Gargaɗi: Labarin na ƙunshe da hotuna masu tayar da hankali da bayanai na tasirin makaman nukiliya.
"Shekaru 80 sun shuɗe, amma babu abin da ya sauya."
Ga yadda waɗanda bam ɗin ya shafa ke bayani kan harin da Amurka ta ƙaddamar wanda ya lalata biranen Japan guda biyu a watan Agustan 1945.
"Babu darasin da aka ɗauka daga halin da muka tsinci kanmu a ciki, hatsarin da muke ciki a yanzu ya fi na baya," kamar yadda Masako Wada ta shaida wa BBC. Yanzu ita ce mataimakiyar shugaban ƙungiyar Nihon Hidankayo, ƙungiyar waɗanda suka tsira daga harin bam, wadda ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a 2024 - Wada mai fafutikar yaƙi da makaman nukiliya ne, wadda ke son yaɗa labaran mutane irin ta.
Tashio Tanaka tana ƴar shekara shida lokacin da aka jefa bam ɗin a Hiroshima saboda haka tana bayyana irin fargabar da Wade ke da ita.
Ta ce rikicin da ake yi a yanzu - kamar na Ukraine da na Gabas ta Tsakiya - na nuni da barazanar yaƙin nukiliya, wani abin da ke "ƙara firgita" ta.
"Idan muka ci gaba da taƙalo yaƙi to za mu iya kai wa ga yaƙin duniya na uku, kuma hakan zai kawo ƙarshen duniyar ne", in ji Tanaka yayin wata hira da BBC, ƴan kwanaki kafin cikar ranar tunawa da shekaru 80 na hare-haren a kan Japan.
Har yau ana ta tafka muhawara dangane da dalilan da suka Amurka ta yi amfani da makamin nukiliya a kan Hiroshima da Nagasaki.
Wasu masu fashin baƙi sun ce harin na Hiroshima ya zama dole ne domin buƙatar kawo ƙarshen yaƙin na duniya na biyu da kuma ceto rayuka.
Sai dai wasu sun musanta cewa yin hakan sam bai dace ba kuma abin ya yi sanadiyyar mutuwar dubban ɗaruruwan mutanen da babu ruwansu.
Abin da babu wanda ya isa ya musanta a yau shi ne illolin da hare-haren suka haddasa.
Wannan shi ne bayani dangane da harin na nukiliya bam a tarihin duniya da kuma illolin da ya haifar ya zuwa yau ɗin nan.
A lokacin bazara ta 1945, Amurka na yaƙi da Japan inda suka kwashe shekaru uku da rabi suna gabzawa da juna, bayan wani harin bazata da Japan ta yi a kan wani sansanin sojin Amurka a Pearl Harbour da ke Hawai a ranar 7 ga watan Disamban 1941.
Harin ya sa Washington ayyana yaƙi kan Japan tare da tsunduma yaƙin duniya na biyu.
A lokacin da rikicin ya yi ƙamari, Amurka ta ayyana yin amfani da makamin nukiliya a kan Japan.
A ranar 26 ga Yulin 1945, Shugaba Harry Truman ya saka wa'adi da ke neman Japan ta miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba ko kuma ta fuskanci gagarumar ɓarna da gaggawa.
Saƙon Truman bai ambaci an yi amfani da makaman nukiliya ba.
To sai dai waɗannan bama-baman na nukiliya suna daga cikin makaman da Amurka ta tanada a wani mataki na ƙoƙarinta na kwantar da rikikin.
Hiroshima ya kasance waje na farko da aka nufa - birnin ya ci gaba da zama wurin da bama-baman ba su faɗa ba kuma akwai sansanin soji a wajen. Ƙwararru da dama sun bayyana cewa gwaji ne kan irin ɓarnar da bam ɗin ka iya yi.
Matuƙin jirgin Enola Gay ƙirar B-29 wanda ke ɗauke da bam ɗin, Kanal Paul Tibbets, ya kai nisan kilomita 9.5 a sararin samaniyar Hiroshima sannan ya saki bam ɗin uranium-235 da ake yi wa laƙabi da "Little Boy" wanda ya fashe a iska, kimanin nisan mita 600 daga ƙasa.
"Da ƙarfe 8:15 ina kan hanyar zuwa makaranta sai wani ya yi ihu "Maƙiyi mai tada bam!" kamar yadda Toshio Tanaka ya ce. "Sai na kalli sama kawai na ga kamar walƙiya, kamar miliyoyin fitilu, komai ya koma fari."
Bam ɗin na Little Boy tamkar bindiga yake aiki, inda yake harba kwanson uranium-235 da dama a jere inda ɗaya ke dukan ɗaya.
A lokacin da suka haɗu, sinadaran da ke cikin bama-bama suka sa suka tarwatse.
Wannan haɗuwar ta bama-bamai na haifar da jerantuwar fitarsu inda ke janyo sakin sinadaran da ke haddasa fashewa.
Little Boy na ɗauke da sinadarin uranium 235 mai nauyin kilogram 64, wanda kusan kashi 1.4 aka yi ƙiyasin ya fashe.
Duk da haka, fashewar na da ƙarfi mai girman tan 15,000 da TNT.
Saboda gaba, kilogram ɗaya ne na TNT ke iya lalata mota.
Fashewar ta haddasa wani tururi mai zafin da ya wuce digiri 4,000 a nisan kilomita 4.5.
"Maza, da mata, da yara kusan tsirara, kayansu a ƙone. Suna tafiya hannayensu a miƙe da ƙuna a jiki, fatarsu ta saɓule tana reto daga kan ƴan yatsunsu," kamar yadda Tanaka ke tunawa.
"Sun yi kama da fatalwa".
An yi ƙiyasi cewa mutane tsakanin 50,000 da 100,000 sun mutu a ranar da fashewar ta faru.
Kaso biyu cikin uku na gine-ginen birnin - kimanin 60,000 - sun zama ɓuraguzai.
Nagasaki ba ya cikin wuraren da aka shirya kai wa hare-haren a karo na biyu na kai hare-haren.
Yanayinsa mai sarƙaƙaiya da kusancinsu da sansanin da ke ɗauke da fursunonin dakarun ƙawance a yaƙin ya janyo wa birnin zama wurin da ake hari.
Daga cikin wuraren akwai Kokura, wani birni da ke da yankunan masana'antu da birane a wani fili.
A ranar da aka kai harin, Kokura ya kasance a lulluɓe da hazo da dusar ƙanƙara kamar yadda matuƙan jiragen suka sanar.
An umarci ma'aikatan su duba wani wurin da zai bayyana irin ɓarnar da bam ɗin ke da shi.
Saboda haka sai suka bi ta Nagasaki.
Bockscar, wani jirgin bam nau'in B-29 wanda Manjo Charles Sweeney ke tuƙawa, ya jefa bam mai suna Fat Man, da ya fashe mita 500 daga ƙasa.
An yi bam ɗin ne da sinadarin plutonium-239.
Duk da cewa sinadarin plutonium 239 ya fi saurin samu a kan sinadarin uranium 235 sannan bam ɗin ya ƙunshi sinadarin kaɗan - Fat Man na buƙatar a yi amfani da wasu dabaru masu wuyar sha'ani a kan Little Boy.
Sinadarin na plutonium-239 ba tsarkakakke ba ne, wani abu da ya janyo gogayyar juna tsakanin sinadaren da ya ragewa bam din ƙarfi.
An yi amfani da wani tsari na ruftawa ciki wajen kunna bom ɗin kafin ya fara tarwatsewa.
Bam ɗin na da nauyin kilogiram shida na sinadarin platinium amma kuma an ƙiyasta cewa kiligiram ɗaya ne kawai ya iya samun damar fita.
Ya isa a saki makamashi da ya kai ton 21,000 na TNT.
"Gawawwaki sun ƙone, muryoyi daga cikin gine-ginen da suka ruguje na kiran agaji, mutane da naman jikinsu na reto sannan kayan cikinsu sun bullutso... Wannan wurin ya zama wani wuri mai ci da wuta. Kamar wuri ne na azaba, kamar yadda wani da ya tsira daga harin Nagasaki Sumiteru Taniguchi ke tunawa a 2020, lokacin da aka cika shekara 70 da tunawa da harin.
Fashewar ta fi ta Hiroshima amma kuma saboda tsaunin da Nagasaki ke da su kasancewarta a tsakani kwari guda biyu ya rage girman ɓarnar.
A Nagasaki, bam ɗin ya lalata wurin da yake da girman sukwaya mita 7.7 inda kaso 40 na birnin ya fuskanci mummunar ɓarna.
"Akwai ɗaruruwan mutane da ke cikin mawuyacin hali, ba sa samun kulawar likitoci," kamar yadda Terumi Tanaka ya tuna, wani da ya tsira daga harin Nagasaki kuma mataimakin darakta a Nihon Hidankyo, lokacin jawabinsa na karɓar lambar yabo ta Nobel a 2024.
"Ina da yakin cewa a lokutan yaƙi, bai kamata a bari irin wannan kisa da cin zarafi su rinƙa faruwa ba".
Babu alƙaluma na yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren bama-baman biyu, ko dai daga fashewar da ta faru nan take ko fashewar da ta biyo baya wasu watanni sakamakon rauni da kuma tasirin fitar makamashi.
Alƙaluman mace-macen da aka ƙiyasta sun kai kusan 110,000 a duka biranen biyu zuwa Disambar 1945.
Sauran binciken da aka yi sun nuna adadin mutanen da lamarin ya shafa a jumulla sun zarce 210,000 zuwa ƙarshen shekarar.
Japan ta sanar da miƙa wuya bayan baman-baman na Hiroshima da Nagasaki.
Sarki Hirohito, ya yi wa ƙasa jawabi ranar 15 ga Agustan 1945, inda ya buƙaci al'ummar Japan da su jurewa yanayin su kuma karɓi nasarar da aka yi a kan su.
An sa hannu kan miƙa wuyar a hukumance a ranar 2 ga Satumba kan jirgin ruwan yaƙi na USS Missouri da ke Tokyo Bay.
Da haka, aka kawo ƙarshen Yaƙin Duniya na biyu.
Cikin daƙiƙa ɗaya bayan fashewar, wani bam na nukiliya ya fitar da hasken gamma da sinadarin neutron da hoton X-ray - wasu sinadarai da ba a iya gani da suke tafiyar kilomita 3 tare da afkawa duk wani abu da ya bi ta hanyarsu har da gawawwakin mutane.
Harin Hiroshima, misali ya shafi kashi 92 cikin 100 na mutane a tsukin mita 600 daga ƙasa.
Waɗanda suka tsira daga fashewar, da ake kira Hibakusha, sun fuskanci mummunan tasirin tsananin zafi da fitar makamashi.
Mutane da dama sun samu mummunar ƙuna.
Shaƙar sinadarin da aka fitar daga makamashi na janyo amai da zubar jini da kuma zubewar gashi.
Bayan wani lokaci, wasu sun yi fama da yanar ido da mummunan ƙari.
A shekaru biyar bayan hare-haren, waɗanda suka tsira sun yi fama da matsaloli na lafiya. Matsalolin sankarar jini a tsakanin mazauna Hiroshima da Nagasaki ya ƙaru sosai.
Shekaru goma bayan hare-haren, akasarin waɗanda suka tsira sun yi fama da kansar maƙoshi da ta mama da ta huhu - an samu ƙaruwa fiye da yadda aka saba.
Galibin hibakusha sun shiga tashin hankali sakamakon irin abubuwan tayar da hankali da suka gani da rasa ƴan'uwansu da ƙaruwar fargabar fama da rashin lafiya mai nasaba da shaƙar sanadaran da suka fita daga makamashi.
Da yawansu sun yi fama da wariya saboda raunin da suka samu a jiki da kuma tunanin cewa suna ɗauke da cututtuka da za a iya kwasa.
Wasu na jin ba daɗi saboda rashin iya kuɓutar da wasu.
"Na kula da marasa lafiya 6,000, wataƙila 10,000. Bayan nan, na ji bana son na ci gaba da kasancewa a matsayin likita. Duka waɗanda na duba sun mutu, ɗaya bayan ɗaya. Babu wanda na iya ceto."
Shuntaro Hida, Hiroshima
"Ina ganin galibin waɗanda suka tsira suna fama da rashin kwanciyar hankali."
Yasuaki Yamashita, Nagasaki
Kusan duka mutanen na neman 'ruwa' suna kuma cewa 'taimake ni'. Na garzaya gidana inda akwai wata rijiya, na kuma kawo masu ruwa. Sun gode mani samma wasu a cikinsu suna shan ruwan suna kuma aman jini sannan suka mutu a kan idona. Na yi nadama kuma na tsorata sosai. Wataƙila ni na kashe su? Ni na kashe su?"
Keiko Ogura, Hiroshima
"Sai da na cika shekara 70 nake iya magana kan mummunan yanayin. Kafin nan, na shiga yanayi na tashin hankali; na yi tunanin ba za su fahimce ni ba."
Toshio Tanaka, Hiroshima
A yau Hiroshima da Nagasaki sun zama muhimman biranen masana'antu da kasuwanci.
Dukkansu suna da dandali da gidajen tarihi na tunawa da mutanen da suka mutu sanadin bama-baman na nukiliya.
Wasu hibakusha sun zama masu fafutuka kan ƙarruwar makaman nukiliya, yaɗa labaransu domin tabbatar da cewa ba a mance da irin munanan al'amuran da suka faru sakamakon yaƙin ba.
Muhimmin saƙonsu shi ne "a gaggauta hana makaman nukiliya" kamar yaddaTerumi Tanaka ya bayyana a jawabinsa na karɓar lambar yabo ta Nobel.
Tanaka ta bayyana bama-baman nukiliya a matsayin makaman kisan kiyashi, wanda bai kamata a ƙyale hakan na faruwa ga bil adama ba."
Akwai ɓangaren makaman nukiliya kusan 12,300 a duniya a yau, a cewar ƙungiyar da ke yaƙi da makaman nukliliya (ICAN)
Hibakusha sun yi fatali da tsarin da ke cewa ƙirƙira da kuma barazanar rama harin nukiliya na iya kare hare-hare da samar da zaman lafiya.
Masako Wada na daga cikin mutanen da suke adawa da barazanar yin amfani da makamin.
"Ba zan taɓa amincewa da batun amfani da makaman nukiliya ba wajen karewa da kuma illata mutane," in ji ta.
"Hakan na nufin ana iya sake ganin faruwar harin Hiroshima da Nagasaki."
A cewar Wada, ƙasa da hibakusha 100,000, waɗanda suka kai shekara 90, ne suka kawo har i yanzu.
"Kusan 10,00 a cikinsu na mutuwa duk shekara," in ji ta. "Don haka, ba za a samu saura ba."
Damuwarta ta wuce ga batun rasa tunaninta.
"Fargabata shi ne kafin faruwar hakan, za mu samu sabbin hibakusha."
An fara wallafa maƙalar ranar 6 ga Agustan 2020, kuma aka sabunta shi da sabbin hirarraki don bikin cika shekara 80 da kai hare-haren bama-baman.
Mai rahoto: Carlos Serrano
Waɗanda suka tace: Carol Olona da Tamara Gil da Princess Irede Abumere da Mark Shea
Tsarawa da zanawa: Cecilia Tombesi da Caroline Souza
Haɗawa: Catriona Morrison da Becky Rush da Marta Martí
Haɗin gwiwa: Camilla Costa
Da haɗin gwiwar Adam Allen da Sally Morales
Jagorar shirin: Carol Olona
Majiyoyi: BBC News, Gidauniyar Atomic Heritage, Atomic Archive, Ƙungiyar da ke fafutukar ganin an kawar da makaman nukiliya (ICAN), Taswirar Nuke, Hotunan Getty. Alex Wellerstein, ƙwararre a cibiyar fasaha ta Stevens; Luli van der Does, farfesa a cibiya zaman lafiya ta jami'ar Hiroshima; Hibiki Yamaguchi, mai bincike a cibiyar neman a kawar da makaman nukiliya a jami'ar Nagasaki; Yuka Kamite, farfesa a Jami'ar Hiroshima; Michael Gordin, farfesa a Jami'ar Princeton.
Hotunan fashewar Hiroshima da Nagasaki daga ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa na Los Alamos