Wanda ya samar da na'urar sanyayawar
Mutumin da ya tsara nau'rar samar da sanyin gaba daya, Dr Saud Abdul Ghani, ya fada wa BBC cewa Qatar na son barin wani abun tarihi, da kasar za ta dade tana amfani da shi har bayan 'yan kwallon kafar sun koma kasashensu.
Ya ce binciken shekarun da aka yi sun kai matakin da ake kira ''kyakkyawan yanayi'' wanda ya samar da muhalli mai dadi ga mutane da yawa. Tattaunawar da aka yi da 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje da aka yi a Gasar Duniya a Qatar a 2019, ya taimaka wajen tsara yadda baki da 'yan wasa za su amfana a Gasar Kofin Duniya.
Yadda 'yan wasa suka ga tsarin
BBC ta tuntubi Hajar Saleh, mai tsaron baya a tawagar mata ta Qatar, wadda ke taka leda tun tana da shekara 11. Ta kwan da sanin duk abin da ake bukata a buga babban wasa a yanayi mai zafi. Ta ce kadawar iska mai zafi ce babbar kalubale.
Mun saba da yanayin zafi, amma idan ka hada zafi da iska mai zafi, sai abubuwa su kara wahala Hajar Saleh
Hajar ta samu damar buga wasa a filayen biyu da ke dauke da na'urar sanyaya filin wasa na Khalifa da kuma Educational City.
Ta ce akwai bambanci ba kadan ba, musamman idan kana wasa a cikin watan Yuni, daya daga wata mafi zafi a shekara a Qatar.
Shin ko tsarin mai dorewa ne?
Masu shirya Gasar Kofin Duniya na 2022 a Qatar, sun yi alkawarin cewa na'urorin samar da iska mai sanyi a cikin filayen wasa ba za su jawo fitar iska mara-kyau ba, saboda wutar lantarki na zuwa ne daga sabon injin tattara hasken rana.
Amma bukatar ganin gasar ta gudana yadda aka tsara ba tare da fitar da hayaki mai guba ba, shi ne abin da aka sa a gaba.
Yawan carbon da ke kunshe - wanda aka fitar a lokacin gina filayen - ya kai kaso 90 cikin 100 na ilahirin wuraren, wanda aka kiyasta ya kai tan 800,000 - kwatankwacin ka tuka fasinja a mota a fadin duniya sau 80,000 in ji kididdigar hukumar kula da yanayi ta Amurka.
Idan muka yi duba kan abin da bai shafi filayen wasa ba. akwai sufuri da ke da tasiri a Gasar Kofin Duniya, ciki har da jiragen sama da zai kai mutane cikin kasar.
Fifa, ta ce yanayin gasar, wadda filayenta ke kusa da juna, an kiyasta cewa hayaki da za a fitar na zirga-zirga tsakanin biranen Qatar, kasa yake da kaso uku da wanda aka samar a Rasha a 2018.
Qatar ta sha alwashin za ta yi amfani da tsarin bunkasa muhalli wajen maye gurbin iskar da aka gurbata.
Kawo yanzu ba a fayyace yadda suke fatan cimma wannan ba. Fifa ta ce tana amfani da fasahohi daban-daban domin maye gurbin sinadarin da za a fitar a lokacin Gasar Kofin Duniya, har da makamashi mai inganci, da sarrafa bola, sake sarrafa makamashi da dasa itatuwa. Koda yake ba za a iya tabbatar da aikin da aka zaba ba.
Wadannan aikace-aikacen kan dauki shekaru kafin su fara aiki a hanyar rage gurbata iska. A wani bincike da BBC ya gudanar ya ce wasu dazuzzuka da aka yi shuke-shuke don reno a kan takarda kadai suke a rubuce.
Don haka, zai dauki lokaci kafin mu yanke hukuncin cewa ko Qatar ta cimma burinta na samar da iska mai inganci ko kuma abin da ta yi ikirari kawai na baki ne.
Kasar na shan suka kan wahalhalun da leburori ma'aikata 'yan gudun hijira su 30,000 da suka fuskanta, wadanda suka yi aikin gina filayen wasannin, har da wadanda da dama suka mutu da wadanda suka ji munanan raunuka. An kuma yi zargi tursasa mutane yin aiki, rashin yanayin wurin mai kyau, rashin wurin kwanciya mai tsabta, rashin biyan albashi da karbe fasfunansu.
Gwamnatin Qatar ta musanta wadannan zarge-zarge, ta kara da cewar tun 2017 ta bullo da tsarin hanyar kare leburori 'yan gudun hijira daga aiki a cikin tsananin zafi, da rage lokutan aiki da inganta wajen da ma'aikata suke zaune. A 2021 kadai ma'aikata 50 ne suka mutu sama da 500 suka ji munanan raunuka a Qatar daga cikin wadanda aka danganta da aikin Gasar kofin Duniya, kamar yadda hukumar ma'aikata ta duniya ta fitar da alkaluman. Wannan wani batu ne na da ban da za a ci gaba da bincikar daular da ke hamada.