na mallakka, gidana, komai ya tafi. Yarana da matata kaɗai na samun damar ceto wa."
Makwabciyar Mr Kadada tare da 'ya'yanta guda huɗu an cikin mutanen da abin ya shafa. Lamarin ya nakasa mijin matar.
Ya'yan Mr Kadada suna cikin fargaba a yanzu musamman ma da zarar an ce yanayi babu kyau.
"Ruwan sama ne ya ɓata komai. Ruwan ya janyo mutuwa da kuma rashin fata," in ji shi.
"Muna ganin abin a matsayin wani sabon bala'i na Anthropocene," in ji Farfesa Vanmaercke. Anthropocene dai kalma ce da masana kimiyya ke amfani da ita domin kwatanta wani lokaci, lokacin da ayyukan bil'adama suka shafi doron ƙasa.
An kiyasta cewa al'ummar Kinshasa za ta ƙaru zuwa miliyan 20 zuwa 2030 da kuma miliyan 35 zuwa 2050, inda zai zama birni mafi girma a Afrika, a cewar bankin duniya.
Rashin tsari mai kyau na raya birane ya kunshi sare itatuwa - abin da ke janyo zaizayar ƙasa - wata sana'a da ake yi ba bisa ka'ida ba a wasu yankuna.
A Buriticupu, mutane na tsoron ruwan sama.
"Akwai lokutan da gidaje ke ruftawa. Suna yin wata ƙara mai tayar da hankali, tana kuma girgiza komai. Mutane su kan yi kuka. Kuncin da hakan ke sa mutane ba ya misaltuwa," in ji Joao Batista, wani bakanike da ke shagon gyara kusa da wani babban magudanan ruwa.
"Na rasa kashi 40 na kwastomomina. Da dama daga cikinsu na tsoron tsayawa a nan," in ji shi. Sai dai duk da haka ya ki barin wurin.
Wani babban rami da ke bayan shagonsa ya taɓa kasancewa wurin wasan yara, in ji shi, sai dai ramin ya zaizaye ya cinye komai.
Ya yanke shawarar shuka wasu itatuwa domin rage barazanar zaizayar ƙasa. Sai dai ganin irin girman matsalar, Buriticupu na buƙatar wata babbar hanya ta magance matsalar.
Sai dai tare da masana aikin gini da kuma zuba jari, "Za a iya shawo kan duka irin wannan matsalar", in ji Farfesa Vanmaercke.
Domin dakatar da zaizayar ƙasa, ya kamata birane su samar da tsarin magudanan mai kyau domin dakatar da malalar ruwa, kamar yadda Farfesa Poesen ya faɗa, domin ruwan ya bi ta wata hanya ba tare da ya bi yankunan da ke cikin haɗarin zaizayewar ƙasa.
Sai dai wannan tsari zai lakume kuɗaɗe a biranen da ba su da kasafin kuɗi mai yawa.
Ofishin mai shigar da ƙara na jihar Maranhao na ɗaukar matakan shari'a kan birnin Buriticupu, inda ya ce birnin bai ɗauki tsare-tsaren da aka amince da su ba.
Magajin birnin Buriticupu Joao Teixeira da Silva ya ki cewa uffan kan lamarin, sai dai ya ce ya nemi buƙatar taimakon kuɗi daga gwamnatin tarayya domin yin aikin hanyar da zai kare kai daga malalar ruwa.
Gwamnatin Brazil ta faɗa mana cewa tana duba yiwuwar fitar da kuɗi dala miliyan 60 wa birnin Buriticupu. Ta ƙara da cewa tuni ta samar da dala 125,000 domin gina wata magudanan ruwa, gyara hanytoyi da kuma rusa gidaje 89.
Ma'aikatar kula da muhalli ta ce tana shirin kaddamar da wani shiri cikin wasu birane, sai dai ba ta yin komai a birin Buriticupu a yanzu.
"Waɗannan ayyuka ne masu girma, ayyuka da ke buƙatar maƙudan kuɗaɗe," in ji magajin birnin. "Abin da muke so shi ne ɗaukar nauyi, daga dukkan matakai musamman birnin, jiha da kuma tarayya."
Sai dai Joao Baptista na sane da cewa idan magudanan ruwa da ke bayan shagonsa ya girma, dole ya bar wurin.
"Wannan yana nuna mana cewa idan ba mu kula da muhallin mu ba, to za ta iya lalacewa. Idan aka ci gaba da ruwan sama irin wannan, to sai dai abin da Allah ya yi mana saboda babu abin da za mu iya yi."
Rahoto: Shin Suzuki
Ƙarin rahoto: Stephanie Hegarty da Emery Makumeno
Editoci Tamara Gil da Carol Olona da kumaAlison Gee
Zane-zane: Caroline Souza
Zane-zanen samfurin 3D: Daniel Arce
Shiryawa: Matthew Taylor, Marta Martí da Simon Frampton
Kula da ayyuka: Holly Frampton da Carol Olona
Mashiryin shiri: Paul Ivan Harris
Ɗaukar hoto: Vitor Serrano, Dareck Tuba da Alex Huguet/AFP via Getty Images
Ƙarin waɗanda suka taimaka: Antonio Guerra, Jami'ar Tarayya ta Rio de Janeiro; Fernando Bezerra, Jami'ar Jihar Maranhão; Gilberto Salviano Almeida Filho da Claudio Luiz Ridente Gomes, Cibiyar Nazarin Fasaha; Marco Anthony Gomes da Helena Filizola, Embrapa; Ryan Anderson, Jami'ar Afirka ta Kudu. Taswirar duniya: Vanmaercke, M., Chen, Y., De Geeter, S., Poesen, J., Campforts, B., Borrelli, P., da Panagos, P.: Hasashen bayanai na gully yawa da kuma zaizayar kasa hadarin a duniya sikelin, EGU Babban Taro 2022, Vienna, Austria, 23-27 May 2022, EGU22-2921 Borrelli, P., Alewell, C., Yang, J. E., Bezak, N., Chen, Y. , Fenta, A. A., Fendrich, A.N., Gupta, S., Matthews, F., Modugno, S., Haregeweyn, N., Robinson, DA , P. (2023). Don samun ingantacciyar fahimtar hanyoyin hanyoyin tafiyar da zaizayar ƙasa da yawa tare a kan filayen noman duniya. Binciken Kiyaye Ƙasa da Ruwa na Duniya, 11 (4), 713-725.